5

777 35 7
                                    

..........Sun jima a ciki yana nunama Abie abubuwa, yanda yaketa faman bayani da murmushi saika rantse bashi baneba. Dan har dariya sukeyi tare da Abie. Kiran sallar la'asar ne ya fiddosu, hakan yayi dai-dai da shigowar ɗaya daga cikin ma'aikata office ɗin, sannan kuma dai-dai da farkawar Anam data sha barci hankali kwance sanyin ac ya gama ratsata.
        Shigowar ma'aikacin mai suna Abeed tazo masa a bazata, dan hankalinsa gaba ɗaya nakan system ɗin gabansa, sai sallamarsa da buɗe ƙofa ne a lokaci guda suka shiga kunnensa. Da sauri ya ɗago idanunsa batare daya amsa sallamar Abeed ɗin ba ya kai dubansa gareta. Anam da bata san mike faruwaba duk da itama taji sallamar tai yunƙurin miƙewa tana laluben veil ɗinta da nufin ɗan lulluɓama jikinta. Abie ya riga ya shige toilet ɗin cikin office ɗin ɗaura alwala tunkan sallamar Abeed....
       “You are vary stupid!! Zaka shigo min kai tsaye”.
A yanda yayma Abeed tsawar da jefa mata rigar suit ɗinsa dake a jikin hanger ba shi Abeed ɗin ba hatta ita sai da ta zabura. Da sauri ta ɗane kujerar baki ɗaya ta ƙudindune kanta dan sam bata ƙaunar tsawa a rayuwarta. Cikin rufewar ido da manta Abie na'a office ɗin ya sake dakama Abeed tsawa da cigaba da masa masifa. Shi dai yay ƙasa da kansa dan bai san laifinsa ba anan har yanzu, tunda ya san ya yi sallama ya kuma yi knocking....
        “Get out!!”.
Ya sake faɗa a tsawace. Da sauri Abeed yay baya da rufe ƙofar. A fusace ya maida dubansa ga Anam da ke leƙosu ta cikin rigarsa. Ya watsa mata wata uwar harara, cikin gargaɗi mai kaushi,
      “Idan kika ƙara fitowa da wannan ƴan iskan kayan saina kashe fuskarki da marukan da bazata ganuba. Stupid girl! An faɗa miki nan muna buƙatar sune”.
    Baki ta tura gaba duk da ta mugun tsorata da yanayinsa. “To ni Yaya MM wannan duk sune kayana ai, kuma ni su na iya saw.......”
    Ganin ya yunƙuro zai tashi ta miƙe da sauri ta koma bayan kujera fuska a kwaɓe. Ƙwafa yay da sake watsa mata harara. Abie dake tsaye da ga bakin ƙofa yana kallonsu tun ɗazun basu lura da shi ba yay murmushi, domin kuwa wasu abubuwa masu ban mamaki ya hango a cikin ƙwayar idon ɗan nasa, ya girgiza kai kawai da ƙarasowa ciki. Sai lokacin Shareff ya lura da shi. Ƙasa yay da kansa dan shi gaba ɗaya yama manta Abie na'a office ɗin. Miƙewa yay sum-sum ya nufi toilet batare da ya yarda sun haɗa ido da Abie ba. Shima baice masa komai ba sai binsa da yay da kallo kawai. Anam dake a laɓe sai da taga ya shige sannan ta fito, cikin taɓe fuska ta ƙaraso inda Abie yake tana faɗin,
     “Uhhm Abie ALLAH Yaya Shareff baida kirki, yanama staff ɗinsa ihu bai masa komaiba kuma”.
    Nanma murmushi kawai Abie yay baice komai ba. Zata ƙara magana Ya Shareff ɗin ya fito tai saurin komawa bayan Abie ta ɓuya. Sai dai hakan bai hanata ganin hararar daya watso mata ba.

★★★★★

         Washe gari su Abie suka wayi gari da shirin kai kuɗin auren Ya Shareff, wanda dama yana ɗaya daga cikin dalilinsa na zuwa Nigeria, dan data Anam ne kawai turota zaiyi tunda yasan akwai mai iya mata komai ai. Ita dai Anam bata san mike faruwaba ma, dan ta jima bata tashi a barcin safe ba kasancewar daren jiya tunda aka ɗauke wuta ta kasa komawa barci saboda zafi, duk da kuwa Mom ta kawo mata fan ta kunna mata saboda tsaki data dinga zubama su Husna kamar wata dangin tsaka, sai dai kuma fahimtar iya gaskiyarta ne yasa Ikram zuwa ta faɗowa Mom ɗin. Ganin akwatuna har set uku a falon Mom masu shegen ƙyau da tarin kayan sa rana ya sata tambayar Ya Khaleel first born ɗin Mom. Shima dai saurayine zangarere da shi dan yana shekara ta 26 a duniya. Khaleel ƙyaƙyƙyawa ne shima kuma nutsatstse. Sai dai akwai tsare gida da rashin son raini harma yafi Shareff zafi, dan shi Shareff inhar baka shiga gonarsa ba babu ruwansa da kai, sannan yana da sakewa da jama'a fiye da Khaleel. Shine na uku a haihuwa a gidan. Dan sanda Mom ta auri Abba haihuwar Mommy biyu ne. Daga Shareff sai Maheer da take goyo. Duk da Shareff ya bama Khaleel shekaru sosai hakan bai hana ƙaunar juna shiga tsakaninsu ba, dan tunda ya dawo daga Indonesia bashi da wani aboki a gidan kamar Khaleel. Da taimakonsa ya san wajaje da yawa daya manta, sannan tun a baya idan yazo hutu dama shine abokin yawonsa saboda nutsuwar yaron na birgesa. Yafi Maheer hankali sosai da sanin ciwon kansa, dan yanada himma da ƙwazon nema duk da ko maganar aure bayayi ma.
       Duk ɗaurewar Khaleel suna ɗan shiri da Anam, sai dai itama ba wani sake mata yake ba dan miskilanci a jininsa yake. Kamar bazai tanka mataba yanata aikin danna wayarsa sai kuma ya kalleta. “Kayan auren Yaya Shareff ne”.
      “Ya mi?! Dama aure zaiyi!?”.
A yanda tai maganar ya tilastashi sake dubanta da ƙyau, haka kawai yaji dariya ta taho masa. Amma sai ya gimtse.
       “Kinada matsala da auren nasa ne Granny”. (Dan haka yake kiranta mafi yawan lokaci).
     “Kuji Ya Khalel ɗin nan da wani magana. Ni ina ruwana da wani aurensa da har zai zamar min wani damuwa. Ai sai dai nai murna zai tafi can ya barmu mu huta matan ta kwashi baƙin hal......”
     Jin ta gagara ƙarasawa yasa Khaleel fashewa da dariya, dan dama dai tun ɗazun ya lura da Shareff daya fito daga bedroom ɗin Mom. Ita kuma sam ALLAH baisa ta lura ba sai yanzun da yaƙe ƙoƙarin baro corridor ɗin baki ɗaya dan dama kamar ya ɗan tsayane yana sauraren su, amma a zahiri waya yake dannawa. Duk da ba inda take yayo ba da gudu ta afka ɗakin barcin su harda murza key.
     Shiko dama daba inda take yayo ba harara kawai yawatsama Khaleel da faɗin, “Dalla tashi muje ka zauna kana abu kamar wani yaro”.
         Har yanzu dai dariya ƙunshe a bakin Khaleel ya miƙe. Idonsa na duban ƙofar da Anam ta shige. Suna ƙoƙarin fitowa yace, “ALLAH my best yariyar nan sam bata da wayo har yanzu. A hakan wai kuma ta kammala karatu. Bayan rashin wayon ƴan fari a jikinta harda taɓarama na ganin ita kaɗai ce a gaban su Mamie. Jiya fa harda kuka ta dinga yima su Mon wai zafi saida aka kawo fan aka kunna mata”.
      “Mom ɗince ta biye mata mtsoww ”.
Ya faɗa cikin halin ko in kula. Shi dai Khaleel yace, “Gara dai da aka kunna mata dan bata saba da zafin nan bane namu. Su da suke fama da dusan ƙanƙara ma wasu lokutan dan tsabar sanyi. Kaga ko tazo nan dole ta shiga wani yanayi dan kano ogace ta zafi..”
      Komai bai ƙara cewaba yay gaba Khaleel ya bisa.

BABU SO...Where stories live. Discover now