Halin Mijina

24 2 0
                                    

*Halin mijina... (Short story)
****Na
*Fatima saje (ummuadam).

Bismillah, Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala Rasulullah.

Barkanku da wannan lokacin 'yan uwa masu albarka, fatan duk kuna cikin koshin lafiya da aminci.

Kabarin Halin Mijina shine tsaraban da nake tafe dashi a wannan rana. Ban yadda ayi amfani da rubutuna ba tare da izinina ba.

**

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

**........() () ()........**

.....Tun ƙarfe goma na safe (10:00am) Mujaheed ya shirya tsaf, ya sha ado cikin shiga ta kamala; ga ƙamshin turare dake faranta rai da samun nutsuwar zuci.

"My dear, har ka shirya haka da sauri; na yi tsammanin zamu fita tare?"

"Ni kaina na so hakan, amma baƙi nayi; yanzu haka suna jirana."

"To shikkenan ba komai; Amma zanyi kewarka sosai kuma anty humaira bazata ji daɗin rashin zuwanka gurin ɗaurin auren ba! "Ya Habibtie, mai zai hana ki wanke ni a gunta kamar yanda kika saba.

"Hmm wato kama san laifinka kenan?"

"Na sani,kuma ina naiman afuwa a gurinki da kuma gun babbar yayarmu. "To anmaka afuwa amma a kiyaye gaba. "To ranki ya daɗe!!

...Habiba na kallo mijinta ya shiga mota yayi tafiyarsa kamar yadda ya saba kullum baida lokacinta a gida, sannan bai damu da halinda take ciki ba na rashinsa kusa da ita ba. Cikin damuwa ta zauna gefen gado saiga hawaye na kwaranya daga idanunta. Hannu ta sa ta share hawayen sannan ta shirya ta kama hanyar zuwa gidan Anty Humaira wacce ake bikin 'yarta ta fari.

An haɗu dangi da abokan arziki anata shagalin biki ana nuna farin ciki. Ƙawayen amarya sun haɗa kai sunata jayayya akan hoton wani saurayin ɗaya daga cikin ƙawayen; Habiba na zaune a gefe sai taji ɗayarsu na cewa...

"In dai majaheed ne to ai saura kika samu, dan najima ina tare da shi; kuma gayen ya haɗu gashida iya wanka ga kuɗi sai dai sam baya san maganar aure, yafi san rayuwar holewa da jin daɗi; kuma abun takaicinma matarsa duk ta fimu kyau amma dan jaraba kullum yana tare da 'yammata a hotel.

Zuciyar Habiba kamar zata fita daga ƙirjinta saboda bugawa; har zatai musu magana dan taga hoton amma saita dakatar da kanta tace bai kamata ta zargi mijinta ba. Sai dai har yammaci wannan maganar tana yawo a zuciyar Habiba.

Siddiq ne ya ɗauko ta a motar mahaifinsa dan ya maida ta gidanta; sai tace zata sai ice cream.
Bayan sun tsaya ta saya kwatsam taga mijinta Mujaheed a mota tare da ɗaya daga cikin ƙawayen amaryar da tajisu suna maganarsa.!

Jiri ya ɗebeta tayi kamar zata faɗi amma Siddiq ɗan anty Humaira ya tare ta. "Anty lafiya kuwa?", "lafiya lau, mutafi gida kawai" har sun shiga mota zasu tafi Siddiq ya gano abunda Habiba ta gani!, "kai!, wancan ba Uncle Mujaheed bane a mota yana sunbatar wata!? "

Cikin ƙarfin hali tace "Kai Siddiq ashe ba kada hankali!, mijinnawa ne zaka gani yana aikata wannan mummunar aikin kuma a nan!? Wannan ba halinsa bane; kawai dai mai irin motarsa ka gani.!"

Halin MijinaWhere stories live. Discover now