chapter 1

72 4 5
                                    

*_A ZATO NA_*🧏🏻‍♀️



✍🏼✍🏼✍🏼 By *Zainab yerima* AKA *_ZEETY_*


_MARUBUCIYAR_
●ANEESATY
●HASKEN RAYUWA TA
●BAZAN BUTULCE BA
●ACIKIN RAYUWA
●MURADIN RAI


wattpad @Zeety-AZ



_Gargadi: ban yadda wani ko wata ta juyamin littafi ba. wannan labarin kirkirarren labari ne ba'ayi shi don wani ko wata ba._



_Wannan littafin sadaukarwa ne ga *Fatima kole* maman Iman the owner of kole's collection_



*for advert contact 08080691306*


*1*

Janbaki Fati take gogawa akan ɗan ƙaramin bakin ta, cikin hanzari tagama shiri domin lokaci ya kusa ƙure mata gashi kawarta Aziza sai kiran ta takeyi, jakar ta ta ɗauka, a tsakar gida tagama yafa gelen ta tana cewa Inna na tafi saina dawo...

adawo lafiya Inna tace tare da jinjina kai na  nuna damuwa irin halin ƴar ta ta.

A kofar gida suka haɗu da Aziza, sake baki Aziza tayi tana ƙarewa Fati kallo saboda gaye taci bana wasa ba, duk dama ba yau tafara gani ba kullum haka Fati take caɓa ado idan zasuje biki.

hannun ta guda biyu ta tafa mata a gaban fuska tare da cewa ya dai kamar baki ganeni ba, baki Aziza ta rufe sannan tace ai ke ɗin ce irin wannan gayen sai ayi tunanin ma angayyace mu alhalin ko invitation bamu gani ba bayan labarin da mukaji a makof ta… ƙarishe maganan tayi tareda fashewa da dariya....

Taɓe baki Fati tayi sannan tafara takunta cikin isa da kwarewa, tace sai kiyi ai, idan har bama zuwa irin waƴannan bikin kinfi kowa sanin bazamu taɓa samun gidan mijin dazamu huta ba, nidai inasa ran irin wannan wajajen ne zan haɗu da dan hamshaki wanda zai fiddani daga talauci.

Kayan da yake ɗinkawa akan keken ɗinki ya tattara ba tare da yagama ba, abokin sana’ar shi ne yace, lafiya Ahmad naga yau zaka tashi dawuri,  kodai akwai babban haraka ne irin taku ta manya....

yanakan tattara komatsen shi yace kaidai bari kawai, na manta dana cewa babe ɗin nan mu haɗu a wannan sabon gun shaƙatawan da aka buɗe, kuma kasan yanzu sainaje wajen Ilu me wanki da guga na samo shadda me tsada yadda bazata rainani ba, kasan yaran manyan nan basu cika son hidima da ƴaƴan talakawa ba.

murmushi abokin sana’an shi yayi sannan yace wannan gaskiya ne, shiyasa mu dai yaran talakawa irin mu zamu nema saboda gudun rainin arziki, da sauri yace kai aboki na raba kanka ai suma yaran talakawan masu kuɗi suke nema, irin ku kenan Ahmad amma ni na tabbata akwai daidai mu.

Haka sukayita ɗan taɓa musu har Ahmad ya tafi.

Suna isa kofan hall ɗin Fati ta tsaya ɗaukan hoto, Aziza da tagaji da jiran ta tace gaskiya nikam zan shiga ciki in kin gama ki sameni, hannu Fati ta yarfe tareda cewa sai ki shigan ai, nidai saina samu hotunan ɗaurawa a Instagram, ko zan samu sabbin masu bina (followers ), haka dai Aziza ta jirata badon taso ba sai dai don ko ta shiga babu Wanda tasani, koda suka shigama haka tayita ɗaukan hoto, don wajen yayi kyau bana wasa ba, wani kyakkyawan saurayi tun shigowar su yake bin su da kallo, karshe dai da yaga table ɗinsu su biyu ne sai yadawo table ɗin nasu, sallama ya musu suka amsa tunda yazo fati ta nutsu tadaina rawar kai kamar ba ita ba, yace musu sunashi Fahad, suma suka gabatar mishi da kansu, haka sukayita ɗan taɓa hira sama sama har aka tashi a wajen bikin...

har zasu fita yace musu idan ba zasu damu ba zai kai su gida, dama abunda Fati takeson ji kenan don haka ba wani jan aji suka amince, koda yakaisu anguwan su a farkon layi kofar wani gida mekyau sukace ya ajiyesu sun iso,  har sun fita yacewa fati dan Allah idan bazata damu ba tabashi number  ta mana, murmushi tayi wanda ya lotsa duka dimples  din dake kumatun ta, a zuciyanta tace anzo wajen lallai yau mun fito a sa'a, take sukayi musayan numba.

saida suka bari yawuce kafun suka kama hanyar gidajen su, yau farin ciki ne fal aran Fati saboda komai nashi ya mata, ga kyau ga iya gaye sannan daganin motan shi kasan ɗan masu kuɗi ne.



*Oumm Ameen*💞

A ZATO NAWhere stories live. Discover now