70 parts Complete wani ihu sukaji da alama ta can baya ne da sauri suka nufi bayan,
Inda suke Jin hayaniya " na duke ta kiyi wani abu akai",
" Rukayya ni kike fadama kinduke ta din ni sa'arkice",
Tafada tana nuna ta da hannu ita kuma sai murguda baki take tana hararta " walh Yau Zaki San wa kika taba a gidan nan"
" Ina jiranki maijiddah kiyi abunda Zaki iya"
" toshikenan" ludayin dake hannunta ta jefa ma Rukayya inda akayi narasa ya sauka kan goshin me gidan nasu,
" innalillahi Wa'inna illaihir raji'un" baba me gadi Yafada inda su duka suka maida kallonsu zuwa garesu,
Yayinda hankulansu ya tashi su duka inda Maijiddah tayi kan yarta da bakinta ke zubar jini,
Wacce tun tuni basu bi takanta ba Rukayya kuwa da sauri tadau Yasmin dake kasa Tana kuka yar da bata wuce 1yr ba,
Tayi nata part din nan suka bar Abdulhameed tsaye inda shima me gadi ganin yanayin me gidan nasa yasa yakoma gun aikinsa........