🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻*_RAYUWAR MEENAT_*
🧕🏻
🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻💞💞💞💞💞💞💞💞
*_(Labari mai taba zuciya♥_)*
💞💞💞💞💞💞💞💞Story
&
Written
by:*_Meenat Laweal tk_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/بسم الله الرحمن الرحيم
Page 5_6
________ Tun dosowar ka wajen hayaniya kawai zaka fara ji tana fitowa daga gidan , da alamun dai rikici na faruwa a wannan waje.
Inna Marka, ta ce" wallahi Hajiya Larai baki isa ba , dole ki gano man inda kika kaiman diya ,
"kuji Inna Marka da karfin hali wai diyarta don taji batun kudi"
Wadda aka kira da Hajiya Larai, ta ce" Haba Marka kinsan dai bazan kaita inda za'a sayar da ita ba ko , to nima yau din nan can inda na kaita suka kirani suke fadaman wai ta gudu , kinsan aikin bana raggo bane kila shiyasa ta gudu don bata iyawa,
Inna Marka, ta ce"wallahi karyane wane wahala ke ban saba mata ba a gidan nan balle kuce haka ,kawai dai kun sayar man da ita kun cinye kudin ,ni da kun mai do man ita da ko aiki ta dunga yi man tunda gaya nan kamar ya kashe mu , gashi mun amshi kudin yaron nan da zata aura,Hajiya Larai, ta ce" toh ay Marka zama zakiyi sai muyi magana , musan yadda za'a shawo kan matsalar koh??, ta karashe maganar cikin sigar tambaya.
Inna Marka, ta ce" Wane zama kuma bayan kun hallake kudi kun barni a hunhun ma'ahun,
Hajiya larai ta ce" ke dai zauna mana,
Zama sukayi ,kana Hajiya Larai ta kalleta don tasan dai Marka mayyar kudi ce to ay matsalar tazo da sauki .Hajiya Larai ,ta ce "Yanzu in mukayi haka dake wa zai gane , tafada tana dunkula mata uwayen kudi a hannunta,
Inna Marka ta washe baki sannan ta ce" Kema yanzu kikayi magana da kin barni shiru ay dole nake maki sababi Hajiyar Allah,
Hajiya larai, ta ce" Yawwa ta wajena ,
Inna Marka, ta ce" Allah yayi maki matar gomna mu sha dadi ,da girman kujerar ki ,Fatlodi ake cewa ne ma ko fislodi?
Hajiya Larai, tayi dariya, ta ce" haba wani fislodi, FirstLady zaki ce kar ki bata sunan mana,
Inna Marka , ta ce" ay abun sai ku yan boko mu da ba na zamanin ba na muhammadiyya kuma ,
Hajiya Larai , ta ce" ni zan wuce ki ja bakin ki ki yi shiru , kinji na fadamaki dai,
Inna Marka, tace haba wane dan iskan zai san yadda akayi ay nasan abun fada,
Hajiya larai , ta ce"yawwa toh sai anjima , tafada tana ficewa ,
Inna Marka ta fiddo taba ta cigaba da bata wuta tanayi tana wakarta ta goggun yan bariki.