#9 in romance on 05/09/2016
"Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?"
Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina."
"Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?"
Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga.
"An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan.
Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare."
Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena.
"Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba."
Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?"
"Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?"
"Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.