Wacece Ni?

81 5 3
                                    

🔆..... WACECE NI?🔅
🔅NA🔅
🔆..... FATIMA SAJE🔅


Ina yiwa ɗaukacin al'umar dake bibiyar rubutuna barka da sallah, Taqabbalallahu minna wa minkum eid mubaraq alaina wa alaikum.

Bismillah, Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala Rasulullah. (Sallallahu alaihi wa sallam)

Tsokaci.

*Wacece Ni* labarine dake da alaƙa da mu mata kai tsaye, labarin rayuwar farfesa Salwa akwai darussa masu muhimmanci gameda rayuwar mata yayinda suke tsaka da neman ilimi ma'ana karatun boko da kuma bayan kammala karatun har izuwa lokacin samun aiki da kuma bayan hakan.

Tsakure

Cikin ado da ƙasaita ta sanya kekkewar doguwar rigarta na shadda mai ɗauke da kayataccen ado na musamman da akai da dutsuna masu ƙelli da ɗaukar hankali. Ta ɗauki daƙiƙa biyar tana ƙarewa kanta kallo gaban madubi domin tabbatar da komai yayi yanda ya kamata, "Hajiya, an gama shirya mota domin tafiyarki" haladu driver ya faɗa bayan ya kirata a waya.

🌸🌻

.....Makaranta.

"Bantaɓa jin farin ciki irin ta yau ba suwaiba, wai nice nake kammala karatun jami'a a wannan kasar tamu ta Naija.!"

"Hm! Ke dai bari, ai ni ko maganar ma ban san ta ina zan fara ba; tun fa ina lissafin shekaruna a wannan makarantar har na daina saboda yawan yajin aiki da ake; Wallahi ji nake kamar na zuba ruwa a ƙasa na sha dan murna."

"To ai gara ke, kin yi aure harda baby, ni fa da ko manemin auren babu! Sai tarin 'yan i love you amma ba zancen zan turo manya."

"Haha! Kin ban dariya Laurat, to ai laifin ki ne; kin dage sai kin gama jami'a zaki yi aure saboda gudun responsibilities na gidan miji."

"Ai ƙawata nayi nadama shariritar da nayi, amma dai Alhamdulillah tunda na gama lafiya sai kuma na duƙufa da addu'a Allah ya kawo miji na gari; amma gaskiya nayi gangancin ƙin auren Kabir gashi yayi aure harda yaransa uku."

"To, abun ba wuya wai 'budurwa taga ƙawarta da goyo' tace ashe abun ba wuya."

"Abun harda tsokana ne? Wato da ni kike yi ko? Ba komai with time zan rama watarana."

"Ai Laurat sai dai ki rame, kinga mu shiga hall din dan naga duk an shiga kuma ga can mutumiyar taki ta shigo da mota."

"Wow! Farfesa Salwa, ina san matar nan! She is my role model."

....... Tattaunawar Suwaiba kenan da ƙawarta Laurat dukkaninsu sun ka kimanin shekaru talatin da haihuwa (30yrs) yau rana ce ta farin ciki garesu domin murnar kammala karatun jami'a da suke yi amma hakan bai sa sun mance da zancen aure ba musamman Laurat data sa aranta aure da makaranta sam bazata haɗasu a rayuwarta lokaci guda ba.

..... Bayan sun shiga ɗakin taro da aka kayatar da ado dimin taron.

Ɗalibai sun cika maƙil, fuskokinsu ɗaukeda murmushi da annashuwa mai bayyana tsananin farin cikin da suke ciki a wannan rana ta musamman.

Duk da farfesa Salwa ta iso daf da ɗakin taron amma ta zauna cikin motarta kimanin daƙiƙa talatin bata fito ba. Ɗalibai da sauran manyan mutane dake dakonta sun ƙawu dan ganin ta shigo.

Wacece Ni? Where stories live. Discover now