"Samha kiyi sauri kishirya lokaci na wucewa "cewan wani mutum me kimanin shekaru 45 , gama fadan haka keda wuya wata yarinya er kimanin shekaru 14 tafita cikin shigan atamfa Riga da skirt se tadaura hijabi dai dai guiwa kyakyawa yarinya son kowa kin Wanda yarasa ,ita ba fara ba and kuma ba baka ba , doguwa ce amma ba chan ba sannan slim ce amma akwai shape ." daddy gani nafito fa " cewan samha . tanashiga mota naga sun dauki hanyan damboa road dake nan garin Maiduguri borno state , a wata makaranta me suna diamond secondary school . bayan shigansu makarantan securityn yace daddyn ze iya tafiya se zuwa bayan awanni kaman biyu seya dawo daukan samha .
Samha zaune akan kujeran dalibai dake ajin zuciyanta ke tsananin bugawa sabida tsoro Dan ita Allah yagani batason zuwa makarantan tafison makarantar ta nada tareda friends dinta amma yazatayi dadynta yadage seta yi diamond ta kudiri niyyan faduwa a jarabawarta nashiga makarantar sabida tasan shine Kadai hanyar komawanta makarantarsu nada . tanacikin tunaninta wata malama tashigo ajin aka raba musu question paper na maths da English kowannensu 67questions 60 obj and 7 essays. Addua tayi tarubuta abunda tagadama sannan tayi submitting tana fita kuwa tahadu da daddy yazu daukanta .
"Mami nifa nakega kaman bazanci ss1 dinsunnan ba sabida yawanci baniya questions dinba " "haba samha sede bakiyi karatu bade ba INA kallon ki ba se bacci ba abunda kika iya mtchew Nide Allah yasa kici Dan dadynku na son makarantan wlh haka Nima " ji tayi zuciyanta yabuga lalle inde har iyayenta nason makarantan to ba makawa se tayi "innalillahi wa inna ilaihi rajiun" .
A week later
Samha tamanta ma dawani magana wai shi diamond secondary school ko shiganshi kawai Sega daddynta ya shigo da envolop ahannunshi mika mata yayi " innalillah " tafada tana zare ido ganin admission letter ne da sunan ta amma abun mamaki maimakon na ss1 se taga na jss 3 kuma tabbas yanda ta kalli fuskan dadynta to ba makawa shiga diamond secondary school dolene ko tanaso ko bataso. "Daddy kaman na jss3 nake kallo " eh cewan daddy "to kuma daddy zanje " ehmana samha har narigada nabiya miki komai fa har kudin uniform next week zamuje karba" samha kallon shi takeyi batasan sanda tafashe da wani mahaukacin kuka ba mami dake zaune gurin tunfarkon abun tadago takalle ta cikin mamaki tace "samha kuka kuma haba sekace bakisan yadda da kaddara me kyau ko akasinshi na cikin imani ba haba kar kibada ni mana ernan " haka dai tayi ta lallabata har tayi shiru kuma ta amince zata shiga diamond secondary school
This is my first novel please if I should continue or stop let me know
Comment and vote it will help a lot
