30 parts Ongoing *_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....ka zalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai dake cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana yake tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shine; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine mecece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!..._*