Rayuwarmu
❣❣❣❣❣❣Da sunan Allah mai rahama mai jin kai zan fara wannan littafi mai suna ( Rayuwarmu) wanda ya kunshi soyayya,sadaukarwa tausayi yanuwantaka littafine da yaxo da sabon salo mai kayatarwa.
Daga ni taku ayshart sani ajah ajarh'scakesandmore.By Ayshart sani
1.
Da gudu ta fito daga dakinta tana kwalawa Mami Kira wani saurayi ya biyota a baya shima da gudu ya biyota Bata dire ko Ina ba Sai a bayan wata matashiyar Mata me kyan jiki bazaka taba dauka ta manyanta da yawa ba,Tama ta haki tace Mami Dan Allah ki yiwa Yaya affan magana Kar ya dakeni tace me kikayiwa affan din tace Allah banyi Masa ba komai shikuwa affan tunda ya ganta a bayan mahaifiyarsu yaja ya kikam Dan duk abinsa Bai Isa ya daketa tana bayan Mami b.
Kallonta yayi yace Allah y kawo Yaya haidar in fada Masa tanajin sunan daya furta ta fito tace ga ni Dan Allah kayi hakuri Kar k fada masa wallahi dukana zaiyi dai dai lokacin taji ance meye bazaa fadamin ba da sauri ta juyo kanta tace ba komai tana kallon affan sai a lokacin haidar yayi sallama mami ta amsa tare da yi masa barka da zuwa,y gaisheta tareda kallon affan yace bros how per yace lpy kalau yaya sai dai wannan yar rainon naka sai ka kara kaimi gurin rainon ta Dan naga kamar tafi da iskanci kallonta yayi tareda girgiza kai ya wuce yayi dakinsa dan ya watsa ruwa yayi alwala suka wuce masallaci kasancewar lokacin magriba ya gabato.
Mikewa mami tayi ta kalleta tace ai sai ki tashi kema kiyi haramar sallah ko tana zunburar baki ta mike ta shige dakinta sai da akayi har sallar ishai sannan suka dawo gida dan aladar mahaifinsu ce yin magriba da isha ba tare da ya dawo gida ba shiyasa har yanxu da alaj yayi masa rasuwa wannan aladar bata barsu ba, har akazo dinner mutuniya bata fito ba mami ta kalli affan tace dubo min waccan yar me takeyi a daki har yanxu bata fito ba ba yadda zaiyi haka ya shiga dakin tana gaban mirror tana kwalliya ya kalleta cikin mamaki yace lallai wai ke killing sai an jiraki in zanyi dinner tayi masa banza yace afrah wa kikewa kwalliya ta kallesa ta dauke kai tace ya haidar y kwashe da dariya sannan yace lallai yarinya baki da hankali ni malama mike ki wuce ana jiranki tun dazu ni kina bata min lokaci ta mike tare da cewa ai n gama haka ya taso ta a gaba har gaban mami ta kalleta tace kin rainani ko afrah bana hanaki wannan haukar kwalliyar ba shikuwa haidar tunda ya kalleta sau daya bai kara ba tace mami kwalliya ce fa ba hauka ba duka mamin ta kai mata tace zan bigeki wlh wai ke aljanune dake Allah ya tsare mu dasu tayi dariya tace aa mami tace maza kisa hannu kin tsayar da mutane daga cin abinci.
Ganin haidar bai mata magana ba tace ya haidar bakace nayi kyau ba ba haidar ba shi kansa affan sai daya kware mami kuwa gabanta ne ya yanke ya fadi tana dago kai sukayi idk hudu da haidar ta fuske ta cigaba da cin abincinta ganin bai kulata ba tace yaya ya dago fuskar nan kamar mutuwa ya ce wallahi zan mareki bana hanaki magana in kinacin abinci ba ta zunburi baki karaf akan idonsa ya kuma kallonta ganin ta waske ya shareta har aka gama cin abinci bars kara magana ba dan it's har ga Allah tana matukar tsoron ya haidar.
Bayan gama cin abincinsu aka koma falo dan yin hira amma haidar ko kallon gurin hirar bayayi Dan yanxu afrah mamki take basa matukar gaske,affan da afrah keta faman magana mami ma yau abin ya dameta .
Ayshart sani.
YOU ARE READING
Rayuwarmu
Romancerayuwarmu littafi me ciki da tausayi,sosai sadaukarwa da Kuma kaunar juna