💧💧 *RAHEELAH....!💥*
©️ *HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers.*FEEDOHM💞*
Wattpad@Feedohm.*SADAUKARWA GA FA'IZA BABAYO ZAKI.*
Alkhairin Allah ya kai maki a duk inda kike.*TUƘUICI GA MEENA MUSA (HAMMAK).*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI, SISTER'S MUN DAWO DA SABON LABARI MAI ARMASHI, BA ƘIRƘIRARRE NE BA, YA FARU A ZAHIRI, SAI DAI MUN CANZA SUNA GARI DA WASU ABUBUWAN, SANNAN AN ƘARA MASHI MAGGI 20% DOMIN ƘARIN ARMASHI.*
*1988.*
*01*
*** A tsakiyar asibitin mai machine ya sauke ta, ta lalubi naira hamsin daga cikin ƙwagiri ta miƙa mashi, tare da gyara zaman bujen ta, da ya ri ga ya yaye tana raba idanu, a hankali ta saki gyatsa ta kai hannu ta sosa ƙugunta, tana mazuran rashin sanin taƙamaimai inda zata nufa, giftawar mai dafaffen dankalin hausa ya dawo da ita duniyar mu, ta shafa ɗan ƙaramin cikin ta, dake lafe kamar babu, kafin ta saki hamma ta ɗaga murya ta kira shi "Kai mai dankali, ya ka nan."
Ta matsa bakin ƙatuwar bishiyar dake tsakiyar asibitin, tayi zaman dirshan tana tambayar "Nawa nawa.?
"Wannan kashin biyar biyar, wannan kuma goma."
Ta nuna na goma ta ce "Ka bari guda uku murtala.?
"Kawo.!
Ta ƙwalalo ido waje tana faɗin "Kan uban can, da sauri haka? To guda huɗu murtala."
"Albarka."
"Haba kai ko? Duka nawa buhun dankalin yake? Kuma na tabbatar daga ƙauyen mu ka saro shi, idan aka bibiya ma na maigidana na ne."
Ya ɗauki farantin shi da niyyar barin gurin, ganin bata da niyyar siye, yayin da tayi saurin janyo gefen rigar shi tana faɗin "A yi haka? Dawo in siya, ai tun farko ni ce nayi wautar cinikin."
Ta ɗauka ta bashi kuɗin sa, sannan ta rage murya tana faɗin "Ina ne masu juna biyu ke zuwa awo.?
"Ban sani ba, amma ki tambayi wancan mai fararen kayan, idan yayo ta nan." Yaron ya bata amsa, sannan ya ɗauki kayan sa yayi gaba abun shi.
Ta ɗaga murya "Waye shi.?
Bai juyo ba ya bata amsa da "Malamin lafiya."
"Dafta.?
"Eh.!
"Nagode."
Zuba mashi ido ta yi har ya zo kusa da ita zai wuce, sannan a hankali ta miƙa hannu tana faɗin "Dan Allah, ranka shi daɗe, yallaɓai dafta, na ce ko ina ne ɗakin ƴan awon ciki.? Ta ƙarashe maganar tana taunar dafaffen dankalin hausa abun ta, cike da tsabar ƙauyan ci da jahilci.
Ya ɗago a fusace da niyyar jefa mata baƙar magana, amma sai samun kan shi yayi da zuba mata mayun idanun sa, a take wata muguwar sha'awar ta, ta ɗarsu a baƙar zuciyar sa ganin ta ƴar fulani jawur mai ƙananan shekaru, ga ƙyau da sura da Allah ya bata, ya washe mata jajjayen haƙoran sa yace "Wa za'a auna.?
"Ni ta ta..! Ta furta haɗe da tsartar da yawu.
Mamaki ya cika sa, ya ƙare mata kallo daga sama zuwa ƙasa, Sam ba ta yi kama da matar aure ba, a hankali ya ce "Ke kuma.?
"Yo eh mana, da hunturu aka ɗamran aure, har yau ban ji alamun na kamu ba, babu amai babu kasala, shine na zo a auna ko ɓoyewa ya yi." Ta basa amsa har lokacin tana cin dafaffen dankalin hausar ta.