A duk inda ɗan Adam yake yana tare da rakiyar jinsin Aljanu da Mala'iku wanda su kawai ke ganin sa, shi ko baya ganin su. Yanar da ubangiji ya sanya wurin sakaya mana maganai wani taimako ne gare mu don tabbas abinda baka gani ba ya fi wanda zaka gani alkhairi. Ko da yake inda a halittar mu take ganin su ai ba zai zama abin tsoro ba, don shi bai ɗaura mana abinda ba mu iya ɗauka. Sai dai a galibin da wannan zata iya
zama baiwa, ga wasu cutarwa ce tunda shi sirri a kwano akan saka a sakaya masa murfi.
A duniyar mutane da masu rai, gida, sutura da ƴaƴa kan zama tsani na wanzuwar zaman lafiya, shin akwai wani lokacin da wainnan kan zama jigo na ɓacin rai da nadama? Shin akwai ranar da muhalli kan zama kufai, rana zafi inuwa ƙuna? Akwai ranar da sutura kan zama tsiraici kuma ƴaƴa kan zama ababen ƙi?
Maƙota! Abun girmamawa, moƙoftan mu haƙƙi ne kyautata musu, sai dai ta ina zaka fara idan suka kasance ɗaya daga cikin jinsin da bamu gani?
Ta ina MAƘOFTAKA ya taɓa yiwuwa tsakanin ɗan Adam DA ALJANU?
Ku biyo alƙalamin ɗiyar Ƴandoma da Deejasmah don jin yadda aka haihu a ragaya.
Maƙoftaka da aljanu sabon tafiya, sabon labari mai cike da ta'ajjubi.
Labarin soyayya, kyautatawa, maita, maƙoftaka, Iyali kai har ma da tausayi.
Tuna da sunan MAƘOFTAKA DA ALJANU 2026
Maƙoftaka da aljanu, wuyar tafiyar ba'a fara ba
All Rights Reserved