PROGUE
Wani lokaci, mutum ba ya tsayawa gaban madubi ne don ganin fuskarsa kawai... yana tsayawa ne don yin hukunci da kansa.
Kin taɓa tsayawa a hankali ki kalli kanki? Ba da ido na wucewa ba, amma da idon da ke neman aibi a kowane sashe na jiki-kamar duk abin da ke jikinki yana buƙatar gyara kafin a ce kin isa a kalle ki?
Pimples da ke fuskarki su fara zama kamar sun fi ƙarfinki magana. Sauyin jiki ya fara zama kamar tambaya mai nauyi wadda ba ki da amsa. Wani ɓangare na zuciyarki yana tambaya: "Me yasa ni ban zama kamar su ba?"
A waje kuwa, duniya na tafiya. Wasu suna dariya cikin sauƙi, suna tafiya da kwarin gwiwa, suna jin kamar komai yana musu daidai. Amma ke... kina jin kamar kowace ido da ta kalle ki tana ɗauke da hukunci a cikinta-ko da ba gaskiya ba ne.
Kin taɓa jin bugun zuciya yana ƙaruwa idan kina tafiya kusa da mutane, hannunki a gaban hijabinki ba don ado ba, amma don ɓoye abin da kike jin zai jawo kallon da ba ki so?
Kin taɓa jin kalma daga wani ta zama kamar dutse a zuciya? Kalma ɗaya kawai... amma ta iya canza yadda kike ganin kanki na tsawon lokaci. Har sai zuciya ta fara maimaita ta ko da babu wanda ke magana.
Sannu a hankali, mutum zai fara zama mai kallo a rayuwarsa-ba mai rayuwa ba. Yana kallon kansa daga nesa, yana kwatanta kansa da kowa, yana rage kansa a duk inda ya ga wani ya fi haske.
Wasu mutane suna kiran hakan "rauni." Wasu kuma ba sa ganin shi ma. Amma ga wanda ke ciki... yana zama nauyi da ba a gani.
Ni Abeedah...
Na san wannan nauyin....
Na san yadda kalma ɗaya za ta iya zama kamar tana bin mutum har cikin dare. Na san yadda mutum zai iya fara jin kamar ba shi da kyau, ba shi da ƙima, ba shi da wani abu da zai sa a tsaya a kalle shi sau biyu. Na san yadda hankali zai iya zama kurkuku-inda mutum kansa ne mai tsare kansa da tunanin wasu.
A story about hating who you're but learning to love anyways...
All Rights Reserved