PART 3

52 4 0
                                    

Ta ƙi aure part three

Ƙawwama tayi ta ƙoƙarin faɗawa wakilin jalil abunda ke faruwa amma sai ta kasa saboda nauyin maganar, haka ta yi ta haƙuri tana ta addu'a kamar yadda sawwama ta shawarce ta.
Kamar wasa shekarar ƙawwama biyu a gidan aure amma sai dai taji ana labarin yanda aure yake, bata san me ake kira soyayya ba tsakanin miji da mata, babu shaƙuwa, babu biyan buƙata, babu komai da ya shafi rayuwar aure sai fama da zuciyarta da ta keyi wajen bijiro mata da hanyoyin saɓon Allah amma haka ta daure ta kau da kai kuma ta nisanci amir dan gudun ruɗin shaiɗan.

Ƙawwama ta kan kai ziyara duk sati ta gaida hajiya mahaifiyar jalil musamman ranar juma'a, yau ma dai ta shirya dan zuwa gidan, ta yiwa hajiya girki na musamman da kunun gyada mai daɗin gaske tana shiga ta jiyo hayaniyar siddiqa da hidaya a ranta tace sun dawo kenan ", salamu alaikum ", hajiya ta amsa wa"alaikum slama barka da zuwa ƙawwama!

Da gudu suka fito oyoyo anty ƙawwama yanzu muke shirin yi miki surprise visit", Allah sarki yaushe kuka dawo ban sani ba? Jiya da yamma muka dawo kuma munce wa yaya karya faɗa miki...

Hajiya ta ce to ai kwa bari ta zauna dai ko, bayan ta zauna suka gaisa da hajiya da sauran mutan gidan. Yini tayi a gidan har bayan sallar magriba amma ji take kamar karta koma gidanta saboda gidan babu daɗi..

kamar siddiqa taga zuciyarta tace anty tare zamu tafi da ke muyi sati ɗaya ", ƙawwama tace wata ɗaya zakuyi dan sati yayi kaɗan. Hmm ƙawwama yaran nan zasu dameki da hayaniya kinsansu da surutu, " haba hajiya ba komai ai nima kinga na samu 'yan hira, hajiya tace to shikkenan kuje amma kar su wuce sati biyu, hajiya a taimaka a bamu wata ɗayan nayi kewarsu sosai", to shikkenan Allah ya bada zaman lafiya.,

har sun juya zasu tafi hajiya tace "amma a kula kar naji abunda bai kamata ba ke hidaya ki kula da siddiqa kinsanta da rawan kai", to mama, sai mun dawo.
Bayan fitansu ƙanwar hajiya dake gefe tace na rasa meye abun so ajikin ƙawwama matar da ta doshi shekara uku amma ko ɓatan wata bata yi ba, dama da ganinta ba san haihuwa zatayi ba, irin sune matan nan da basa san ciki dan kar halittan jikinsu ya canza" Karima na sha faɗamiki bana san jin wannan maganar, daga yau kada ki sake"inji hajiya, ' ai dama nasan haka zakice sam bakya ganin laifinta ai shikkenan.

Zamansu hidaya alkhairi ne ga ƙawwama dan ta samu masu ɗebe mata kewa kuma ta samu lafiya dan sati ɗaya da zuwansu hawan jininta ya fara sauka. Ƙawwama na zaune a ɗaki bayan ta idar da sallan walaha sai hidaya ta yi sallama ta shigo ta zauna gefenta tace anty yau satinmu biyu amma banga yaya jalil ba ko dai tafiya yayi? Ƙawwama tace ba tafiya yayi ba kawai dai ya san kuna nan ne zaku tayani hira shiyasa bai damu da yazo ba", hidaya tayi mamakin jin haka amma sai ta taƙaita tambaya tace to shikkenan barin je na ɗaura mana girki dan yau duty nane, to ba komai na gode fa hidaya naji daɗin zuwanku.

... Bayan wata guda hajiya da kanta ta zo dan ɗaukansu siddiqa dan gani take sun takurawa ƙawwama, bayan komawarsu gida sai hidaya ta samu hajiya tayi mata bayanin yadda zamansu ƙawwama da yaya jalil ya ke, tabbas hajiya tayi mamakin jin haka sai ta ɗau waya ta kira shi kuma ta kira ƙawwama suka haɗu a parlour ta, hajiya ta nemi suyi mata bayanin abunda ke faruwa tsakaninsu amma sai jalil ya nuna babu komai suna zaune lafiya, ganin yadda yake magana babu tsoron Allah ba kunya abun ya bata mamaki, ganin haka yasa ta kwashe labari kaf ta faɗawa hajiya, " banda salati hajiya ta kasa cewa komai cikin gaggawa ta kira general meeting tsakanin family ɗin guda biyu, cikin sa'a ɗaya da rabi kowa ya haɗu guri guda nan take hajiya ta bayyanawa kowa halinda ake ciki kuma sawwama ta jaddada gaskiyar abunda ƙawwama ta faɗa",

haba ƙawwama yanzu ashe ba zaman daɗi ki ke yi a gidan ɗana ba amma baki taɓa faɗamun ba nima fa kamar uwa nake a gurinki ina ƙaunar ki kamar yadda nake san yarana, haba malam yanzu harda kai za'a haɗa baki a yi shiru akan maganar nan," malam yace nima bansan abunda ke faruwa ba sai yanzu amma duk yanda akai ta hana yaran ne su faɗamun dan haka sai ki faɗi dalilinki na yin shiru duk da kinsan abunda ke faruwa,"

maman su ƙawwama ta ce ni fa gani nayi bai kamata ace yarinya ta jima ba aure kuma daga auren ace har an fara ƙorafi ba sannan idan maganar ya shiga dangi zamu ji kunya," hajiya tace "hm" kinyi tinanin kuwa amma banda 'yarki baki kyauta ba sam mama ko kinsan wannan matsalar da ƙawwama ta shiga yana jefa matan aure cikin damuwa wanda sanadin haka wasu ke afkawa zuwa ga zina, maɗigo, da masturbation (yin amfani da yatsa ko wani abun wajen biyan buƙata) musamman irin matan da mazajensu keyin tafiya tsawon lokaci amma ki ka bar 'yarki saboda gudun abun kunya kin manta yaran nan amana ne a hannunmu dole ne muna bibiyar al'amuransu na rayuwa ko da ace sunyi aure," kuskure kam nayi dan Allah kuyi haƙuri malam ka yafe mun kema ƙawwama kiyi haƙuri na zalunceki 'yata,! ƙawwama tana kuka tace ba komai mama na fahimceki,"

hajiya tace saura kai babban ja'irin ka wani sunkuyar da kai kamar mai ciwon wuya zaka mun bayani dalilin da yasa ka wulaƙanta amanar da aka baka ko sai kaga ɓacin rai na,!?

TA ƘI AURE.! Where stories live. Discover now