dasunan Allah mai rahama maijinkai zanfara littafina maisuna
INAH DA UBA dan haka Allah narokeka yanda nafara lafiya Allah yasa nakare lafiya kuskuran dake ciki Allah kagyara mana baki daya
wannan littafin na sadaukar dashine wa masoyana masu nunawa novels dina sosayya nagode Allah yabar kauna da so da Amanda
kaman yanda kuka sani nakawo maku littattafayna guda biyu kuma kunnuna masu kauna RAYUWAR KULU dakumaGIDANMU KHO GIDAN MIJINA yanzu kuma nakawo maku INAH DA UBA nagode
wannan littafin maisuna INAH DA UBA kagaggen labarine mai nushadantarwa dakuma fadakarwa da sauransu ina fata wannan littafin yasamu karbuwa a gareku masu karatu idan yayi day day da rayuwar wani ina neman afuwa akan hakan
nagode kuji dadi lafiyaaaaaaaa
way kina inane assama'u kizo kiyi sauri kafin idi yarufe shagonsa yatafi masallaci dan Allah kifito kinji yar albarka
bazaki fitoba saina shigo dakinnan ko
banason iskanci kinajina kuwa ko kinbarni inata faman surutu to wlh idan nashigo sai jikinki yagaya maki mai kafiyar tsiya da taurinkai
au bazaki fitoba kuwa bari nashigo dakin
kina ina kinama bayan kofa ko to fito nan ai tunda nashigo dakin to sainamiki dukan tsiya marar jintsiya
umma umma dan Allah kiyi hakuri wlh bazan sakeba kinsan abinda ya hanani fita domin dana fita zasu fara daga inda suka tsaya kuma kinsan hakan umma kaway kije da kanki dan Allah
masha Allah yarinya nagano anjawo daga bayan kofa kyakykyawace masha Allah etah ba faraba ba kuma baka bace amma kuma
ruwan tarwadace kanta babu dan kwali gashinta yazubo bayanta babu kitso akanta fiskarta tana hade da gajeriya dakuma doguwa gata yarinyar ita kanta doguwace daganinta bazata huce shekara goma sha biyarba 15
ai dama tunda bangankiba nasan cewa kina bayan kofa to fito ga kudinnan naira darine kije kisiyo mini battery guda biyu kinsan na fitilar ya mutu shine zansaka sabo gashi magaruba tayi karda muzauna a duhu kuma karda kidade kinjiko
wlh umma gwanda muzauna a duhun dan Allah ko kuma
kokuman ubanki nace kokuman ubanki wato ina danne zuciyata karda namiki duka amma kina tunzurata sabida bakyajin magana bansan rashinjin wakikayiba domin niday inajin magana kuma har iyayena suka mutu narabu dasu lafiya
saiday naimaki fatan Allah yashirya minike assama'u ya kareki
zokiyi sauri kisiyo abinda yar albarka
to umma bari nadauko hijjabina
kiyi sauri kidawo duk wanda yatsokaneki karda ki kulasu kinjiko kiyi masu yanda kika saba kimai dasu basu da hankali ke kuma kinada hankali bazaki kulasuba kinjiko
shikenan umma zanyi yanda kikace
Allah nagode maka tunda nataho ban hadu da kowaba a hanya amma saiday shagon malam idi gidan muna furci da gulma idan anyi masu magana suce ai muna furci yakoma gindin mata sabida basu da aikinyi kuma kowannensu sunada iyalai amma halayansu basu da kyau
domin duk mutumin da akace bashi da aikinyi sai zaman muna furcin mutane dayi dasu to wlh ba mutumin arzuki bane Allah yasa mudace
subahanallahi bakin shagon kuwa a kway mutane amma bansan yawansuba gaskiya.amma bari nakarasa
salamaalaikum ina yininku
lafiya kalau yar gidan umma assama'u ya umman taki
tana lafiya malam idi ina yini
YOU ARE READING
INAH DA UBA
FantasyThis is the story about a village girl that suffers a lot since from from her childhood and when she grew up she went to the city in search of her father.