Part 11

1.1K 32 0
                                    

        *♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] ‪+234 703 300 1537‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

            *©°•Jeedderh Lawals•°*

    *®°•Fikrah Writers Association°•*🖋

                         *51*

            Hasken rana daya haske min idanu ne ya katse min daddadan barci mai cike da natsuwa da nake yi. Na bude idanu na a hankali na sauke su akan agogo, karfe tara da kwata. Na maida dubana zuwa ga curtains din dakin wadanda aka daga sama, hakan ya ba haske da zafin rana damar lekowa ta cikin manyan windows din dakin. Abbu baya kan gadon kuma nasan da kyar idan yana toilet, ko ina ya shiga? Na tashi a hankali na nufi tagar da niyar rufewa, wani dan guntun murmushi ya subuce min lokacin dana yi tozali da terrace garden a bayan dakin, shuke-shuken roses da different flowers and plants ne wadanda suka kawata wajen matuka, ga wooden couch nan mai raga-raga kamar anyi saka a tsakiyar wajen inda zaka zauna ka huta, naja numfashi na shaki kamshin furannin har ina lumshe ido, sai dana gaji da tsayuwa sannan na saki curtains din, komawa nayi na yaye zanin gadon na je dakina na dauko wani na dawo na shimfida shi kuma dayan na jefa a cikin washing machine na shanya shi a nan cikin toilet din wajem da aka tanada musamman for laundry. Kayana na tarkata na wuce dakina, na jiyo motsi a kicin amma ban leka ba. Ruwa na tara mai dumi na shiga na kara gasa jikina don har lokacin ina jin zafin wajen, na daura babban towel a jikina na fito na zauna a gaban dressing mirror nayi goge-goge da shafe-shafe, kwalliyata nayi kamar yadda ya zame min Al'ada, na fesa turaruka masu kamshi mai kwantar da hankali, jiya naga Anty Shafa tana jera su a kan dresser din nasan ita ta sai min tunda Arabian perfumes ne ita kuwa yawanci irin turarukan da take amfani dasu kenan.
         Kofar dakin aka turo aka shigo, cikin sakan daya na juya na kalli wanda ya shigo na maida kaina kasa na dukunkune a tsakanin cinyoyi na. Ya tako a hankali har ya iso gare ni, kaina ya dago nufin shi in kalle shi amma na jimke idanuna, murmushi yayi mai sauti, "yau kuma a haka zamu gaisa Baby na?" nayi shiru ina kokarin janye fuskata amma yaki bani damar hakan sai ma mikar dani tsaye da yayi ya kalmashe ni a cikin jikinsa, ya dora habar shi a kan gashin kaina yace "babu gaisuwa ne yau?" kaina na kan kirjin shi na girgiza alamun a'ah, kaina ya sake dagowa nayi saurin kara rufe idanuna, peck naji ya bani a kunci da lebena kafin ya sake ni gaba daya, "it's okay, na fahimta. Kunya ta ake ji ko?  Yanzu zan fita a dakin, yi sauri ki shirya kizo mu yi break fast, yau da kaina na tattare hannun riga ta na hada miki break fast" idanuna suka yi walai cikin rashin sanin nayi hakan da tsananin mamaki, dariya yayi tare da dan jan hancina, "thank goodness I've got to see this beautiful eyes, yes ni na hada break fast now yi sauri kizo muci kafin ya huce, ko In zo in shirya ki da kaina?" wayyo nayi saurin girgiza kaina, yayi er dariya ya fita. Wardrobe na bude na ciro wani tausassan yadi ruwan madara riga ne da siket na saka, na lalubi silifas mai taushi na zura tare da yafa dankwalin a kaina da yake babba ne na fita.
          Yana zaune akan kujera yana duba waya ina fitowa ya tashi tsaye tare da wucewa wajen dinning nima na bi bayan shi, kujera yaja min na zauna a darare shima yaja ta kusa dani ya zauna. Kwallin kula daya ce a wajen sai flask na ruwan zafi da cups da kayan shayi. Ya hada mana tea tare da daukar plate ya bude kular ya juye abundance ke ciki, nayi shagaraa da baki ina kokarin tantance abinda yake gabana. What did you expect? Konanniyar wainar kwai ce tayi bakikkirin da ita, yasa fork ya yanki kadan ya kai bakinshi kamar mai testing, yace "kar ki samu da bakin da tayi pa, bata yi komi ba" a sanyaye na dauki fork nima na kwaikwayi yadda yayi, abu na farko daya fara ratsa min harshe shine dan banzan gishiri sai kuma dacin konewar da tayi ya biyo baya, ganin yana kallona yasa na takura tun karfina na hadiye kwan, take zuciyata ta tashi, ya daga min gira, "ya??" na dage tun karfina na kakaro yaken tare da mishi 👌 alamun good, yayi murmushi. Wata na sake cirowa na kai baki, wannan karon na jima a bakina kafin na iya hadiyeta. Na ja kofin shayin na fara sipping, gani ba gwanar shan shayi da madara bace. Shi kanshi daya kai loma ta biyu gani nayi ya dakata yana kallona, "kamar gishiri yayi yawa koh?" nace umh. Ya kara kai ta uku bakinshi na bishi da kallo tsigar jikina har tashi tayi, ba shiri ya furzar da ita ya lalubi kofin tea ya kora dashi.
         Kallona yayi yace "sorry baby, ko zaki zan sama mana wani mu ci? Da alamu na manta yadda ake girki ko don na jima ban yi ba?" kamar jira nake, na tashi na hade kan kayan na nufi kicin. Store dinmu shakare yake da kayan masarufi wanda nasan kila zai iya daukarmu shekara kafin mu ci rabin kayan, murmushi kawai nayi tare da girgiza kai, Daddy!.
          Cikin mintuna talatin na gama soya chips da plaintain, nayi vegetables sauce na dauka na kai mana muka yi break. Na tashi na hade kayan waje guda Abbu ya biyo ni da wasu. Na ajiye kayan tare da juyawa, da sauri Abbu ya riko hannuna, ban kalleshi ba na sadda kaina kasa, yace "are you ok Nafeesah?" na gyada mishi kai a hankali, yace "please Ki daina jin kunya na haka Baby, kin riga da kin zama ni kamar yadda na zama ke. I need you to be free, frank and comfortable idan muna tare, bana jin dadin hakan da kike yi. I know it'll be awkward, but still kiyi trying mana kinji?" na gyada mishi kai, yace "noo, amsa min da bakinki" na daga bakin da kyar nace "toh" ya kai bakinshi kan nawa ya dan tsotsi leben nawa kafin ya dago yana murmushi, "datz you baby...., zan fita yanzu me zan kawo miki?" nace "babu komi" yace "k, ki kunna kallo ko ki shiga dakina a study room akwai kayan exercise ko kuma just do anything so that you won't be bored don zan dan jima, sai na dawo" nace "a dawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya" yace "Ameen Nafeesah ta" ya juya ya fita bayan ya bani peck a goshi. Ni kuma na fara wanke kayan da muka karya dasu.

NI DA ABOKIN BABA NAWhere stories live. Discover now