🍂🍂 *FARAR MACE...*🍂🍂
*Sabon Taku**Oum Sumayya*
BabybintuuWANNAN LITTAFIN NA KUD'I NE AKAN FARASHI ME SAUK'I 500 VIA 4210014214 LAWAL SHAMSIYYA ECO BANK SHAIDAR BIYA TA 07017296839 MASU TURA KATI MTN/AIRTEL TA 08139624956 Y'AN NIJAR ZASU TURA KATIN AIRTEL NA 500F TA 07017296839 DAN ALLAH BANDA KIRA ONLY WHATSAPP
*PAGE SAVEN AND EIGHT*
Da sauri ta b'oye abayan labule jin k'arar k'ofa alamun wani yashigo zuciyar ta ne tasake bugawa kamar zata faso k'irjinta tafito "to waye kuma?" Tafad'a ahankali tana d'an lek'owa ta tsakanin labule sake waro many'an idanun ta tayi aranta tace "Hajiya Hindu? Metazo yi nan ko daii taga shigowa tane ko duk abu d'aya muke farauta? Lallai da wal...." Maganar ta yakatse ne ganin Hajiyar na yayyafa wani abu ak'ofar bedroom d'in tana y'an waige waige da alamu bata yarda da wajen ba wani irin daskarewa tayi atsaye tana kallon ta matar da duk gidan babu wanda yakaita nuna ma Omar so haka yanda suke da mahaifiyar shi babu mejin kansu kenan fuska biyu gareta lallai kam mutum mugun icce ne.
Wani k'ayataccen murmushi Hajiya Hindu tasaki kafun tace afili "lokacin tarwatse war ki daga ke har y'ay'anki yayi hahahhhaha" tafashe dawata muguwar dariya tana tafiya tana cigaba da dariyan cikin k'asaita tabar side d'in.
Cikin wani irin mamaki take kallon ta harta b'ace ma ganin ta cikin azama tafito daga inda tab'uya takunna fitilar wayarta tana haska inda Hajiya Hindu tazuba abu bisa mamakin ta sai bataga komai ba shiru tayi tana tunanin itafa abu me ruwa taga tana yyyafawa ya haka? Tsaki tayi kamun tabud'e d'akin aranta tana ayyana "kowa tashi tafishe shi burinta daban burinaa daban" wani garin magani tad'auko a braziyan ta dawasu layoyi guda biyu katifar gadon tad'aga barbad'a maganin tayi cikin axama kamun tajefa laya d'aya ak'asan gadon d'ayan kuma tashiga toilet ta sak'ata ak'asan Jacuzzi tafito dasauri saida tad'an lek'a ta tabbatar babu kowa sannan tafuta asad'ad'e kamun tasa key takulle k'ofar tajuya tabar da wajen da mugun sauri tana y'an waige waige.
Lokacin data iso kano dare yayi sosai dan d'aya ta gota hakan yasa dak'yar tasamu adaidaita sahu zuwa modibbo estate dake cikin jan bulo saida takira Aunty awaya tashaida mata tana bakin get bajimawa ta iso har lokacin jikin ta sanye da kayan dasukaje dinner kallon Halisa tayi sama da k'asa kamun tajuya batare da kowannen su yayi magana ba haka tabita abaya zuciyar ta na bugawa dan tasan Aunty bata d'aukan excuse ko kad'an koda suka isa side d'in agajiye tayi relaxing akujera idanun ta na raurau ganin Aunty tana kad'a k'afa ahankali tafara bama Aunty labarin gwagwarmayan dasuka sha da Omar har koran ta da yayi yau d'in,
Shiru tayi tana still tana kad'a k'afan ta kamar baza tace komai ba saikuma tasaki murmushi tana kallon Halisa da take share hawaye cije gefen lips d'in ta tayi kamun tace "banyi tunanin samun nak'asu daga gareki ba ko da wasa shiyasa na sakan kance nake ta d'aura ki bisa ayyukana ashe ban sani ba nayi babban kuskure but ba komai shiga ki kwanta dasafe kya koma yola inyaso Yahanasu saita xo inaga ita zata fiki d'aukan abubu....."
Cikin kuka tazame agaban ta tana fad'in "Dan Allah Aunty kimin rai wallahi duk yanda kikace nayi haka nayi abu d'aya nake tunani Omar mata maza ne shiyasa yakasa aikata komai agareni kuma namiki alk'awari daga yanzu baza ak'ara samun matsala ba kiyi hak'uri dan Allah kitai maka min karkice na koma yola"
Shiru tayi as usual tana maimaita "mata maza?" Saikuma tace "ban gane mata maza ba gaya min yakukai dashi shin kin tabbatar yasha desire tablet d'in?"
Kai ta gyad'a mata cike da tabbatar wa kamun tace "agabana yasha wallahi amma muna fara romance abun nashi takwanta kamar tsumma"
Shiru tasake yi cikin nazari tabbas maganar boka ta tabbata ankashee mai maazak'uta to kenan waye dasauri tamik'e tana fad'in "Hajiya Hindu kenan to meyasa tabbas dole gobe mukoma ga boka tashi kije nagane komai yanxu"
Cikin sauri tamik'e tanufa d'akin ta tana sakin ajiyar zuciya tana shiga takunna switch haske yagauraye d'akin komai agyare kamar tana nan da alamu kullum sai angyara zama tayi abakin bed tana sauke ajiyar zuciya gamida sakin murmushi batayi tunanin Aunty zata biyu cikin sauk'i ba ahankali tayi baya tana lumshe idanun ta dan agajiye take saboda maganin datasha bak'aramin kasala yasakin mata ba.
Da idanu taraka ta tana nazarin ta kamun taxauna tana kallon agogo biyu saura ajiyar zuciya tasaki gamida furzar da wata zazzafar iska mik'ewa tayi dasauri tafad'a bedroom d'in ta wanka tayi gudu gudu tashirya cikin wasu y'an iskan sleeping dress tashafa shu'umar humrar ta tad'aura kimono akan kayan barcin tafuto tabi ta wani corridor tafiyar mintuna uku ta isa wani side d'in key tasa tabud'e tashiga tana kunna hasken wayarta dan golf d'in d'akin akashe yake sai k'aran ac dake tashi ahankali tanufa wata hanya nan ma falo ne daga gefe kuma k'ofofi biyu da alamun nan ne bedroom d'in a falon tacire kimonon kamun tajefa wani abu abakin ta tanufa bedroom d'in cikin wani irin taku nan ma ba haske hakan yasa tasake kunna hasken wayarta makeken royal bed ne dayai bara zanar cinye bedroom d'in gaba d'aya sai wardrobe da mirror dake gefe sai wajen da prayer mat ke shimfid'e sai ragowar filin idanun ta tawatsa saman gadon kallo d'aya tamai tagane ba barci yake ba domin tasan Alhaji baya kwanciyar rigingine k'arisa wa tayi tahaye gadon tana fad'in "Alhaji naa!"
Batare daya kalleta ba yajuya bayan shi da sauri dan bai son wata hayaniya ahalin dayake ciki,
Harara ta maka ma bayan kamun tasa hannun ta akafad'an shi tana d'an matsawa tace "uhm meyayi zafi shiba wuta ba ka kwant..."
Azafafe yace "get out!"
Zaro idanun ta tayi zata k'ara magana yasake katseta "i said get out"
Da mamaki take kallon shi kafun tasauka agadon jiki asanyaye tabar side d'in.
Ahankali tamik'e tana ninke sallayan dake hannun ta kamun tamata masauki agefen mirror kallon kanta ta tsaya yi kamin takai hannun ta zuwa saman kumburarriyar fuskarta tashafa wasu siraran hawaye ne suka zubo mata batare data share ba tace "Ya arhmar rahimin kakawo min d'auki nasan kana sane da duk halin danake cikin ya Allah kabani k'arfin gwiwar cinye wannan jarabawar" tak'arisa maganar wani sabon kukan na kubce mata tazube akan kujerar mirror cike da tausayin rayuwar datake ta fad'awa daga wannan sai wannan "shin menene laifinta dan takasance bak'ar fata ita tayi kanta? Allah daya yita shine yayi fararen meyasa Ya Omar baizai fuskanci kalar tata kaddarar ba meyasa bazai karb'eta ba kodon tausayin halin maraici kunci da tashin hankalin data fuskanta tunkan tasan kanta ba meyasa yakasance me bak'ar zuciyar da baya fahimtar kowa sai kanshi ya Allah" tafurta da mugun k'arfi zuciyar ta nawani irin suya tana sakin shashsheka kamar numfashin ta zai d'auke amsa kuwwar maganar shi kawai takeji akunnenta "Bazan tab'a iya zama dake amatsayin house maid bama balle amatsayin matar aure domin hakan abun kunya ne agareni ki kalle ni da kyau kigani na wuce da class d'in ki illiterate kuma bak'ar mace mummuna kamar ki to ince ma friends d'ina me? Tirr da wannaan had'in na tsohuwa wallahi ko ahaka aka barni ancuce ni anb'ata min record dan haka kisan duk yanda zakiyi kiguje ma aurena domin inada wacce nake so *FARAR MACE* kyakkyawa ga ilimi ga uwa uba wayewa idan kuwa kikai kuskuren aure na narantse miki saikin gunmace uk'ubar dakika tsinci kanki abaya saina zamo miki tauraro me wutsiya and salin alin ma ki bujire ma auren nan idan ba haka ba uhmmm" yayi wata k'wafa yabar d'akin idanun ta talumshe tuna maganganun shi wasu zafafan hawayen nasake zubo mata watak'il haka zata k'are tata rayuwar cikin k'unci,
Yanda taga rana haka daren yak'are a idanun ta barci duk iya satan shi haka yabarta kiran sallar farko tasake d'auro alwala taci gaba da kaima Allah kukan ta saida ta sallaci asubahi sannan tasamu wani wahalallen barci yayi gaba da ita mai cike da munanan mafarkai akan Omar da wata wacce bata ga fuskarta ba suna biye da ita awani k'urgurmin dauji da duhuwar bishiyoyi yasa ko gaban ta bata iya gani gudu kawai take tana waigen su tana fad'in "ataimaka min zasu kashe ni taimako taimako" amma babu alamun wani zaima jita wani razanannen ihu tasaki jin anbuga mata wani abu akai tazube awajen tana bud'e idanun ta dishi dishi take ganin ta saboda jinin daya wanke mata fuska dariyar tane take amsa kuwwa acikin dajin kafun takalleta cikin wata iriyar murya tace "kin gama gudun Junaiha gashi kinzo hannu yau dole ki mutu kibarni da muradina abun so da begena Omar kin b'ata min komai tun shigowar ki rayuwar shi dan haka dole ki mutu yazama dole nakashe ki yau hahahaha"
Amugun firgice tafarka tana fad'in (La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin" tana y'an waiige waiige babu kowa ad'akin sai hasken rana daya faso ta windon ajiyar zuciya tasaki tana sharce gumin datayi duk kuwa da ac dake aiki shiru tayi na y'an mintuna tana son tuno fuskar data gani kamar tasan fuskar amma kuma ta b'ace mata duk yanda taso ta tuna fuskar ta gagara amma kuma mafarkin yak'i b'ace mata knocking d'in da akeyi ne yakatse mata tunani hakan yasa tamaida hankalin ta ga k'ofar kamun tamik'e da sauri taje tabud'e "Aunty Hannah" tafad'a calmly tana bata hanya tashigo sannan tamaida k'ofar takulle tak'arisa gefen bed tazauna tana gaishe ta ganin tama kanta masauki akujeran mirror,
So friendly ta amsa gaisuwar fuskar ta awashe tace "kinyi wanka kuwa?"
Kai ta kad'a alamun a'a,
Cikin fara'a tace "tom bara na had'a miki kiyi saimuje breakfast anfara hallara a babban dining"
Sok'ok'o tayi tana kallon Aunty Hannah jin abunda tafad'a ganin harta mik'e tanufa toilet yasa tatashi da sauri ta tare ta da fad'in "la Aunty ba saikin had'a min ba zan had'a da kaiina inna shirya zan zo kije kawai" tak'arisa maganar tana kama handle d'in bayin tashige abunta batare data jira cewar Aunty Hannah d'in ba,
Da murmushi taraka ta kamun tad'an saki ajiyar zuciya tabud'e wardrobe d'in tad'auko mata wani had'add'en cotton lace milk mara nauyi dagani basai anfad'a yaci kud'i turare tafesa mai kamun taciro mata pant da bra duka sababbi suma tafeshe su da turare ta aje agefen gadon tana sake zama y'an kalle kalle take ad'akin ganin komai tsaf,
Wanka tayi cike da mamakin sakin fuskan da yayyen Omar dajanta ajiki dasuke yi tun lokacin da aka furta had'a su aure musamman Aunty Hannah dake da mugun izza ji da kai ga kuma k'asaita kamar wata basarakiya amma ji wai itane da had'a mata ruwan wanka ajiyar zuciya tasaki gamida tab'e baki tad'aura tewol tana y'an sak'e sak'e gaba d'aya cikin sati biyu komai yacanza agidan kowa sai janta yake ajiki kamar basu bane suka tsane ta ada kamar ba ita bace suka tsangwame ta kamar ba ita bace boyi boyin suba amma yau har ita ake gayyata cin abinci wanda ada sai anci anrage ake bata"huuuum tabbas dawata ak'asa bazatai saurin amincewa dasu lokaci d'aya ba dole akwai wata kitumirmurar da ake shirya mata dole tayi taka tsantsan kuma dukkanin su zata shayar dasu ruwan mamaki" murmushin dayafi kuka ciwo tasaki tafito daga toilet d'in hannun ta rik'e dawani tewol d'in bazata taganta xaune hakan yasa tad'an tsaya cike da jin kunyar yanda tafuto,
Da sauri Aunty Hannah tamik'e tayo kanta tana fad'in "k'araso mana Junaiha yakika tsaya?" Tayi maganan tana murmushi gamida janta zuwa bakin mirror tazaunar da ita akan stool tana fad'in "bara namiki light make up muje suna jiran mu ko" tayi maganar tana d'an gogge mata ruwan fuskanta da tewol d'in hannun ta cikin sauri kamun tafara yimata light make up,
Gaba d'aya sai tayi still tana kallon Aunty Hannah dake ta k'ok'arin shafa mata powder cikin y'an mintuna ta kammala mata light make up sosai tayi kyau kayan tad'auko mata karb'a tayi takoma toilet tashirya gaba d'aya rawan jikin dasuke kan ta baya burgeta saima haushi da bak'in ciki datake sake ji acikin zuciyar ta futowa tayi bayin tasaka flat shoe d'in data mik'o mata milk tanajin tana yaba kyan datayi itadai yak'e kawai take ta zuba mata,
Ahankali Aunty Hannah ta fuskance ta murya asanyaye tace "Junaiha dan Allah alfarma nake nema agareki kuma nasan bazaki kasa yimin ba kodon darajar iyayen mu kitaimaka min"
"Anzo wajen" tafad'a hakan azuciyar ta amma afili sai tace "ayya Aunty Hannah fad'a indai baifi k'arfina ba zan miki" tayi maganar tana danne zuciyar ta,
Ajiyar zuciya tasaki kamun tace "dan Allah Junaiha so nake ko antambaye ki kan za'a raba auren nan kice a'a"
Bazata tawani kalle ta saikuma ta duk'ar da kanta hawayen datake rik'ewa suna zubowa,
Dafa ta tayi taci gaba da fad'in "yes hakan shine yadace dake domin a y'an k'ananun shekarun ki be kamata ace kin zama bazawara ba sannan koba komai Omar d'an uwan kine auren shi rufin asirin kine sannan natabbatar komai daren dad'ewa zaku daidaita kanku dan haka koda antambaye ki kice kin hak'ura xaki zauna dashi ALLAH yasa hkane mafi alkairi"
Wani irin abune yataso mata har bata san lokacin data furta "Ya Omar baya sona nima kuma bana son shi saboda k'iyayyar dayake min ne yasa yagudu taya kike tunanin wataran zamu daidaita?"
Rungume ta Aunty Hannah tayi cikin lalllashi tace "Zan miki bayani anjima kedai kiyi yanda nace miki yanzu"
To kawai tace amma azuciyar ta tace "dama ta zanyi wasa da ita lalai Aunty Hannah ai ana tambaya na zance araba d'in inyadda kwallon mangwaro nahuta da k'uda" tana wannan zancen zucin suka k'arisa d'akin cin abincin anshimfid'a k'atuwar leda ga ahalin gidan duk azaune yayin da ma'aikata sai faman kawo many'an warm suke suna jerawa gaba d'aya k'amshin turare mabambanta ne suka cika wajen masu fira nayi masu danna waya nayi tunda suka shigo idanun kowa yadawo kansu hakan yasa taduk'ar da kanta tana addu'a ahaka suka k'arisa sai jitayi Aunty Hannah tamata masauki kusa da Ammi tana fad'in.....
K'arfe takwas ya iso estate d'in nasu bayan yayi parking yajima acikin motar kamar bazai fitoba sai kallon motocin dake parke yake kamun yawani furzar da wata zazzafar iska daga bakin shi aranshi yana ayyana "gwara nashiga duk abunda zai faru yafaru" yana gama kissima hakan hakan yab'alle murfin motar yana sanye da k'ananan kaya wandon jens royal blue da riga ja kafar shi sanye da sau ciki idanun shi sanye da bak'in glass fuskan nann amurtuke kamar be tab'a dariya ba direct side d'in Ammi yanufa zuciyar shi tana wani irin bugawa kamar zata faso k'irjin shi haka yakeji dukkanin wani takun dayake bazata yaji....✍🏼Oum Sumayya
YOU ARE READING
FARAR MACE SABON TAKU
RomanceSaikun karanta tukunna zaku gane yanda abun yake da 500 zaku more karatuku cikin salama