jidderhlawalbello
Labarin *SO GASKIYA NE* Labarine daya ya shafi rayukan mutane uku, labarin soyayya ce da ta shigi wani matashin saurayi mai jini a jika mai takama da ilimi,dukiya tattare da wayewa data shige shi batare da yashirya ba duk da kasancewar shi a daya daga cikin mutanan nan da ba su yarda da soyayya ba . In takaice muku ya fi daukan soyayya a matsayin tasuniya ,labarai koh kuma wani fairytale. Duk da kasancewar ita wacce yake so tana da wanda take da burin karashe sauran rayuwar ta da shi duk da shi din ya fi daukan ta a matsayin aminiyar shi.
Shin me kuke ganin zai kasance a wannan littafin mai suna *SO GASKIYA NE* .
Zai yi nassarar shawo kanta da soyayyar shi?
Zai yi nassarar samun soyayyar ta?
Shin soyayya ce koh abota take ma wannan din nan?
Ku biyo ni a cikin labarin *SO GASKIYA NE* Don ku ga ya zata kasance.