Nana_haleema
Hausawa suna cewa da mutuwa, aure da arzuƙi ƴan uwan juna ne. Ni kam na ce a haɗa da RABO domin shima yana daga cikin waɗanan ukun. RABO in ya yi kira ko kana cikin mahaifiyar ka sai ka amsa shi ka fito duniya. KIRAN RABO ya kan canja ƙaddara daga baƙa zuwa fara, KIRAN RABO ya kan mayar da wasa ya zama gaske, KIRAN RABO yana mayar da abinda ba zai yu ba ya zama mai yuwa. Wani yana shigowa rayuwar wani dan ya zama silar amsa KIRAN RABON sa, wani yana fita daga rayuwar wani dan hakan ya zama silar amsa KIRAN RABON SA. Ya ake gane rabo ya yi kira? Ba a ganewa, sai bayan Allah ya yi ikon sa a kai ake fahimtar daman can kiran rabon ka amsa. Ana amsa KIRAN RABO a lokacin da ba a san an amsa shi ba, ba a jin kiran da kunne balle a kasa kunne a nutsu dan a saurari lokacin da rabo yake kiran ka. Kamar yadda bawa ba ya sanin lokacin da mutuwar sa, lokacin auren sa, lokacin da ƙaddara ta kira shi haka ba a sanin lokacin da RABO yake kira sai dai ka tsinci kan ka a lokacin da ka amsa. KIRAN RABO lokaci ne dashi kamar dai yadda mutuwa take da lokaci!.