Bismillahir Rahmanin Rahim...
All praise be to Allah subahanahu wata'alah...
Daga farko Ina so na isar da sako game da labarin Nan meh suna Fatima Zahra qageggen labari me,Wanda banyi shi Don cin zarafi wani ko wata ba . Da fatan zaku karbe shi hannu bibbiyu..
Daga tako Aisha" hanifa"...1997...
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Prince Ashraf: Basarake ne meh ji da kyau da mulki ga Isa uwa uba korjini...Ashraf ya kasance da daya tilo gun mahaifan sa" Sarki Abdulbasir Salman da mahaifiyar shi Gimbiyar Etopia *manasa*.. Sarki Abdulbasir Sarkin Maiduguri ne..
Mai martaba nada Mata uku.Ta karko wato Hajiya balkis,ta biyu hajia rumaisa Sai ta uku gimbiya Manasa..Hajiya Balkis ta kasance ita ce matar sarki ta fari wacce aka musu auren hadi yanda al'ada ya zantar..haka zalika matar shi ta biyu...duk sun kasance sunci buri kan karagan mulki wato *Throne* din.ko wacce Tana so ta fara haifar da namiji,ya zama magaji..
Sai dai Kash ko waccen su ya'ya Mata ta Haifa.Sai mai martaba tafiya ta kamashi kan wani kasuwanci da taron sarakuna da za'ayi a kasar etopia...
Sarki Abdulbasir Salman ya samu karbuwa sosai,Don Banda zaman sa sarki akwai Abota meh karfi sakanin shi da prince Ashmar,sunyi karatu a UK " university of Oxford"tare yayin da akidar su tazo daya suka kulla abota..
Toh fah anan yaga Gimbiya Manasa...
Wanda ba'a Bata lokaci ba gurin bashi auren ta sabu sanaiya dake sakanin su da zumunci meh karfi..
Zuwan Gimbiya Manasa ba karamin daga hankalin su hajia giwar sarki wato Balkis da Gimbiya rumaisa..
Nan fah suka hade Mata Kai Amma na ciki na ciki,ganin sunfi kusa it's Kuma bare ce..
Amma sun Lura,Don a wannan karon zabin sarki Abdulbasir Salman ne🥀Don ya aureta me bisa zabin shi na kanshi ba auren hadi ba kamar nasu..
Haka rayuwa a cigaba yayin da Gimbiya Manasa tazo tare da amintattunta gudu biyar tun daga kasar su...Ta toshe duk wani Abu da zai hadata da sauran matan Don gudun magana da dattaku irin nata..
Gimbiya Manasa mace ce meh nutsuwa da sanin darajar Dan Adam,ga kyautatawa jama'a.
Sai da tayi shekara daya ta haifi danta sak Mai martaba,yayin da sauran matan suka ji labari tamkar saukan aradu,ai basu Kara girgiza ba Sai da akace Da namiji ta Haifa..
Wanda sarki ya Nuna farin cikin shi anyi shagali anyi kyaututtuka sosai a wannan Rana da yaro yaci sunan mahaifin Mai martaba Wato * Sarki Ashraf Wanda ya gushe*Tun Yana yaro ansha kawo Masa hari Amma Gimbiya Manasa*Giwar sarki Abdulbasir* ta kasa ta tsare...
Har Sai da yakai mun zalin girma da nutsuwa ya shige shi,yayin da mahaifin shi ya koyar dashi rayuwa kan karagan mulki..
Wannan Isa irinta sarakai da kwarjini bbu Wanda Ashraf ya bari na mahaifin shi Don jinin sarauta a jininsa yake..Ashraf yakai shekaru 19 Wanda sarauniya Manasa ta nemi ya tafi kasan waje karatu tare da mishi nasiha yayi riko da addinin shi da kamalar shi sannan yasan shi waye! Sarauta ba kawai sintar shi yayi ba! Aa every path shi cikakken Basarake ne,so Gadunta kayi Ashraf,nasan baza ka bani kunya ba Ina alfahari dakai...
Sarauniya Balkis wacce ke da ya'ya Mata uku ta farko Halisa,Khadija Sai ta uku Iman..
Halisa nada shekaru 29 Tana matakin hada Masters dinta,while Khadija ke da 27 Tana matakin second degree Sai Iman 25 wacce take first degree dinta..
Sarauniya Rumaisa wacce ta kasance matar sarki ta biyu,Tana da ya'ya uku ita ma,ta farko Aneesarh meh shekara 25 sa'ar Iman Wanda 2 month ne sakanin su,Sai safa da marwa Wanda suka kasance Yan biyu suna da shekaru 18... Ashraf ya girme su..
Wanda wannan labari na tafiyarsa kasar waje karatu ba karamin Kona musu rai yayi ba.Don sunyi sunyi abar Yan matan su fita kasar waje karatu,Mai martaba ya Nuna Sam beyi naam da wannan tsarin ba...
Bbu yanda suka iya suka yi shiru Amma sun kullace sarauniya Manasa..
Please
Comment
Share
Nd vote please...
Mu hadu a episode 2 insha allah.
YOU ARE READING
Fatima Zahra. dedicated to my dearly mom..
General FictionA arrogant nd handsome prince with middle class gurl,which he falls in love with her in first sight..