50 parts Complete Season 1.
"Wato gani ni makwadaiciya ko?, To koda kika zo wannan gidan kin same mu muna cin sa ba wai tafowar ki muka fara ba bak'ar munahukar Allah, ai wallahi waje kika samu shiyasa, yanzu fisabilillahi dubi jikin ki, haka kika zo daga gidan ubanki?, shin ko kin manta ne in tuna maki yanda kika zo kamar wadda ta kwana dubu bata saka Lomar Tuwo a bakin ta ba, Wuya kamar Marik'ar Lema gabadai ilahirin jinkinki haka yake kamar na wata Tambad'ad'd'iyar Akuya, shin wai Zahra'u ko kin manta ne?. Ina jiran amsar tambaya ta..."
"Kazat-ubaaaaa, akan wannan bak'in kifin har zai sa Rai na Ya b'ace, Allah ya kiyaye ni wallahi, ai ni ba irin ki ba ce, dan haka yanada kyau ki sake tunani bak'ar munafuka."
"Ni ba haka nake nufi ba Hajiya Allah ya baki hakuri, kawo kular sai in zube maki kifin.!"
...."Awww yanzu dan kin raina ni har sai na mik'o maki kullar zaki zube man kifin? lalle Zahra'u wuyanki Ya yi kauri, to bari kiji in gaya maki wallahi wannan jikin naki ba zai tab'a bani tsoro ba yanzunnan wallahi sai in ciraki sama-sama in buga ga k'asa, idan kuma kina tantama sai yanzu akafta ki gani..........!
****
"Iyyeeee to sannun ku da zuwa babbak'un munafukai, da ma na sani ai, wato an zo ganin k'wam ne ko? dan a gani idan na mutu aje zuwa shela.!"
Nan da nan wajen ya yi tsit hayaniyyar ma aka daina kamar wajen da ak............
Ta k'ara da cewa "To wallahi zama daram-dak'am a cikin duniyarnan kamar yanda bakwa son gani na haka zaku barni sai sanda lokaci na ya cika na barin duniyar munafukai shegunan banza 'yan-tsiya wad'anda ba abin da suka iya sai tsintse da tsegumi, kuma wallahi na rantse da Rabbul-samawati wal-ardi dik wanda bai bace man da gani ba Ubangiji Allah ka-isar man ka fidda man hakki na bisa ga kan uban kowa".
Anan wasu suka dinga ce wa "Ba amin ba" .................!
Dik a cikin wannan littafin mai taken suna da WAHALA DA GATA SEASON1..... ku kasance tare da shi
FOLLOW, VOTED, CMMNTS, SHARED