Wasu Mabiya... (Complete)

8 2 0
                                    

*WASU MABIYA....(short story)
*NA
*FATIMA SAJE (ummuadam)


Wunin laraba daren alhamis, Malam ya gabatar da karatu kamar yanda ya saba tsakanin magriba da isha'i; cikin walwala da shauƙin ina ma ace Malam zai ci gaba da karatun kar a tsaya saboda iya bin salonsa wajen koyarda ɗalibai

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

...Wunin laraba daren alhamis, Malam ya gabatar da karatu kamar yanda ya saba tsakanin magriba da isha'i; cikin walwala da shauƙin ina ma ace Malam zai ci gaba da karatun kar a tsaya saboda iya bin salonsa wajen koyarda ɗalibai.

"Ko kai kaɗai muka mallaka a matsayin malami tabbas ka ishemu a wannan gari harma da ƙetaransa"

Wannan kalaman Luqman kenan, ɗaya daga cikin ɗalibai masu hazaƙa sai dai matsalarsa shine yana tsananta yabo ga Malam; wannan dalilin yasa shi kansa Malam da sauran ɗalibai kamarsu Abdurrahman da Abdussamad suke masa nasiha tare da jan kunnensa akan tsananta yabo ga Malami musamman a gaban idonsa ba zai amfnar da shi ba, hasalima zai iya zamowa silar zamiya ga Malamin amma sam Luqman baya wa'azantuwa domin shi a ganinsa yabon gwani ya zama dole.

Malam mutum ne wanda ya kwankwaɗa daga tekun ilimi daga gurin mahaifinsa da kuma Malamansa, Malam mutum ne mai fara'a da kyawawan ɗabi'u kamala da magarta sukan bayyana ƙarara ga duk wanda yayi arba da shi; bugu da ƙari mutum ne mai tawali'u baya nuna shi wani ne na musamman ko yayi cika baki akan haibarsa.

Duk da nagartar Malam da gujewa jin yabo daga bakin mabiya, a karo na farko malam yayi murmushi da jin yabon Luqman a wajen karatu.

Tabbas hankalin ɗalibai ya tashi, duk sanda aka yabi Malam sai ya zubda hawaye yana cewa ku daina cutar da zuciyata ban kai nan ba; amma yau sai sukaga akasin haka!

An shirya wani babban taro a fadar sarki garin, baƙi sun halarta daga sashe daban-daban na duniya; an gayyaci Malam tare da sauran Malamai dan wa'azantar da mutane akan abunda ya shafi aƙida da ikhlasi.

Malam yayi jinkirin halartan taron saboda wani uzuri na gaggawa, hakan yasa malam bai samu kujerar zama a high table ba; a haka ya haƙura ya zauna cikin sauran yaaku bayi.

Bayan sauran Malamai sun gabatar da wa'azi da nasiha ga 'yan uwa musulmai basu ankaraba har lokaci ya ƙuri saura minti biyu a tashi daga taron. Ran Malam ya ɓaci matuƙa har hakan ya nuna a fuskarsa saboda wa'annan dalilai guda biyu.

Har suka dawo gida Malam bai saki fuskaba, bayan sun shigo parlour sai sukai sallama da sauran ɗalibai; amma Luqman ya dawo daga baya ya samu malam yace "gaskiya yau an ƙasƙantar da matsayinka malam, bayan an kaika cikin wa'anda basu kai ka ilimi ba kuma aka manta da kai har sai da lokaci ya ƙure sannan aka baka abun magana kuma ake so kayi jawabi cikin minti biyu duk yawan iliminka ai ko minti goma ne sunyi maka kaɗan"

"Tashi kaje wajen 'yan uwanka a majalisi, ina so na huta kafin la'asar" Malam ya faɗa.

Babu shakka kalaman Luqman sunyi tasiri a karo na biyu kenan a zuciyar Malam; tindaga wannan lokaci Luqman ya fara samun kula ta musamman a gurin Malam wanda hakan ya bawa Luqman damar ci gaba da yin sara akan duk wata gaɓa daya samu dan cinma manufarsa.

Wasu MabiyaWhere stories live. Discover now