AKIDAR WASU MAZAN PG 02

0 0 0
                                    

♡'''AK'IDAR WASU MAZAN'''♡♡♡

                '''NA'''

            
'''KHADEEJAT BAITA( mamashu)'''

'''Littafina na kudi ne akan farashin 200 kacal ki biya ki more karatunki cikin salama domin biya ki tuntubeni ta wannan lambar 08161536074.'''

'''
Daga marubuciyar:'''

*Kaddarata ce*
*Ni da surukata*
*Yaya mata.*

'''Yanzu kuma na zo muku da wani sabon labari mai taba zuciyar mai karatu,zallar butulci,Rashin godiyar Allah soyayyya hade da tsantsar nadama,duk a cikin wannan littafin kedai kawai ki biya ki mallaki naki. Kunsan alk'alamin yar MUTAN GIWA baya rubuta shirme.'''

'''Wannan littafin sadaukarwa wane ga Abdallah Abdallah Abubakar ( Abbapossible)'''

'''Bismillahir Rahmanir Rahim'''

         Chapter two

.......✍Mirginawa ya yi cikin b'acin rai me yasa Khairin sa zata b'ata masa rai alhalin yana cikin farin cikin kasancewa da ita,tsaki ya saki mara sauti tare da kashe fitilar da ke gefen gadonsa ya koma ya kwanta,tunani ya fad'a na yadda zai yi kar Khairi ta haihu da wuri domin shi kwata kwata a tsarinsa yara biyu kawai zai Haifa kuma daga su babu k'ari mace da namiji kawai yake so babu tsarin tara iyali a wajensa yadda turawa ke haihuwa shima haka zai yi dan haka babu batun wata haihuwa da yawa,idan ban da abun Khairi haihuwar fari ta fara da biyu ai ta kashe ni kuma ina laifin ta shekara Goma kafin ma ta haihuwar farko sannan kuma ajira aga na biyun,sakin wani tsakin ya yi. Da kyar dai bacci ya d'auke shi hirar da ba a karasa ba ya yi ta cikin mafarki.

Washe gari cikin shirin tafiya kamfanin mahaifinsa na had'a batteries na mota ya fito kyakkyawa ne sosai ajin farko dogo mai cikar zati fuskar sa na dauke da kasumba wadda ta dace da kalar fatarsa,bai da haske sosai kuma bai da duhu kalar fatarsa irin chocolate ne amma mai haske yana da manyan ido hade da dogon hancin da ya dace da karamin bakinsa yana da faffadan kirji hade da yar kiba kadan ba mai muni ba sosai Muazzam kakkyawa ne kalar irin da Mata ke so ne domin ya hada duk wani cikar halitta da ake so namiji ya kasance.

Fitowa ya yi daga b'angaren sa ya nufi cikin gidan dan gaisawa da mutanen gida, tin da ya doshi k'ofar parlon ya fara jiyo hayaniyar yaran gidan take zuciyar sa ta buga shifa bai son hayaniya ji yayi kamar ya koma amma babu dama tinda k'aidane dole duk wanda ya kwana ya tashi a gida ya zo ya gaida mahaifinsu, d'aure fuska ya yi tam sannan ya shiga parlon cikin sallamar sa Wanda bata ga ma fitowa da ga cikinsa ba ya shiga parlon.  Yaran dake ta hada hadar cin abinci ganinsa kowa ya shiga taitayinsa tare nutsuwa,Mum Sara Amaryar Alhaji Jaafar ce ta tsuke fuska tare da kallonsa tace " Daga shigowar ka yara duk sun nutsu kamar sun ga wani malaikan mutuwa gaskiya kana matsa yaranan". Dan sakin fuska ya yi tare da shafa gemunsa yace " Haba aunty Amarya ni me kika ga nayi musu"? Dariya ta yi sannan tace " Ai dai mun kusa kai ka naka gidan mu huta yaran mu ma su huta". Shima dariyar ya yi yace " Ai kuwa dai ,Abba bai fito bane naga karfe 8 ya kusa?" Ya juyar da maganar ta hanyar tambayar ta.

" Yanzu zai fito ya gama shiryawa" itama ra bashi amsa, Wucewa ya yi dakin mahaifiyar sa domin gaisheta nan ma kannensa ya gani suna shiryawa Aysha da Zainab sai Rukayya kallonsu yayi da dan sakin fuska yace " Ina Mum?" Rukayya ce ta bashi amsa tace " Wanka take". Neman waje ya yi ya zauna tare da fito da laptop dinsa yana dubawa. Mum hajara ce ta fito daga dakinta cikin shirin fita,Kallonta ya yi yace " Mum ina kuma zaki da wannan safiyar?" Zama tayi kafin ta bashi amsa" Ai ma gaisa kafin ka fara min tambaya ko?" K'aramar dariya ya yi yace " Mum Ina kwana?" Lafiya lau" itama ta bashi amsa sannan tace " Humaida ce ta haihuwa yar wajen Asiya shine zanje asibitin tinda aiki a kayi Mata jiya shine na shirya kaga ma ka wuce dani ba sai direba ya kaini ba". " Haihuwa kuma duka duka yaushe Humaida ta haihu amma kuma har  ta kara haihuwa?" Ya tambya cikin jin haushi, " To laifi ne dan ta haihu kuma Muaazam? Mum hajara ta tambya cikin mamaki.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 13, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AKIDAR WASU MAZANWhere stories live. Discover now