02

25 4 0
                                    

💧💧 *RAHEELAH...!💥*
                           

©️  *HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers.

        *FEEDOHM💞*
   Wattpad@Feedohm.

*SADAUKARWA GA FA'IZA BABAYO ZAKI.*

*TUƘUICI GA MEENA MUSA (HAMMAK).*

*02*

       ***Duk abunda ya kamata na taimakon gaggawa yayi mata duk da dai ba ɓangaren sa ba ne, domin dental ya karanta a health technology tsafe, hakanan yake zama a pharmacy sakamakon sakacin gwamnatin mu, ya kalle ta cike da takaici ganin ta yage baki tana ihun "Wayyo Audu, yau na shiga uku! Ahe awon ciki ba banza ba? Kai Allah tsine asibiti da tarkacen cikin ta, Allah ya yi ma iyata albarka."

Ya daka mata tsawa "Ke gafara rufe mani baki, bani son lalata, ba mace kike ba? Ko an faɗa maki haihuwar banza ce.?

Ta dafe baki tana faɗin "Da ƙwaranƙwatsa bai rufo! Azaba nake ji da sukurniyar fitar wani abu a mafitsara ta."

Takaicin ta ya kusa kashe shi, Sam bai iya lallashin mace ba, hasali idan ka ga yana ƙwantar da kai, buƙatar sa yake son biya, da ta biya kuma sai wulaƙanci, amma wannan kam baya buƙatar alaƙar ta tsaya a haka, so ya ke ta zame mashi tamkar dadiro, da ƙyar ya samu ya danni zuciyar sa, ya sassauta murya kamar mai mura ya ce "Ba ki na yin al'ada ba.?

"Eh duk bayan mako huɗu, amma tun da nayi aure ban yi ba."

"To dunƙulewa ta yi, shi ne yanzu na fiddo maki da ita, gudun kar ta danƙare a jikin yaron cikin ki ya mutu, dama amfanin zuwa awon kenan."

"Au to..! Ta faɗa tana matse ƙwalla.

"Ki ɗaure ki bar wannan ihun.!

Daga haka ya miƙe ya fice, yayin da ya ja ƙofar ya datse ta, tare da kashedin ta jira shi, zai je banki ya ciro kuɗi, kar ta kuskura ta fita ko'ina.

"Su kuɗin ciro su ake ba nema ba.?

"Eh.!

"Ƴan birni kuna cin banza, idan na tashi dawowa zan taho da buhu na, ka taimaka ka kai ni in cira nima, tunda ba tambari gare ku ba, a goshi. "

Yayi banza ya ƙyale ta.

Har kusan marece sannan cikin ya lafa, ya dawo ya same ta zaune ƙasa tana goge jinin da ya ɓata mata zani sosai da takarda, duk ta ƙazance gurin.

Baice da ita komai ba, sai itace ta yi karaf tace "Tunda ka tafi cikin ke sukurniya, yunwa na neman hallaka ni, dan Allah ka kira mani mai awara.!

"Tashi mu je an sallame ki, idan kin je gida ki cinye duniyar.!

"Ni Mayya.? Ta dafe ƙirji.

Yayi watsi da ita, yayin da ya yi gaba abun shi, yana tunanin yadda zai iya gyara gurin, ya saki siririn tsaki, haɗe da ƙunduma mata ashariya a zuciyar shi "Ƴar kan abun uba ƙazama.!

    Har bakin gate suka fita, sai dai bai yadda sun jera ba, yana gaba tana baya, ya buɗe baki kamar ba da ita yake magana ba, yana kallon gefe ya ce da ita "Kar ki manta duk bayan ƙwana biyu ki dawo."

Ta gyaɗa kai da sauri, tare da ƙarɓe naira 500 ɗin da ya bata sabuwa fil ta ƙulle gefen zanin ta, a rai take faɗin "Riba uku da ashirin, a auna ka, a sai maka balango sannan a bika da jika biyu da rabi, shi yasa mata ke nacewa zuwa awo."

Har ta soma tafiya ta juyo ta ƙwala mashi kira "Ƴallaɓai Daftari.!

Ya hayayyaƙo mata "Ya akai.?

RAHEELAH. Where stories live. Discover now