PART 1

192 4 0
                                    

*'Ta ƙi Aure... Part one
*Na Fatima Abubakar Saje
* Ummuadam.

GODIYA

Bismillahir-rahmanir-rahim.

Ina mai miƙa godiya ga Allah subahanahu wata ala mai kowa mai komai daya bani ikon fara wannan rubutu mai albarka in sha Allah. salati marar adadi ga fiyayyen halitti manzon tsira annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam.

Godiya ta musamman ga iyaye na tare fatan rahama a garesu duniya da lahira.
Bazan manta da miji na ba wan da kulawarsa, taimakonsa tare da sadaukarwan sa gare ni ya zama silar kasance wata a wannan matakin da nake a halin yanzu.

'Yan uwana da dangi na tare da yara na, ina muku fatan alkairi tare da addu'a Allah ya kare ku ya ƙara dankwan zumunci tsakaninmu.

Bazan manta da ɗaukacin al'umar musulmi ba, ina fatan Allah ya mana gafara, ya jiƙanmu, ya yalwata mana arzukinmu sannan ya haɗa kan ahlus-sunnah a duk in da suke.
Allah ya sauƙaƙa mana tsadar rayuwa, ya bamu aminci da nitsuwa, ya yaye mana musiba da bala'i, ya shiryarda mu da 'ya 'yan mu da zuriyarmu baki ɗaya. Amin.

GABATARWA

"Taƙi Aure" labari ne da na ƙirƙira kuma na rubuta dan faɗakar da kaina da kuma sauran 'yan uwa musulmai baki ɗaya, musamman mata.

GARGAƊI

Ni nake da hakkin mallakar dukkannin rubutuna, ban yarda ayi amfani da shi dan wata manufa ba sai da izini na.

BAYANI

Idan wani sashin labarin yayi daidai da labarin ki/ka to an samu cin karo ne kawai amma ba da niyya ba.

Ina maraba da gyara, ƙorafi ko shawara daga gare ku. Ina fatan wannan littafin ya amfane ni da ku baki ɗaya. Amin.

~~~~~<<<<>>>>~~~~~

(GIDANSU SAWWAMA DA ƘAWWAMA)

Mahaifiyar sawwama da ƙawwama na zaune a ɗaki ta zuba tagumi kai kace saƙon mutuwa aka faɗa mata, malam iro ya yi ta sallama amma ko gizau bata yi ba hakan ya tabbatar masa ta yi nisa cikin tinani. Wai haryanzu bazaki cire damuwa a ranki ba gameda auren yarannan sai kace kice uwa ta farko da yaranta suka kasa auruwa?
Dogon numfashi mama ta ja tareda sauƙe hannunta ƙasa tace malam kenan ai "ruwan da ya dakeka shine ruwa" ko da ace bani kaɗai bace amma nawa na sani, wannan shekaran sawwama zata cika shekara talatin da biyar ita kuma ƙwawwama zata cika shekara talatin da biyu amma ace haryanzu suna gida basu yi aure ba! Duk inda na shiga sai an nuna mun yatsa ana gata can yaranta sunƙi aure. Malam ya kaɗa kai yace wannan gaskiya ne dan ko ni sai kinga irin kallon da ake mun a waje wai har cemun suke ko ni zan auri yaran oho.

Haka iyayen sawwama da ƙawwama suka ci gaba da tattaunawa akan babbar matsalar da take damunsu na rashin auran yaransu da wuri.

A gefe guda kuma sawwama da ƙawwama na zaune a ɗaki suma suna tattaunawa akan al'amarin da iyayensu ke magana akanta inda ƙawwama ke cewa abunda ake mata na tsangwama a cikin dangi da ƙawaye yana damunta "yaya sawwama har kunyan shiga taron biki ko suna na keyi saboda sai kiga yara ƙanana suna mun kallon raini dan kawai sunyi aure wasu ma sun haihu ko hira ake na haihuwa da na sa baki sai kiji suna cemun inbar wanda suka sani suyi magana, cikin sanyin murya sawwama tace bai kamata ki ɗaga hankalin ki ba my sister ai kowa ya san aure da arziki lokaci ne idan Allah ya kawo lokacin ba mai hanawa dan haka ki kwantar da hankalinki muyi ta addu'a Allah ubangiji ya bamu mazaje na nagari ƙawwama tace amin amma dai ni kawai so nake ace nayi auran nan kowa ya huta, sawwama tace a'a ki dai yi aure dan ki huta ba dan kowa ya huta ba, ƙawwama tace hmn big sis bazaki gane ba na matsu nayi aure Allah dai ya kawo wanda za'ayi da shi.

Bayan kamar wata ɗaya sai ƙawwama ta samu miji mai suna jalil wanda ake kira da matashi da kuɗi abokin tafiyar manya. Cikin mako uku akai maganar aure kuma aka ɗaura aka kai amarya gidanta.

Sawwama bata so auren ya kasance cikin gaggawa haka ba saboda ba a yi bincike ba bare a san halaye da ɗabi'un shi amma ba yanda ta iya kasancewar ƙawwama tana san shi kuma iyaye da dangi duk sunyi na'am da al'amarin musamman ma dayake abun naima ne ya samu. Anyi biki na gani na faɗa mako guda ana shagalin bikin kamar baza'a gama ba sai dai duk events ɗin da akai sawwama bataje ba tace kar mala'iku su sa sunanta a cikin list ɗin masu zuwa party, abunda tayi ya ƙara jawo mata baƙin jini a gurin mutane harma ake ta faɗan cewa hassada ce take yiwa ƙanwarta.

A kwana a tashi ba wuya ƙawwama tayi watanni biyar a ɗakin mijinta, jalil ya kasance mutum ne mai hidima da yin alkairi ga iyayen matarsa hasalima kowa na musu murnar samun siriki kamarsa sannan kirkinsa da fara'arsa yasa kowa a dangi na ganin girmansa to amma shin hakan ya ke a gidansa kuwa?

Da sanyin safiya sawwama ta jiyo kishiyar mamanta na habaici tana cewa "taƙi aure ta zaɓi zaman gida sa'anninta na can gidan miji ana kiransu mama da inna"Ko damuwa bata yi ba dan ta saba jin irin wannan kalaman.

lokaci bayan lokaci sawwama takan kai ziyara gurin ƙanwata ƙawwama dan sada zumunci, wata rana ta je sai ta sameta tana kuka tana waƙe mai nuna tsananin damuwa da baƙin ciki "subahanallahi my dear mai ya faru, rasuwa akai ne? Sawwama ta faɗa cikin damuwa" ƙawwama tanajin muryar yayatta ta miƙe da sauri ta rungumeta tana kuka tana faɗin na shiga uku yaya na yiwa kaina mugun zaɓe kaicona na ƙi jin maganarki na gujewa bincike kafin aure yanzu gashi ina cikin matsala.

Sawwama ta riƙe ƙanwarta suka zauna bakin gado tace faɗamun mai ya faru kike faɗan munanan kalamai haka? da ƙyar ta numfasa sannan tace tinda mukai aure da jalil bamu taɓa kwana tare ba yau tsawon wata takwas kenan amma kowa rayuwarsa ya ke yi ko hira bama zama muyi wata rana sai muyi kwana biyu bamu haɗu ba saboda ina bacci zai fita kuma ina bacci zai dawo sannan duk abunda nace ina da buƙata sai yace na faɗawa amir zaman kaɗaici na neman ya kasheni a gidannan. Sannan kuma kwanaki na faɗawa mama amma tace karma na bari aji maganar kar mutuncinsa ya zube tinda ban rasa komaiba kawai nayi haƙuri haka nayi shiru amma yanzu wata sabuwar matsala ce ke neman faruwa da ni wacce tafi wanda nake ciki na rasa ya zanyi ji nake kamar ina rayuwa a wata duniyar da babau kowa sai ni!...

Sawwama tace na fahimceki ƙawwama haƙiƙa kina cikin jarrabawan da ban taɓa zato ba to amma mene sabon abunda ke fatuwa da ke? Ƙawwama tace "na kamu da soyayyar Amir."

A tsorace sawwama tace "meye!
A garin yaya ki ka yi wannan gangnancin kamuwa da soyayyar ƙanin mijinki?"

"Nimafa mutum ce yaya kuma zuciyar dake jikina irin ta mutane ce. Me ki ke tsammanin zai faru da ni alhalilin ina cikin wannan halin? Amir shi yake tayani hira, shi yake kai ni duk in da zanje, shi yake koya mun karatun computer a gida bansan ya akai ba naji na kamu da sansa...
Sawwama tace inna lillahi wa inna ilaihi raji'un tabbas kinyi kuskure ƙanwata amir ba muharraminki bane sannan kuma bai halatta ki samu kusanci da shi har haka ba musamman ma da yake kina cikin irin wannan matsalan to amma abunda ya kamata shine zanje na faɗawa kawu abunda ke faruwa tsakaninki da mijinki dan a kirashi yazo ya faɗi dalilin shi na gujema hakkinki."

TA ƘI AURE.! Where stories live. Discover now