***Murmushi kwance akan fuskarsa duk da shi ba ma'abocin yawan murmushin bane ya buɗe gaban motar ya zauna yana kallon wanda ke zaune awurin zaman driver,
"wai tun yaushe ka shigo garine?"
"just ɗazu ɗazun nan Ramadan"
"amma sai yanzu ne kake tunawa dani?"
"ba zaka gane bane abokina..... Da banma yi niyyar kiranka ba har sai nagama zan wuce sai in zo mu gaisa daga nan in tafi"
Murmushi yayi bayan ya maida hankalinsa kan titi bayan sun soma tafiya,
"saboda me? Kai baka son nima in samu irin ladan da ka samu wurin tarairaiyar baƙo? Baƙo fa rahama ne kuma alkhairi ne annabi da kansa yayi umarni da mu girmama baƙonmu....."
"to ai ni lokacin da kaje garin mu inada masaukin da zan baka amma kai bani da masaniyar ko kana da inda zaka saukeni ko akasin haka, sannan ku rayuwarku tasha banban da tamu, ku idan za azo sai an sanar daku saɓanin mu da ko yaushe mutum yazo muna maraba dashi "
" lallai Abdallah hakama zaka faɗa? To waye ma ya faɗa maka wai banida masaukin da zan saukeka? Muje kaga girman gidan, duk girmansa mu 4 ne kaɗai aciki"
"to shikenan ayi min afuwa"
Ƙarar Wayarshi dake cikin aljihun wandon jeans ɗinsa itace ta katse musu maganar da suke yi, ganin sunan umma wato mahsifiyarshi ya sashi katse kiran tare da kiranta,
"wa'alaikumussalam.... Umma ina yini, alhamdulillah.... Ehh nasameshi, gashi ma har zamu tafi gidansu.... Amin umma, to sai da safe"
Jin wannan maganar da yake yi ya tabbatarwa da Ramadan cewa mahaifiyarshi ce, hira suka cigaba da yi har suka ƙarasa gida, tun daga waje Abdallah yake bin gidan da kallo har suka shiga ciki, dama jikinsa ya jima yana bashi cewa Ramadan ba ɗan talaka bane, haɗuwar da yaga gidan yayi ya sake tabbatar masa da hasashensa, bedroom ɗin Ramadan suka shiga domin babu kowa acikin falon gidan, bedroom ɗin ya ƙawatu kamar na mace komai tsaf tsaf kuma fes fes, ga makeken gadonshi mai kama da na mutane biyar dark blue kusan komai dake cikin ɗakin ma dark blue ne jakarshi ya ajiye sannan ya zauna bisa saman gado yana bin cikin ɗakin da kallo domin Ramadan ya fita. Mintunan da basu wuce biyar ba Ramadan din ya shafe kafin ya dawo cikin ɗakin,
"muje ka ɗan sha ruwa ko..."
Miƙewa Abdallah yayi yabi bayansa yana sake bin ko ina da kallo har suka ƙarasa wurin da aka tanada domin cin abinci, zama suka yi dukkaninsu kan table Ramadan ya fara serving din su, tuwon shinkafa ne miyar taushe da tantakwashi yasha man shanu sai lafiyayyen zoɓo mai sanyin gaske cikin glass jug, tuwo guda uku ya sakawa Abdallah sannan ya zuba masa miya fal cikin wani ɗan madaidaici kwano na tangaran,
"wannan abincin fa ina zan kai shi?"
"cikinka, ka daure ka cinye shi ko zaka fi jin daɗin bacci"
"zan dai iya cin ɗaya da rabi zuwa biyu"
"a'a dan Allah ka daure ka cinye"
"to bari in jarraba"
Abincin suka fara ci suna ƴar hira jefi jefi, Ramadan dinne ya fara tashi ya shiga ciki,bedroom ɗin Hameeda ya shiga wacce ke zaune gefen gado tana shirin bacci saboda da wuri take son kwantawa dalilin zirga zirgar da ta sha,
"mommy..... Ɗazu na leƙo kina salla" ya faɗa yana ƙoƙarin zama gefen gadon,
"me ya faru?"
"mommy baƙo muka yi....."
Dakatawa tayi da abinda take yi ta kalle shi,
"baƙo kuma?"
"ehh mommy baƙo..."
"to daga ina?"
"daga Kaduna.... Mommy zaki iya tuna wata tafiya da nayi zuwa Katsina lokacin hutun season da muka yi har nayi dare a Kaduna motana ta lalace kika ce in bari saida safe sai intaho in zauna in kwana?"
Ɗaga masa kai tayi alamar tunawa,
"to shine wanda na kwana awurin sa"
"OK, amma dai ai ka tabbatar mutumin kirki ne ko? Bana son ka rinƙa yin abokai barkatai Ramad...."
"mommy baida wani problem wannan guy ɗin"
"to shikenan, zuwa yaushe zai zauna tare damu?"
"mommy ban tambayeshi ba but na san ba zai wuce 1 week ba"
"Ok shikenan babu matsala, you can go"
Tashi yayi yafita nan ta cigaba da shirin baccinta.
Wurin Abdallah ya koma wanda har lokacin yana saman dining a zaune yana latsa wayarsa,
"muje kayi salla sai ka kwanta ka huta ko"
"ok toh, nagode"
"karka damu ana tare"
Sai bayan da suka idar da sallar isha sannan Abdallah yake sanar dashi maƙasudin zuwanshi garin wato yazo ne zai yi interview na neman wani aiki, da wuri ya kwanta saboda yana son ya tashi da wuri kar ya makara gobe, ai kuwa asubar fari ya tashi yayi sallah yayi duk addu'o'in da ya kamata yayi sannan ya shirya bayan ya tashi Ramadan, suit yasa wadanda suka yi masa kyau mutuƙa, misalin ƙarfe 7 ya tafi duk da Ramadan yana ta ce masa ya tsaya yayi breakfast ko tea yasha amma yaƙi yace sai ya dawo.
Misalin ƙarfe 9 da kusan rabi ya dawo gidan ranshi a mutuƙar ɓace fuskarshi babu annuri ko kaɗan, mai gadine ya buɗe masa gate ya shiga, nan gaban balcony ya hango wata farar budurwa tsaye tana yin waya ta jingina da jikin ƙarfen da aka gewaye balcony ɗin, sanye take da pink ɗin riga ta bacci mai ɗan kauri kanta ta yafa wani ɗan siririn mayafi wanda zai baka damar hango manyan kitson kalabar dake kanta wanda ta haɗasu ta ɗaure da jan ribom, ƙafarta takalmi ne na roba me kama da silifas, kallonsa tayi shima ya kalleta sannan ya wuce batare da yayi mata ko sallama ba,kai tsaye bedroom ɗin Ramadan ya wuce amma bai same shi a cikin ɗakin ba sai dai ya jiyo motsin shi acikin toilet yana wanka, zama yayi gefen gado yana rage kayan jikin sa, wayar shi ya ciro daga cikin aljihu yana duba miss called din da aka yi masa, umma ya gani dan haka ya soma kiran ta bugu biyu ta ɗauka,
"umma wallahi ba a dace ba, sai fa da muka je muka taru sannan suka ba mu haƙuri wai anɗaga interview ɗin idan za ayi zasu sake neman mu..... Sai bayan da suka wahalar damu...."
Daidai lokacin Ramadan ya fito daga cikin bathroom, sallama yayi da umma ya juya ga Ramadan ya soma yi masa bayanin abinda ya faru,
" neman aiki dama ya gaji haka, ka ƙara haƙuri sannan a cigaba da nema insha Allah wata rana za a dace..... Yanzu ka tashi kaje kayi breakfast"
"kai anya kuwa zanyi breakfast ɗinnan? Ai ni da yanzu ma kawai nake son in tafi in shiga mota in wuce gida"
"a'a, haba dan Allah kamar ana korarka? Daga zuwa jiya, ka bari ka huta, nima mommy ce zata aikeni yanzu ka bari in je in dawo"
Daƙyar Ramadan yasha kansa ya yarda akan zai sake kwana, tare suka fito da Ramadan ɗin ya hau kan table domin karyawa shi kuma Ramadan ya wuce wurin Hameeda, babu jimawa ya fito yana riƙe da mukullin mota yayi waje, shi kam Abdallah breakfast din shi yayi hankali kwance sannan ya tashi ya koma ɗaki yaci gaba da kallon wani nigerian film a makekiyar talibijin din bangon dake cikin ɗakin, shiru shiru yana ta zaune shi kaɗai Ramadan bai dawo ba har ya gaji da zaman domin misalin 12 da kusan rabi kenan na rana, wayar shi ya ɗauka ya fita, yana fitowa falo ya hango budurwar nan ta ɗazu da ya gani zaune kan kujera da laptop akan cinyarta hannunta riƙe da cup tana kurɓar tea,
"sannu ko" yace da ita tare da wucewa yafita compound ɗin gidan domin rage lokaci......
DU LIEST GERADE
BAƘO........
RomantikMatashi ne mai ji da kansa wanda baya taɓa ɗaukar reni sai dai yana da wata ɗaɓi'a guda ɗaya...... Baƙo ba asan halinka ba!!!