***Saida ya sake ɗaure fuska ya ɓata rai sannan ya gyara tsaiwarshi ya kalli mutumin dake tsaye gaban shi cikin shiga ta kamala da kece raini,
"waccan da kake magana akanta ba aure zata yi ba infact ma tana da mijin da zata aura....." ya faɗa cikin ɗaurewar fuska, wani ɗan gajeren murmushi mutumin yayi sannan ya dubi matashin saurayin dake tsaye gabanshi cikin ƙananan kaya wanda ba zai haura shekaru 27 ba sai faman ɓaɓɓata rai yake yi,
" Haba ƙanina..... Ba zaka bani yayar taka ba? Ni ka bani dama kuma kayi min izni zan nemi soyayyarta da kaina...."
"malam na faɗa maka ba aure zata yiba wai ko dole ne?"
Daga haka ya ƙara gaba yana jan dogon tsaki duk da kiran da mutumin ke yi masa amma bai jira ya saurareshi ba,
Tana tsaye gaban mota tana jiransa hannunta riƙe da wayar hannunta tana latsawa, ganin yanda ta ɗaure fuska ya hanashi yin magana ya buɗe motar ta shiga har lokacin tana latsa wayarta, key yayi wa motar suka bar harabar gaban supermarket ɗin sannan ya kalleta,
"momcy......"
Dakatawa tayi daga latsa wayar da take yi ta kalleshi,
"ina jinka ubana...... Yau ma za a sake titsiyeni ayi min faɗan ne akan nayi bazawari?"
"mommy ba haka bane..... Nifa bama wannan maganar zan yi miki ba...."
"Autoh ai da naga da yake kai ne uban nikuma ƴar shiyasa"
Shiru yayi bai sake magana ba kamar yadda itama ta mayar da hankali wurin duba samfurin kayan da aka turo mata daga ƙasar dubai ta kafar sadarwa, har suka je gida hankalinta na kan wayarta, fita tayi daga cikin motar lokacin da yayi parking, shine ya rinƙa jidar kayan da suka zo dashi suna shigarwa ciki mai gadi yana tayashi, wani corridor yabi wanda zai sadashi da bedroom dinsa, kwanciya yaje yayi zuwa azahar ya fito bayan yayi salla ya nufi bedroom dinta, a bakin ƙofa ya tsaya yayi knocking har sau biyu kafin yace,
"momsy na in shigo?"
"shigo" ta faɗa cikin sanyin muryarta, buɗe ƙofar yayi ya shiga, tana kwance gefen gado tana waya, akan bedside drawer ya zauna yana jiranta har ta kammala wayar sannan batare da ta kalleshi ba tace,
"ya aka yi?"
"mommy dan Allah kuɗi zaki bani...."
Zaune ta tashi tana kallonsa,
"wai kai Ramad meyasa baka jine? Kuɗin nanfa nima ba a ruwa nake ɗebosu ba..... Kullum maganarka inbaka kuɗi inbaka kuɗi, yanzu me zaka yi da kuɗi?"
“mommy wayata ce fa ta fashe kalli ki gani.... Wallahi ko buɗewa bata yi... "
"ohhh ni hameeda ina ganin ikon Allah..... Ramadan last time dubu dari uku na baka ka siyi waya and yanzu ka sake dawowa da wata maganar daban...."
"to ki ara min mommy idan ba zaki bani ba"
Harararsa tayi kafin ta koma ta jingina da jikin gadonta tana sake maida hankalinta kan wayarta wacce kira ke shigowa,
"tashi ka fita zanyi waya anjima ka dawo sai muyi magana........"
"mommy wani abu kike ɓoye min kuma?....."
"kai, nace ka fita, excuse me please"
Tashi yayi ya fita yana ciccije lips, ko ja mata ƙofar bai yi ba ya wuce kitchen yana zancen zuci,"wallahi ba zai yuwu ba.... Wai ita mommy dole ne, tab, to wallahi this is not be possible" abinci ya zuba ya fita falo ya ɗauki remote yana ci yana kallon wrestling a tashar sports channel, jin motsin fitowarta yasa shi ɓata rai, zama tayi tana kallonsa,
YOU ARE READING
BAƘO........
RomanceMatashi ne mai ji da kansa wanda baya taɓa ɗaukar reni sai dai yana da wata ɗaɓi'a guda ɗaya...... Baƙo ba asan halinka ba!!!