DielaIbrahim
A wani zamani daya shuΙe, Da zarar magriba ta gabato kusan ko wani gida zaka riske su Ιauke da *FITILAR ΖWAI*
Tun ba a fara min halitta ba na ke wahala, har tsahon watanni biyu a cikin ciki ina gwabzawa tare da mahaifata, ni ne Ζwan halittar dake cikin ta,Ζwan halittar da ake son a zubar. Kaifin kwakwalwar da Allah yayi ma jarirai ya sanya na ke fahimtar cikin labaran ta akwai rina a kaba. Mahaifiya ta ta shiga halin tsaka mai wuya, ta sha gwagwarmaya a rayuwar ta don kare ni daga magungunan da Abba na ya ke kawo mata don zubar da ciki na, Abba ya manta cewa mugun nufi, baya kashe Ιan barewa kuma da ikon Allah haΖan sa ba zai taΙa cimma ruwa ba akan gurbatacciyar buΖatar sa.
A lokacin da sinadarin allurar ya feso zuwa mahaifar wato cikin in da na ke babu irin jijjigar da ban sha ba, maganin ya so ya tarwatsa sassan jiki na wanda bai da Ιe da zama tsoka ba, da ikon Allah na koma bayan mahaifarta na yi wa kai na Ιuya duk da tsananin wahalar da na sha tsakanin rayuwa ko mutuwa, Allah ya zaΙa min rayuwa, tsahon watanni shidda ina bayan mahaifarta sannan na dawo na zauna daram a cikin mahaifarta na kuma Ιaura daga kwanakin da na tsaya,lokacin na san da cewa kainuwa dashen Allah ne, haka zalika zakaran da Allah ya nufa da cara ana muzuru ana shaho sai yayi abin sa.