5 parts Complete Rungumeta yayi yana cewa ''nayi kewarki nima sosai'' ya cire mata hijabin jikinta da d'an kwalinta yana shinshinar gashin kanta, yace ''nayi kewar shak'ar k'amshinki'' ya shafa hannunta yace ''laushin jikinki ma duk nayi kewarsu, kuma ai ke kika hanani keb'ewa dake dan fushi dani kikeyi'' ta sauk'ar da numfashi tace ''matarka tana gidan kake son in sake dakai? Ni fah ina tsoron ta dake ni, wallahi ta fini girma da jiki''.
Dariya sosai Abakar yayi sannan yace '' tunda kin hak'ura ki tashi mu tafi, nan mutane zasu iya kallon min ke kuma ina kishi'' maryamah tace ''kishi? Kishin me?'' Ya d'aga mata gira yace ''eh, ni nasan meh nake kishi, hancin nan ma...'' ya ja hancinta sannan ya cigaba ''banson ana kallonshi bare sauran jikinki'' dariya sosai Maryamah tayi sannan ta d'aura d'ankwalinta ta sa hijabi suka bar wurin