*ONE BLOOD*
_Mallakin_ _Nu'aiymah Abdull Tafida__Alhmdllh am back, dear ones, I come back to you in my new book, One Blood, with many wonderful and wonderful lessons, Challenges for us women._
_Dedicated This book to my lovely Tween sis Na'imah Abdull Tafida, Half of my sister half body and fighting partner of my blood, I love you Twinny_ ✨😍
_Episode 1&2_
Harara na gallawa kofar falon tamkar idanuna zasu fado kasa dan massifa, cike da tsantsar takaici na juyo ina watsawa Inna wani banzan kallo da ya kusa firgita 'yan hanjin cikinta, sai dai bata nuna ba sai ma gyara zaman ta da tai tana wani tabe baki gamida kallona a kaikaice tana gutsirar goron hannunta tace. "Ke kam kin shiga uku Nu'aiymah, na rasa wane irin danyan Kaine dake haka."? A fusace na figi hijabina na fice a folon bayan na dauki wayata cike da jin haushin Inna. Direct inda yayi parking din motar sa na nufa ba tare da nayiwa kowa na gidanmu sallama ba dan haushin kowa nakeji babuma kamar Inna dan itace ta batamin kudirina na yau akan Ya Abdull. Tsaye na samesa ya hade hannuwansa a kirji ya juyamin baya dukkan alamu dai sun nuna waya ya keyi. Tsaki naja ciki-ciki cike da jin haushinsa a raina dan wallahi nidai Allah ya gani na tsani wannan bawan Allah'n babu dai yadda zanyi ne kawai, banbi takansa ba na bude murfin motar na zauna ina huci da girgiza kafa kai kace yana gani na, kusan few minutes naji daddaden turaransa mai sanyaya zuciya da bargon jiki ya daki kofofin hancina, hakan ne ya tabbatar min da shine ya shigo motar, ai da sauri na dauke kaina gefe inajan tsaki ciki-ciki ta yadda bazai jiyo ni ba!. Jin shiru bai tada motar ba yasa na saci kallon sa ta gefen ido, sai a sannan na kare masa kallo dan tun safe da ya kawoni gida rabon da in sakashi a idona sai yanxun da yazo daukana. Kishingid'e yake saman kujerar motar yana sanye cikin uniform d'in sa na kakin soja ga alamun dai dawowar sa kenan daga office ko gida bai tafi ba, ya rufe kwayar idonsa da bakin eyeglasses d'in da sukayi massifar yi masa kyau ya karawa kyakkyawar farar fuskar sa ma'abociyar kyau da kwarjini kyau sosai, a hankali yake tauna cingam din bakinsa kas-kas kai kace wani mace, gabadaya hankalin sa na kan wayarsa yana dannawa. Harara na watsa masa ta wutsiyar ido caraf muka hada ido dashi, dauke kai nayi gefe gamida tamke fuska, ko ban juyo ba nasan ni yake kallo bai kai ga furta komai ba muka juyo karar kwankwasawar gilas ta gefen sa. A tsorace Leyla ta miko masa kwandon hannunta tayi mana sai da safe ta wuce bangarensu, ya ajiye kwandon bayan motar ya figi motar da gudun tsiya bayan security's d'in sun bude masa kofar muka fice. Har muka iso gida idanu na a lumshe suke saboda baccin da nakeji, bai ko gama yin parking ba na fito daga motar na shige bangare na. Nu'aiymah na fita daga motar Abdull yabi bayan ta da kallo cike da takaici. Shi kam kwata-kwata ya rasa meke damun yarinyar nan wani lokacin har tambayar kansa yake anya ba Aljanu ne da'ita ba? Dan rashin kunyar ta da tsiwarta gareshi kan bashi mamaki dan dama tun can! Shi ba wasa yakewa yaran gidan nasu ba gabadayan su tsoransa da shakkar sa suke massifar yi sabanin ita, bazai ga laifin ta ba dan ta rainashi dan dama tun can! Iyayen nasu ne suka janyo masa wannan rainin da suka aura masa wannan 'yar cikin sa dan ya tabbata inda ace yayi aure da wuri da ya kusa haihuwar kamarta. Lol🤥 badan iyayen nasu sun kasa hakuri kuma sun tsani matarsa ba tun can! da mezaiyi da wata Nu'aiymah?, wannan wace irin rayuwace *RANA ZAFI INUWA KUNA* (my last book 200 naira) ya ajiye mata biyu a gida amma babu daya wacce zaice yanajin dad'in zama da'ita kowacce da tata matsalar. Zazzafar iskar bakinsa ya furzar gamida lumshe idanunsa. Ya kwashe kusan Mintuna goma sannan ya fito ya nufi d'aya part din dake facing din na Nu'aiymah. Tana zaune ta hakimce a had'adden falon nata wanda tsaya fada muku tsaruwarsa da kyawunsa wallahi zamu bata lokaci ne amma na bawa kowacce dama ta kiyasta da kanta. Sai dai rashin gyara da kulawa ne yay masa cikas, falon ya tsaru iya tsaruwa sai dai babu abinda ke tashi a ciki sai wani hamami da karni, sanye take cikin katuwar bakar ti-chert mai gajeren hannu da zanin Atamfa, kayan fruits ne a gabanta tanata faman chatting, Tana ganin shigowarsa ta mike da sauri ta fada jikinsa tana shakar daddaden k'amshin turarensa. A hankali ta dago tana kallonsa cike da ta6ara mai game da zallar shagwa6a take Fad'in. "Bb is it now or not?" Ta fada Tamkar za tayi kuka. Janyeta yay daga jikinsa da sauri sakamakon wani irin tsami da doyi da ya daki kofofin hancinsa lokaci guda, baice komai ba yasa hannu ya shafa gurgurarren gashin kanta da ya cukurkude wuri guda saboda rashin gyara, kwandon hannunsa da ya shigo dashi ya ajiye gefe cikin dabara ya dauke kai duk dan kar ta fahimci halinda yake ciki dan lumfashinsa har wani sama-sama yakeyi, cikin dakiya yace. "I'm so sorr.." "For What Bb? Tambayar ka kawai nayi fah." Ta fada tana kwabe fuska cike da tsantsar Sangarta, baice uffan ba yaja hannunta suka karasa cikin falon ya zauna itama ya zaunar da'ita saman cinyarsa yana kawar da kai daga warin bakinta yace. "The same is true of a husband without a hat and a flirt? I'm very busy today and I'm coming back." Ya fada yana lakace mata hanci yana kokarin danne bacin ransa ya kakalo murmushin dole. Kara lafewa tayi a jikinsa tace. "Shine kuma na ganka tare da waccan yarinyar har warhaka bacin kasan yau girkina kuma har warhaka kuna tare? Haba Bb ai kaima kasan kun shiga hakkina." Ta fada wani zunburo baki, Murmushi kawai yay ya shafa kanta ya raba jikinta da nashi ta hanyar mikewa tsaye yana fad'in. "Hum Mata you are the parents of jealousy. That is why you forgot this morning I took Nu'aiymah home." 'Yar dariya tayi cike da yake tana kai masa dukan wasa a kirji tace. "Kai ko hum." Katseta yay da Fad'in, "Kinga ba wannan ba ni yunwa nake ji ga abinci nan dana karbo mana gun Mami yau mun huta da cin abincin restaurant ki shirya mana dinner zanje na watsa ruwa na sakko." Daga haka ya haye upstairs zuciyarsa na tashi ya bar Zuhrah nan tsaye cike da takaici jin yace daga gidan Mami ya amso abincin bama Ummah ba. Yana shiga ya rage kayan jikinsa ya rage daga shi sai boxer ya hau gyaran dakinsa babu ji ba gani dan Abdull shegen kyankyami da tsabta ne dashi dako wata macen wlhy Albarka, yana gama gyaran dakin nasa dake a bangaren Zuhrah ya fada toilet ya wanke tas sannan yay wanka ya fito daure da Towel a kugunsa, yana tsaka da tsane ruwan jikinsa ta shigo dakin zugum-zugum babu ko sallama, tsayawa tayi tana kallonsa tamkar zata hadiyesa, takowa tayi a hankali zuwa garesa da sauri ya daga mata hannu duk da ba ita yake kallo ba but tsaf ya kare mata kallo a jikin madubin, a nasa tunanin yanxu da taga dawowarsa zataje tayi wanka ta canja kayan jikinta masu tsami ne amma kash! Ya rasa wace irin ballagazar mace ce Zuhrah tun yana mata nasiha har ya dawo yana mata gwari-Gwari amma taki sauyawa shiyassa ya zuba mata na mujiya tana duk abinda taga dama, hatta kwanciyar aure inba shine yay bukatarta ba ya nemeta toh fa ita bazata nemesa ba, abu daya ta kure wajen yinsa shine dure-duren shan maganin mata nasha dana matsi ita a nata tunanin ta wannan hanyar ne kadai zata mallaki mijinta a tafin hannunta😆. Abdull ya kkatseta da fadin. "Nace kije kiyi wanka ki sauka muci abinci." Ya fada da kyar yana kokarin bude drowar kayansa, a fusace tace. "Bb me kake nufi ban fahimta ba wannan wane irin wulakanci ne."? Wani irin kallo ya watsa mata da ya kusa firgita ta sai dai bata nuna ba ta fice daga dakin fuu! Gamida banko kofar dakin ji kake garam. Tsaki yaja ciki-ciki cike da takaici ya janyo doguwar jallabiya ruwan milk ya dauki freshner ya feshe dakin dashi dan ta canja masa kalar k'amshin dakinsa da doyin jikinta, shima ya feshe jikinsa da turarukansa masu sanyin da k'amshin dadi ya sakko kasa. Baiga Zuhrah a falon ba abincinsa ya zuba yaci yay nak sannan ya deba a plate ya nufi bangaran Nu'aiymah gudun kar ta kwana da yunwa dan yasan zafin kai irin nata bazaisa tazo taci abincin ba duk da kuwa tasan ba Zuhrah'n ce ta dafa ba.
YOU ARE READING
ONE BLOOD
FantasyOne blood, Labari ne akan wasu 'yan uwa na jini da kwata-kwata babu jituwa a tsakanin su.