Cinyarsa! Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya mai sanyi Abbu ya sauke yana lumshe idanunsa, da sauri Akeela ta ɗaga jiƙaƙƙun eyes lashes ɗinta zuwa sama kafin a hankali ta buɗe idanunta tare da sauke Kallonta a fuskarsa Abbu wacce take dab da tashi.
Wani sassanyan Murmushi ya sakar a hankali kuma cikin sakin fuska yace..
"Babyna Daughter na"
Ƙuri tayi masa da idanu, saboda kamarsa da Mutumin ɗazo, she's a cleaver gal amma muguwar taɓararriyar mai saurin kuka, ko dan yawan ciwonta ya sanyata kuka ohhhu?!
Tana da ilimi sosai musamman na addini bata wasa da sallah sam komai tana da tsari.
Murmushi Abbu ya sakar mata yana shafa sumar kanta dai-dai fuskarta yace.
"You're wake up Babyn Abbunta how do you feel now? Ya jikin?" Ya faɗa yana manna mata kiss a goshinta a hankali ta zame jikinta daga kan cinyarsa tana ɗan marai-raice fuska kamar zatai kuka da sauri tace "no don't cry kinji" kai ta ɗaga masa tana lumshe idanunta can kuma ta buɗe murya can ƙasa kamar bata son yin magana tace "uhm who are you?" Shafa cikinsa yay kafin ya gyara zamansa tare kama fararan hannunta wanda suke da mugun taushi kamar auduga yace.
"Ok let me introduce myself to you" shiru yay yana kallon tana jin wani irin masifafan yanayi a kanta kafin ya numfasa yace.
"I'm Abubakar Bello, but some of people knowm me as Bukar, I'm the second born Of my parents, ina da big bro but he's passed away wajan shekaru masu yawa, babban yaya ne shine your father, Isma'il Bello kenan, we lost our father good 30yrs kenan, ina tare da my mother we called her Didi zaki ganta kamar su ɗaya da Aleema, seriously i love her irin sosai ɗin nan more than anything dake nan duniya, bayan ita ina da yara 4 my first son ɗina yafi komai muhimmacin a rayuwarta his name is Abdul-hakeem Bukar Bello zaki iya cewa Yaya, ko hero ko Hamma like yadda Fulani suke faɗa, sai Adnan we lost him shima amma komai ya faru it was a destiny, sa kuma Aleema sai auta Afaf amma yanzu bani da wata Auta sai ke Babyn Abbunta" ya faɗa yana jan hancinta, ɗan Murmushi tayi wanda yasa numfashin Abbu kusan ɗauke wa, domin wannan Shine karo na farko da tayi Murmushi wanda ya haddasa lomawar dimples ɗinta tare da teeths gave ɗinta wacce take siririya sosai, numfashi ya sauke yace.
"Ina da mata guda biyu ta farko sunanta Ayusher we called her Ummi, sai Khadijertou muna ce mata Mami, Nayi karatu mai yawan gaske, ni mai kuɗi ne the richer old man, ada nayi siyasa sosai amma yanzu na sauka, yanzu ina business ne ina da Manyan companies a nan 9ja da kuma ƙasashen waje, ina da manyan contact, ƙwangila kala-kala Allahamdulillah ina duba na ƙasa na ina taimako samuna bai tashi a banza ba, and duk da hakan komai na gidan nan Akeem ke yinsa baya using Kwabo nawa tashi yay ya nema duk yawan dukiyarsa shi ya nema da kansa babu sa hannu na, yana da faɗin rai koni sai nayi da gaske nake juya sa dan yana mugun suna ne yana da biyayya yana da ilimin addini fiye da tunanin mutum I'm so proud of him Wannan shine kawai"
Kallonsa tayi ba tare da tace komai ba shi dai yaji daɗi yana da kirki amma wannan ɗan nashi bashi da mutunci ko kaɗan, har yanzu ta kasa mance abinda yay mata har yanzu kuma tana jin ƙamshin turarensa a jikinta kamar zai zautar da ita.
Bata san mene yasa ba sai kawai ji tayi kuka ya kwace mata, da Sauri Abbu yace "Subuhanallah what happened ina ke maki ciwo" girgiza masa kai tayi tana kwaɓe fuska tare da tura baki gaba "Okey tell me mene ne?" Cikin shassheƙar kuka tace "Baffa na bai so na, he doesn't care about me zai haɗani da wani mai fitsarin ƙwance and ƴarni ɗin nan zaiwa Aure uhm" ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka ita tana ganin ai kamar abin kunya ne a gareta mutane suji za'ai mata Aure wata muguwar kunya ta keji kamar me.
Bakinsa ya buɗe yace.
"No one's forcing you to get you marriage Babyn Abbu Autata Ohyyyah come here" ya faɗa yana jawota jikinsa tare da fara rarrashinta wani sabon sonta ya ratsa mata zuciya.
Akeela kam ganinsa take tamkar Baffanta Musamman da taji yace shi ƙanin Baffan tane.Gyara zama Didi tayi tana kallon mutumin tace "Shikenan lashe baki yana tsotse laɓɓansa dan Allah Wannan ai sai ya jamin abin faɗa ko ba haka ba? Mugun hali kuwa bai bar kuwa ba ranar nan balango nace ya siyo min yaƙi to dan Allah ina imani a nan? Taimako nefa abin ma da dukiyar tasa babu san tayaya akai ya rata ta ba, ai ba kayi magana ba ace Hassada bace ba" ta ƙare maganar tana goge hancinta gaba ɗaya mutanan wajan Murmushi suke domin sun fahimci kawai rikicin tsofa ne murmushi mutumin yay kafin yace "In sha Allah Hajiya babba zamu kirasa" da sauri tace "kuce Ubanwa ya faɗa maku a'a babu ruwan ai assurru ma'al sirri koba gaskiya ba, kawai ai faɗa masa ko dan tsire da kaza mai zafi ce yana kawo min" jinjina kai yay yace "to shkknan yadda kikace haka za'ai" tashi tayi Bala driver yana biye da ita a haka suka nufi mota tana shiga ya jata zuwa gida.
A wajan 6 na yamma motar Akeem tayi parking a parking space, P.a ne ya fito tare da buɗe masa ƙofa, gently ya fito da ƙafarsa yana wani lumshe idanunsa tare da sauke ajjiyar zuciya a hankali yake motsa bakinsa yana tasbihi a ransa, ya gaji sosai domin rabin aikin a hospital yay ga program ɗin da zai fara a M.hausa channel, a hankali ya wani ya motsa fuska yana cije bakinsa wani siririn tsaki yaja ganin kallon da P.a ke masa dariya p.a yay kafin yace "Sorry sir" banza yay masa yana shigewa cikin gidan, juyawa p.a yay zuwa gida.
Lokaci daya shiga Afaf ce a Parlo da Aleema sai Akeela dake kwance saman duguwar sofa tana bacci gashinta duk ya rufe mata fuskarta, ga wani ƙaramin Teyana wide-leg trousers dake jikinta sai Applique logo detail t.shirt jikin nan nata sai glowing yake.
Wani series film suke kalla mai suna My perfect husband a zee world.
Da sauri Afaf tace "Wlcm Hero" harara ya watsa mata cikin sauri ta ɗauki remote tare da kashe kallon.
Ɗauke kai yay ya nufi upstairs, yana shigewa Akeela ta sauke ajjiyar zuciya yana dafe ƙirji dariya Aleema tayi tace "Laa! so you're pretending kenan ai kam zan faɗa masa" kwaɓe fuska tayi tana langwaɓar da kanta gefe alamar "No" ba tare da tace komai ba kuma.
Wanka yay ya sauya kaya zuwa Racing jersey da tracksuit trousers, a hankali yake sakkowa daga steps ɗin benen idanunsa a lumshe yunwa ya keji sosai sai baza ƙamshi yake yana tafiya kamar so, kai tsaye kitchen ya nufa domin samun mayen nasa Coffee da ice cream domin ya duba gaba ɗaya ya shanye ice cream part ɗinsa, yana shiga ya rufe ƙofar kitchen ɗin tare da jingina da jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa.
Tana tsaye a kitchen ɗin tana haɗa tea sai zabga madara take a mug ga kyawawan ƙafafuwan ta a waje ƙafarta sanye cikin wani slippers ga laft tummy ɗinta a lafe ya ƙara fidda shape ɗinta, a sanyaye take komai kamar bata so tana gamawa ta ɗauki mug ɗin tana juyawa idanunta ya sauka a kansa tsananin tsoro da gigicewar da tayi yasa gaba ɗaya ta saki mug ɗin cikin rashin Sa'a gaba ɗaya tea ɗin yay masa ka! Nan da nan fuskarsa tai ja idanunsa ya ƙanƙance ya wani haɗe fuska ta mau a hankali kuma ya fara takawa zuwa inda take tsaye....*TSINTACCIYA*
NRML GRP ₦300
VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616*NOTE*
NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.*FITATTU HUƊU🔥*
BAƘAR FATA
AutaR ManyADATTIJON ARZIƘI
Real ladingoSULTAAN
Mss flowergaba ɗaya ₦800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218*SARAUTAR MARUBUTA*
YOU ARE READING
TSINTACCIYA
RomanceRayuwa mai ɗauke da ƙunci da kuma tarin baƙin ciki, Yayinda hasken wata ke fitowa yana haskaka samaniya, a lokacin ne kuma zuciya keyin zafi da wani irin tafarfasa, Idaniya sun makance dalilin zubar Hawayen da ban san yaushe ne zai tsaya ba, Ina ji...