*PAGE 1~5*"Wai kai sai wani d'oki kake kamar wanda yau aka kai maka matar."
"Abokina bazaka gane bane Wallahi tunda na auri Husna ban ta6a kusan tantaba kai baka tunanin zan shiga hakk'inta?" Ya k'arasa maganar fuska d'auke da damuwa.
Wani dad'i ne ya lullu6e Yusuf sannan yace
"To ai sai kayi hak'uri tunda kasan tsoro take ji kuma idan kayi bata cire wannan tsoron ba Wallahi ciwo zaka ji mata kaca-kaca."
Gaban Farooq ne yayi mummunar fad'uwa sannan yace
"To Abokina menene mafita?" Ya tambaye shi.
"To mafita dai d'aya ce kawai ka hak'ura har sai ranan da Husna ta bude baki tace ka kusanceta."Waro ido yayi yace
"Kai Wallahi Husna bazata iya cewa na kusanceta ba koda kowa zamu shekara ne sai dai kawai na cire tausayinta nayi abinda yake raina dan kuwa Wallahi yana damuna kasan dai abinda Doctor yace mun."Wani kallon tsana Yusuf yayiwa Farooq sannan yace
"Kenan kayarda ka kashe 'yar mutane ko?
Dan kuwa nasan kai bazaka sausauta mata ba.""No Yusuf yanzu nazo wajen kane dan kabani shawara saboda kai ka dade da mata kuma kaine aminina dan haka nazo gunka please Abokina ka taimaka mun."
Murmushi mugunta Yusuf yayi sannan yace
"To shawara ta d'aya ce kajira ta nan da sati d'aya idan kaga babu halamun buk'ata a tattare da sai kawai kayi abinda kayi niya.""Hmm to Allah yakaimu nan da satin amman Wallahi nikam a matse nake."
Haka dai suka tayi a tsakanin su sannan suka yanke akan sai nan da sati.
Yusuf ne ya rak'oshi har gida a lokacin da suka shigo gidan wani wawan k'amshi ne ya daki hancin su Wanda sai da gaba d'ayan su suka shiga wani hali.
Zaune take akan d'aya daga cikin kujerun da suka zagaye parlour.
Swiss lace ne a jikin ta Wanda ya amsheta kamar dan ita akayi.
Farooq ne yayi sallama wanda Yusuf ya kasayin Sa.
Amsa musu tayi cikin zazzak'ar muryan ta sannan ta tashi tana musu sannu da zuwa.
Yusuf sake rikicewa yayi da ya kalli halitattar Husna Wanda bai ta6a tsammanin tana da shi ba.
Farooq ne ya d'an bigeshi yace
"Kai kuwa sai kace Wanda baka Santa ba sai wani kallon ta kake" ya k'arasa maganar cikin zolaya.D'auke idon shi yayi a kanta sannan yace
"Wallahi abokina sai naga kamar Yau ta chanza mu.....""Sannun Ku da zuwa"
Yusuf yayi saurin amsawa da cewa
"Yauwa sannu amarya ya kike?"Murmushi tayi tace "Lafiya k'alau Ya Yusuf, ya Anty Hafsat?" Ta tambaye shi.
"Lafiya ta k'alau gobe insha Allahu zan kawota ku wuni saboda Ku fara sabawa tun yanzu."
"Kai amman naji dad'i Wallahi ya Yusuf Allah yakaimu."
Shikuwa Farooq yana zaune yana kallon amaryar Sa wacce duk kallon da zai mata sai yaji wani abu a jikin shi.
Juyowa tayi tace
"Sannu da zuwa ya Farooq."
"Yauwa sannu uwar gidana uwar 'ya 'ya na ya kike?
Ya kuma kad'aici."
"Alhamdulillah
Ya office?"
"Alhamdulillah My Angle."Wannan kalamai na Farooq ne ya fara 6atawa Yusuf rai hakan ne yasa shi katseshi da cewa
"Abokina nifa yunwa nake ji muci na gudu nima gida na."
Murmushi Farooq yayi yace
"To ai ga abinci a dining muje mana."Haka kuwa suka tashi suka nufi dining dan cin abinci amman ina Husna Sam ta kasa sakewa dan wani kallo Yusuf yake mata hakan ne yasata tashi tabar abinci.
Bayan sun kammala sun koma parlour in zauna Yusuf yace da Farooq
"To Abokina ni zan gudu amman dan Allah kar ka kusanci yarinyar nan Wallahi yanda na fahimceta har yanzu tsoro ne a ranta kagani dai ko abinci ta kasa ci.""Eh nima dai hakan nagani amman kasan bazai yu na zuba mata ido ina kallon ta ba, dole sai nayi abinda yake rai na."
Mugun kallo ya masa sannan yace
"To naji ka k'irata kuzo Ku rakani zan wuce."Haka kuwa ya tashi yaje ya kirata suka rakashi bakin motar shi sannan suka dawo cikin gida.
Bai tsaya a ko inaba sai gidan shi,
ba laifi yau tayi wanka tayi kwalliya har da turare ta saka a gidan ta abinda rabonta da shi har ya manta.Sallama yayi ya shiga kamar yanda yayi tsammanin a parlour ya sameta kwance akan three siter.
Amsa mishi tayi ya shiga
"Sannu uwar 'yan jin dad'i ai daman nasan kina nan kwance."Turo mishi baki tayi tace
"Sai yanzu kadawo kasan inajin yunwa."Kallon ta yayi yace
"Wai ni bawan kine da zan dinga dafa miki kina ci to Wallahi Yau bazan dafa ba sai dai ki kwana da yunwa."Mik'ewa tayi da k'yar ta zauna tace
"Haba ya Yusuf kaima kasan bazan iya fad'awa ba kuma ko na daga bazan iya ci ba ko naci ma amarwa nake.""To Allah yasa kar ki iya ki zauna nikam bazan dafa ba" ya k'arasa maganar yana hayewa sama d'akin shi.
Ita kuwa cewa tayi
"Oho dai idan baka dafa ba zan iya badawa a siyomun."Haka kuwa tabawa Isyaku mai wanki da guga kud'i ya siyo mata tsire kasan cewar tanada yogurt a friez.
B'angaren Farooq kuwa hankalin shi gaba d'aya baya jikin shi yanda yau yaga Husna........
YOU ARE READING
ABOKIN MIJINA
Historical FictionLabri ne akan Aminai guda biyu, Wanda d'ayan ya dage akan matar abokin sa akan lailai sai ya cika burin sa a kan ta. Menene wannan burin aboki akan matar aminin sa? Ku biyoni domin jin yanda labarin ABOKIN MIJINA yake!