Part title

198 10 9
                                    

🌚Masarautar Qamar

Bismillah Rahmani Raheem

By Khadija (KMU)

Page 1&2

Tafiya takeyi a hankali kanta a sama har ta isa inda take saida Awara hada kayan suyar ta tayi wanda daman an riga an kawo mata su tun kafin ta taho nan da nan ta fara soya awarar ta nan da nan ta fara ciniki as usual kafin kace kwabo ta saida awararta ta amshe kudin ta tass

Yara uku ta samu tace su daukar mata kayan awarar ta saida yaran sukayi gaba ta biyosu

A hankali take tafiya wadda kamar dagan gan take yinta dogayen kalaba ne guda hudu a kanta wanda suka zubo mata har gadon bayanta gashi nan nata bakir kirin earpieces ne a kunnenta tanajin wakar rush by ayra star daidai majalisar su tareeq tazo wucewa zayyad ne yace gafa demoness nan ja'afar ne yayi dariya yace to kaje ku gaisa yace ka rufamin asiri tareeq ne yace bullshit yace meyasa kuke maida kanku baya wai sai yayi shiru zayyad ne ya kwashe da dariya nasan mi kakeson kace miyasa muke tsoronta to ai naga kai baka tsoronta don Allah I dare you to go and confess your love to her right now dan iska inji zayyad shidai ja'afar dariya kawai yakeyi abinshi.

Tareeq cikin muguwar hasala ya nufi daidai inda take.

Hurriya jin wakarta takeyi hankali kwance da yar karamar wayarta Mai malatsi kallon tareeq tayi da idanunta masu kyau wanda duk bala'in ka baka iya minti daya cikinsu frowning face dinta tayi tana raising brow daya irin miye matsalar ka kasa kallonta yayi kallonshi tayi in a mocking way tace ka fara gadi ne ko kana bina bashi the girl is beautiful not just beautiful but extremely beautiful she's got this flawless caramel skin that looks like miloo and creamy milk that are put together to give her this perfect and flawless skin idanunta are dark brown which made her look intimidating she' thin and tall the girl is almost perfect with nothing left for people to criticize sai dai bata kama da Nigerian's kwata kwata she's more like an Ethiopian tareeq da banda kallonta ba abinda yakeyi don he can swear wannan yarinya sune hurul tin wato masu kyaun duniya Hurriya ta kalleshi tace hey i'd slap you but that will be animal abuse ta ida maganar da wani tone na raini get lost tace tareeq da daman kamar abinda yake jira kenan yayi sauri ya nufi wurin abokanashi da suna ta kallon drama tasu Hurriya saida tazo ta saitin su ta kallesu tace bunch of idiots sannan ta wuce tayi hanyar gidansu dukansu bayanta suka bi da kallo wanda gashin kanta kawai ke lilo

Da yar sallamarta ta shiga gidan da take zama, tabawa bata amsa ba itama Hurriya ko a jikinta ta kusa shiga dakinta kenan taji tabawa nacewa shigar mutum kadai ta isa kasan kowaye mutum a hankali tayi maganar yadda bata tsamanin Hurriya taji abinda tace saidai fa Hurriya Allah ya horeta da ji don kamar giza gizo haka take dawowa Hurriya tayi saida taje saitin tabawa ta zuba mata idanun ta masu masifar kyau saidai ba maisan kallon su saboda abinda suke fiddawa wato flame ta kalli tabawa tace gwara ni nawa a bayyane yake naga taki diyar kuma kullum cikin hijab take Amman sana'ar ta wato saida jiki from this man to another ta amso maku kudi kullum ita ake kallo a matsayin ta kirki nice ta banza Tace and i don't give a damn because people always think about what they see and believe what they want to believe so I'm at your service shegu masu kan kwarya tana gama maganar ta shige dakinta tabawa da ta hangame baki bude duk inda sabo ma ta saba Amman Abun Hurriya kullum kara karuwa yake

Hurriya kam risho ta fiddo ta kunna ta dora ruwa ya mutu ta juye abokiti ta shiga ban dakin su tayi wanka tayi alwala wata hijab ta nemo sannan tayi sallah duk da cewar sallahr bata wani iya ba Sosai ba Amman tana kokar tawa sosai hijab din ta ajiye sannan ta ciro kudin awarar da tayi ta fidda kudin siyyarta sauran kuma na adashe ne da takeyi abinta. Yunwa ta dan dameta don haka ta zari dari biyu ta fito jeans ne a jikinta sai wata yar karamar riga maroon ta fito duk inda ta gifta kallonta ake but she don't give a damn saida tayi tafiya mai dan nisa sannan taje wani shago ta siyi indomie guda daya ta juya ta koma gida dan risho dinta ta kunna ta dafa indomie din tana gama ci ta kwanta sai bacci domin ta gaji bata samu asuba ba don sai karfe shidda ta samu ta tashi daga baccin tsakar gidansu ta fito ta shiga tayi alwala sannan tayi sallah.

Wani blue din wando ne jikinta sai t-shirt Mai zanan zaki fuskar ta fayau sai dogon gashinta da ta nade sosai gidan mai-anguwar su taje hade da sallamarta a tsakar gida iske matar gidan wadda Kamar ita take jira wanke wanke aka fiddo mata ta zauna tayi abinta bayan tagama tayi shara da sauran ayyyukan gidan.

Kallonta laminde tayi wadda tagama dafa shayi zata kaima Mai unguwa tace Hurriya angama ne daga mata kai Hurriya tayi wadda ta samu kujera ta zauna tana jin wakarta ,ta saba indai Hurriya ce duk yadda kaso kayi fira da ita bata baka dama abinda ya kawota shi kawai zatayi ta kama gabanta

Laminde bayan ta kaima mai unguwa karin kumallo ta zuba ta mika ma Hurriya itama shayi da bredi amsa tayi ta cinye ba tare tace ta gode ba tana kallon Hurriya tagane nufinta don haka ta miko mata dari biyu kudin aikinta sannan ta kama hanya ta tafi gida saman katifar ta haye ta danyi bacci bayan ta tashi daga bacci ta wanke fuskarta sannan ta fita ta bada kudin adashen ta wanda take zubi kullum

Tana fitowa daga gidan adashen ta nufi yar karamar kasuwar da take siyen waken suya da murmushi Saminu ya tarbi Hurriya ya gaisheta as usual don duk idan zata zo wurin shi bata taba gaishe shi ba sai ya kasance yana gaisheta da kanshi saboda ko zata kula ta gyara Amman ina idan ya gaisheta zata daga kafada ne taki amsawa yasan batasan dogon bayani tafison duk abinda tazo ayi mata shi lokacin da takeso don haka yace Hurriya bani da wake yau amman ga ashiru can ki siya a wurin shi daga kai Hurriya tayi ta nufi ashiru dake awo kallonshi tayi da idanunta tace a bani wake kallonta yayi sama da kasa sannan yace kindai san kudin waken Hurriya batace mashi komai ba har ya fara zuba waken cewa tayi batasan shi ta nuna mai kyau tace ya zuba mata ashiru kam ya bata fuska yayi banza da ita ya cigaba da zuba wake Hurriya batace mashi kala ba ya miko mata waken bude ledar tayi kamar tana dubawa ashiru yace malama ki bani kudina kina wani leka abu kamar An cuce ki bani san shegantaka idan bakiso ki bani kayana Hurriya batace kala ba daukar ledar waken tayi ta juye mashi abinshi sannan ta sanya tiya ta auni mai kyau ta juye a ledar ta ajiye mashi kudin shi ashiru da mamakin ta ya kamashi daman waye baisan shi a kauyen ba saboda fitinar shi masifarfe ne na bala'i kuma tijarare don haka saitin da Hurriya take tafiya ya tsaya yace yau rashin tarbiya da rashin da'ar kaina tazo karuwa to baki isa ba don wallahi yau sai na cin mutunci ki don ba'a haifi wani a garinan da Zaici man mutunci In kyaleshi ba daga hannu yayi da niyyar marinta Hurriya bata matsa ba kuma batace kala ba saidai flames din idanunta da suke fita a idonta bama gaskiya bane don wani mugun kallo tayi mashi wanda ya sanya dole saida ya aje hannunshi kasa sannan tace I dare you to slap me tayi wani tauna lebenta sannan tace sakarai waye duk garinan bai sanka ba da molesting yaran mutane ba kowa yana tsoron ka saboda rashin mutunci ka and you're here calling me a whore ko cikin ni dakai waye babban dan iska ta nuna kanta tace ni ko kai sannan tace to idani karuwa ce dakai nayi karuwancin ko kuma da tsoho shiru ashiru yayi sannan ta kara zuba mashi wannan idanun nata tace daga yau na karajin kayi abinda bashi bane sai na kira ma hukuma sun tafi dakai sun bama karensu ya cinye ta ida maganar tana mashi kallon cewar Ina maka gargadi tace sakarai Dan Akuya sannan tayi gaba abinta tabar ashiru da sakin baki da kowa na layin mamakinta yake saboda abinda bai taba faruwa ne ya faru shikanshi ashiru kasa matsawa yayi daga inda yake lallai hausawa sunyi gaskiya yaro baisan wuta ba sai ya taka.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 28, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Masarautar QamarWhere stories live. Discover now