Akwai tazara mai tsayi a tsakanin cikar wani babban buri, daga lokacin da nesa ta sake yin nisa, sai zuciyar dake cike da rauni ta sake sarewa. Tabbas babu maraya sai rago, matsoraci baya taɓa zama gwani, duk nisan jifa tabbas ƙasa zai faɗo, duk yawan tazarar dake tsakanin cikar buri, watarana buri zai cika, muddin Allah ya gaddara hakan a cikin zanen gaddarar. Daga lokacin da Allah yayi ikon sa, sai wannan tazarar ta zamtu mafi kusa da wannan burin. Ina burin? Ina Tazarar? Ina alfaharin? Ina taƙamar? Ina ikon da arzikin?
Ga tafiya mai kama da wuju-wuju, zafin rana mai dafar da tafin sawu... Cooking the story, coming soon. S-reza ✍️
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa sadda ze kawo mana karshen shi walau Mutuwa walau sakamako na farin ciki.
HIDAYAT yarinya me ƙarancin shekaru marainiya gaba da baya, bata da kowa bata san kowa ba, ta taso cikin kangin rayuwar marikiya an aura mata mafi zaluncin miji cikin maza a rashin sani, wadda ya kasance ɗa ga marikiyarta Kaddarar ƴaƴa ta Haɗa ba tare da wannan azzalumin miji yayi maraba da su ba, ya rayuwa zata zame mata? Ta ina zata iya Kula da kanta da kuma yaranta? Cin su shan su, suruturarsu? Anya zata iya tsallake wannan jarabawar kuwa? Anya ba zata gaza a hanya ta fawallawa Allah lamuranta ta zubawa sarautar shi idanu ba? Shin da dangin miji zata ji ko da Shi karan kanshi mijin ko kuwa da baƙar rayuwa da take ciki? Shin zata iya tsira daga wannan taskar na Tsaka mai Wuya? Duk ku biyo ni cikin wannan littafi na KOWA YA GA ZABUWA...
Na muku Alkawari ba Zaku taɓa yin nadama ba, Alqalamina a feke yake don Nishad'antar daku, fad'akantar daku da kuma ilmantar daku duk a cikin wannan littafi.. karku bari a baku labari.