Labari ne da ya k'unshi; Tausayi, Mamaki, Al ajabi, Sadaukarwa, Jin dadin Rayuwa, K'uncin Rayuwa, da kuma Duhu da ya mamaye zuciyoyin wasu bayin Allah dake cikin Labarin. Wannan Labari ya kunshi darussan rayuwa dake faruwa damu yau da kullum.
Gidan Habib Lema na dauke da Labarin wata Uwa da ta gina Gidan ta cikin Tsaftaciyar So, Aminci da k'aunar juna.
A rana daya, lokaci gudu wata Azzulumar Mace, wacce ba Allah a ranta ta shigo Rayuwar su, ta hanyar Asiri, Kissa da Kisisina ta tarwatsa musu Farin cikin su, ta hargitsa gidan ta hanyar lika ma Matar Gidan mafi munin sharrin da yayi sanadiyyar rabuwarta da Gidan aurenta, Mijinta da 'Ya'yanta. Haka Yaron ta ya taso da BAKIN DUHU a zuciyar sa, be ji, yadda be gani, ya koma Rayuwar k'unci da tsana. Abu yayi k'amari a lokacin da ya rasa tillon K'anwar shi, wacce ita kadai yake kallo ya ji dadi, hakan ya k'ara jefa Rayuwar shi cikin wani BAKIN DUHUN.
A wannan halin ne Allah ya hada shi da kalar tashi Alherin Rayuwa.
Shin Wacece Alherin shi?
Me zata yi da zai zame mishi Alheri?
Zaku ji amsoshin ku a Labarin KE ALHERI.