#1 in GENERAL FICTION on 27/05/2017 #2 in GENERAL FICTION on 10/05/2017 #3 in GENERAL FICTION on 19/05/2017 #4 in GENERAL FICTION on 16/05/2017 Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara galihu. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo mara yanci. Kasancewarta MACE! Ya sa ta zamo ja baya a cikin al'umma. Rauninta ya sa aka yi amfani da wannan damar wajen muzguna ma ta! Rauninta ya zama katanga a gare ta wajen samuwar ilimi. Kasancewarta MACE! Na iya sa wa ta zamo MADUBI a cikin al'ummarta,ta zama a bar kallo, a bar koyi. Cin zali da keta haddin mace wannan ya taka ma dokar addini. Addini be ware ta ba wajen neman ilimi. Haka ma a sauran bangarori na rayuwa. Haka Halimatu Ammah ta taso cikin bahaguwar rayuwa mai cike da qalubale. Shigowar zaratan matasa da suka taka rawar gani a rayuwarta ya zamo ruðani a gare ta. Kowannensu ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ci gabanta. Hakan yasa ta kasa tantance wanane zabinta tsakanin MUKHTAR da ARK a karo na biyu da za ta fada rayuwar aure. Wacce take dar-dar da ita, a sakamakon TUNA BAYA na rayuwarta da SALISU. Ku biyo ni dan jin tarin amsoshinku. Ayeesh ChuchuAll Rights Reserved