🦽👨🏻‍😭SUN GUJE NI )😭👨🏻‍🦽
(SANADIN CUTAR LAKKA)
   IT BASED ON TRUE LIFE STORY.

LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).

SHAFI NA BIYU.

*RANA ZAFI INUWA...*
   Wacece mace tagari ?kuma wani mataki ake bi domin a samo ta?
  Mace tagari ita ce macen da ke ƙoƙarin sauke dukkannin wani nauyi wanda Allah ubangiji ya ɗaura akan ta wanda ya ke tsakanin ta da mijin ta,itace wacce in ka kalle ta ko da kana cikin ɓacin rai sai ka ji sanyi acikin zuciyar ka saboda tunawa da ka yi ka zo gaban mai rarrashin ka,ita ce ma'adanan sirrin ka mai ƙoƙarin killace sirrin ka da killace ma ka dukiyar ka,ita ce bango abin jinginar ka,itace mai share maka hawaye ayayin zubar su sannan itace mai koƙarin rumgume ka a duk lokacin da aka ce ma ka ka durƙushe,ita ce mai tunasar da kai haƙƙoƙin Allah a kan ka sannan ita ce za ta tsare ma ka mutuncin ka ta hanyar killace ma ka kan ta idan kuma ku ka samu zuriya da ita ,ita ce makaranta ta farko a duniyar ahalin ka,za ta koyar da su darussan ma su wuyar mantawa sannan ta koyar da su yanda za su bauta ma ubangijin su cikin tsafta da tsarki tare da ƙanƙan da kai".zuciyar sa ya naƙalto ma sa,

Hanyoyin da ake bi dan mallakar mace tagari kuwa Annabi sam bai ɓoye mana ba tun da ya fa ɗa mana cewar" idan za ku yi auri ku auri mace ma'abociyar ilimi" ba wai ka aure ta dan tsantsar kyan ta ba saboda idan ka aure ta dan kyau watarana za ta tsufa,idan ka auri mace dan nasabar ta ko mulki watarana nasabar da mulkin za su gushe,idan ka auri mace dan dukiyar ta kuwa watarana dukiyar za ta ƙare amman idan ka auri ma'abociyar addini shi ilimi sam ba ya gushewa dan ilimi gadon Annabawa ne da salihan bayi dan haka shi kogi ne da ba ya ƙafewa samun mace tagari mace tagari shine tushen samun nagartaccen zuriya".
(Amman yanzu a wannan lokacin na mu ƴanmata da samari sun sanya ƙafa sun yi fatali da wannan koyarwan ta Annabin tsira sam ba sa bin waɗannan matakan kafin yin aure shiyasa kuwa mu ke ganin rashin daidai a rayuwar auren mu na wannan zamanin cewar ummu jiddah)

Yuzarsib wanda ya gama wannan tunanin tuni ya ji zufa ya jiƙa mi shi taguwar shi ƴar shara da ke jikin sa wanda ya sa aka ɗinka ma sa ita musamman dan lokacin nan na zafi dan rigar ta kasance ba ta da hannu har ka na iya hango farar singilet ɗin sa fara tas,zama ya yi ɗabas a ƙarƙashin bishiyar da ke gabas da gidan sa dan ya fito ne da niyyar ya je ya ci abinci amman tunanin matar sa Ra'isat shugabar ƙazaman matan jihar su ya sanya ya mance in da za shi kuma sai bai isa ya je gidan su dan ko da ya je maman sa ba za ta bashi ba cewa za ta yi kar ya cika ciki ya bar mata ƴa da abinci wannan shi ake kira da rana zafi inuwa ƙuna,

jingina ya yi da jikin bishiyar cike da tawakkali da sakankance wa na miƙa ma Allah kukan shi ya ce"Allah na san ka na ji kana gani,ka kuma fi ni sanin halin da na ke ciki dangane da mata ta"

"Allah ka san na aure ta ne saboda in yi ma mahaifiyata biyayya, Allah ka yi ma ni maganin abinda ya dameni alfarman biyayyar da na yi a gareta".

Tamkar wanda aka cire mishi ƙaya haka ya ji bayan ya kammala addu'ar sa ya ji duk damuwar sa ta wanye iska na kaɗa shi ta kowani sashi ,

jin ya samu nutsuwa ya sa ya miƙe yana waige-waige dan sam bai san inda ya dosa ba,har ya isa gurin abokan shi da ke xaune a teburin maishayi kasancewar yamma ya yi,

"Young Alhaj"shine sunan da su ke ƙiran shi da shi  amman tunda ya yi auren nan watanni biyu baya ya koma "Ango ya sha mai",

sai da ya tattaro da dukkannin nutsuwar shi kafin ya tunkare su ya yi musu sallama,su na ganin shi gurin ya kiɗime da kiran sunan "Ango,Ango"

"Na'am ya son ran ku gwauraye"

"ji ɗan iska to yaushe kai ma ka yi auren har za ka fara mana gori"cewar wani daga cikin su,

"Watanni biyu da su ka wuce  ka ga kuwa na daɗe da fita daga ajin ku"ya furta hakan yana zama a tsakiyar su tare da kyalƙyalewa da dariyar shaƙiyanci irin dai yanda abokai kan yi in ɗaya ya riga su aure an dinga zolayar juna kenan,

"To uwar me ya kawo ka teburin maishayi mai mata"

"Kuɗi masu gidan rana"ya ba su amsa tare da umurtan mai shayin ya dafo mi shi taliyar indomie da ƙwai da kakkauran shayi rabin gwangwani,

Nan guri ya ɗauki sowa wani na cewa "aikuwa wallahi ka ci baya gardi ya dafa mana abinci mu ci kuma kai mai mata kaima ka ci"

"kare da kuɗin sa fa........."ya ce mu su,nan mu su ya kaure a tsakanin su

Aminin shi wanda ya fi kowa kusanci da shi ya  ce"kai ku dakata banzaye dan Allah,ni fa tuni na san me zuwan shi wannan gurin ya je nufi",

dakatawar kuwa su ka yi suna kallon shi ya ce"Amarya ta samu ƙaruwa ne girki na gagarar ta"

Yusuf ya harere shi tare da cewa "kai kam shegen gulmar ka ke haɗani da kai to wa ya sanin makan ko hakan ne,

"to wai ma ina ruwan ka?,

shiru ya yi yana kallon sa tamkar sakarai kafin ya sheƙe da dariyar shaƙiyanci ya ce

"ni ko na ke da ruwa dan garama a faɗa min da wuri in fara shirin kayan takwara dan na san ɗan mu na farko suna na za ka sa ko my second?"ya ƙarashe maganan ya na ƙanne ido ɗaya,

"sosai ma ba dai kai ka bada sadaki da kuɗin gaisuwa ba,ka yi lefe ba,ai dole na in sa sunan ka da gudu na ma ai Ubana na bariki"

Dariya maganan Yusuf ya ba su nan su ka kyalkyale da dariyar gabaɗayan su daga bisani su ka cigaba da hira har sai da aka yi kiran sallan Magrib kowa ya watse dan zuwa sauke farali.

sai da aka sallaci sallar ishsha sannan Yusuf ya bar masallacin,faɗuwar da gaban shi ya ke ya  ƙaru dan shi kam duk lokacin da ya dunfari gidan shi sai ya ji wani faɗuwar gaba na musamman saboda ya san dole sai ya je ya taras da abin da ran shi zai ɓaci,a yayin da ya fito waje kuwa sai ya ji tamkar wanda aka fitar daga cikin ruwan zafi gaskiya yana karɓan gashi shi kam bai dace ba wallahi,

Aikuwa yana buɗe ƙofa ya faracin karo da tulin wankin kaya da ya umurce ta da ta tattaro ta fiddo su waje akai wanki dan ba ya jin tun da tazo gidan ko ɗan kamfai ta taɓa wanke wa,duk uban kayan lefen da aka haɗo mata ta sanya ɗinkakkun da ƴan kantin,

ganin yanda ta ke wurgo kayan a  tsakar gidan ga wani irin warin ɗauɗa ya sa ya yi gyaran murya wai ko zata ji shigowar sa ta tsagaita amman sam bata ma ji shiba sai ma wani kayan al'adar ta da ta watso ya sauka a saman fuskar sa nan wani ƙarni da hamami ya dirar  masa nan ta ke ya fara amai tare da yin hanyar makwarari ya fitar da duk abinda ya ci nan ya koma gefe riƙe da cikin sa yana mayar da numfashin wahala,

Ra'eesat wacce ta fito jin kakarin aman shi tsayawa tayi tana ƙare mi shi kallo sheƙeƙe can ta ce"auu daman ba ka da lafiya ne?",

Shiru ya yi mata kawai dan yana iya shaƙe ta a yanda ya ke jin haushin nan na ta dan sarai ya san da gangan ta mashi abin da ta yin saboda ya san ta ji ƙarar ƙofa lokacin da  ya shigo har ma ya hango ta tana leƙen shi,

Jin bai ce ma ta komai ba ya sa ta juya tana ƴan waƙe-waƙen ta duk da ya na buƙatar taimakon ta a lokacin na ruwa amman haka ya bar ta ta wuce dan  jikin sa ya yi sanyi kun san amai da kashe jiki.

Wannan mutum ce ko dabba fans?



*Ummu-jiddah*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 24, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SUN GUJE NIWhere stories live. Discover now