💀☠️💀
*KOFAR AJALI*
*_Final Chapter_*
_Littafi na Uku_
💀☠️💀
_________________________*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
*FB PAGE*
https://www.facebook.com/profile.php?id=100070173921421
_________________________*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
*M. W. A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
_________________________
*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*
*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0️⃣1️⃣**RECAP ON PREVIOUS SEASON*
"babban kalubale da zaku fuskanta game da wannan aiki shine Harun,domin yana dauke da bakar kambu (Crown.) na Sihiri wanda wannan kambun mallakan sarki Bahru ne,da wannan kambu kadai zai iyya lalata duk shirin ku kuma da wannan kambu zai iyya fitar da muggan Halittu izuwa goron kasa sannan da wannan kambu zai iyya dawo da Rayuwar Bahru wacce yin hakan babban kalubale ne a gare mu dama sauran al'umma baki daya,dan haka ya zama lallai ku rigasa samo wayennan abubuwa dana lissafo muku su."
Bangaren su Harzad kuwa a guje suka fice daga cikin wannan Yana,fitarsu kuwa suka ruga ta sanadiyyar sunga ginin na kokari nutsewa dasu.... a sa'in da suke wannan gudu kuwa manyan duwatsu sukayi ta fadowa daga saman wannan guri....
Sun sha da kyar kafin suka tsira daga wannan mummunar al'amari cen suka tsinci kansu a wata kofa wanda acikin wannan kofa ko'ina kasa idanu kwai zaka gani birjik a zube,ko ina ka sa idanu su zaka tarar.....idan kakai idanun a saman wannan daki kuwa mutane ne da dama aka rataye su a gurin yayin da aka nannade su cikin yana kamar yadda aka yiwa Amrita....*NEW EPISODE*
*_22st_Aug_2024_*A iyya yadda aka fahimci rayuwa, komai tayi farko lallai karshenta na nan zuwa,domin kuwa rayuwan ta ginu ne akan bangarori guda biyu, nasara ko kuma akasin haka.
dukda cewa ba kowace mafarin bace take da tata karshe, amma kuma ba'a cire rai da samun karshen duk wani halin rashin dadi daya samu mutum a rayuwa ,akanyi lokaci da wasu bangarori na al'umma ke farin ciki yayinda wasu ke kokawa akan kuma samu lokacin da kowa na cikin halin kaka ni kayi kamar yadda ta samu duk bangarori biyu na wannan tafiya wato bangaren su Amrita da kuma tasu Atif,kowace bangare da abinda take fuskanta a halin da suke ciki, idan muka dauki bangaren su Amrita zamuga suna cikin rudanin dasu kansu basu san suna ciki ba domin kasacewar Harun a tawagar tasu yayinda yake 'badd'a kama, ba karaman matsifa bane a gare su,bangaren su Atif kuma dukda cewa suna gab da haduwa da abokan tafiyansu da suka raba hanya a baya ta dalilin hadarin da suka fada, amma kuma basu cike da farin ciki domin basu san wani irin hadari bane ke tattare da aikin da akace ya rataya a wuyan su........
Tohfa kada na cika ku da surutu bari mu lulluka cikin labarin mu daura daga inda aka tsaya.
Tsawa hade ake da walkiya akeyi sa'annan kuma idan akayi walkiya ta sauka duk abinda ta samu narkarwa take.... Ganin haka yasa duk suka gigice hatta Ali domin shima kansa baisan musabbabin faruwan hakan ba.
Fitulun Gurin d'add'aukewa sukayi daya bayan daya ,gurin sai tayi matuƙar hudu, cirkwa cirkwa sukayi suna ta waige waige hade da mamaki faruwan hakan "taya hadari mai cike da walkiya zata faru a irin wannan lokaci kuma a irin wannan guri?."
Tambayoyin dake cike cikin kwakwalansu kenan wacce babu amsa da suke dashi daga su har Ali,har sai da sukayi ido hudu da masu alhakin faruwan hakan wato wasu kyawawan ƴan mata guda biyu da suke tafe cikin kasaita yayin da kuma suka tunkari gurin da suke tsaye, suna sanye da fararen kaya wacce zaka kasa babban cewa shin kayan da auduga akayita ko kuma da tsantsar furanni akayi dan kuwa kayan tana matukar daukar ido gashi kuma ta zube har kasa, daga cen nesa suke tahowa yayin da duk inda suka ratsa sai hasken fitulun su kawo, haɗa fuska Ali yayi bayan yayi arba da mutane biyu dake biye da wa 'yan nan kyawawan ƴan mata,wato Atif da Mu'azz, ganin hakan ya saka shi mikar da hannayen sa gaba hadi da bawa taron zuman nan umurnin kai musu farmaki, amma kuma baiyi nasara ba domin kuwa ganin hakan da yayi yasa daya daga cikin ƴan matan nan ta ɗaga tafin hannun ta daya nan da nan sai wani farin haske mai dauke da kara mai razanarwa ya baiyana yayinda saukar wannan haske ya dire a tsakiyan taron zuman nan,aiko tuni suka fara konewa hatta wayenda ke nesa da gurin suma suka kone kurmus, Ali shima ba'a barshi haka nan ba domin kuwa dayar yarinyan itama ta gwada nata karfin tsafin wajen dukar kasa da sawunta ta tashi sama, faruwan hakan keda wuya gurin ya gauraya da tsawa hadi da walkiya,Dukda wannan abubuwa dake faruwa Atif dai da Mu'azz basu tsaya da takun da suke ba,haka suka cigaba da takun suna tunkaran inda Samra, Forzy da sauran abokan tafiya nasu ke tsaye....