PAGE__1

43 4 2
                                    

🤱🏻🤱🏾 *UWA DA 'DA...*🤱🏾🤱🏻
                💎 _Sai Allah_💎

_Writting by:_ *_BILLY S FARI💎_*

Re-post on December 2022

_Wannan littafi haƙƙin mallakata ne ban yarda wani/wata su canza mani labari ta kowace irin sigaba saida izinina! Saboda haka akula👈_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
   
    **TRUE LIFE STORY**

💎page___1💎
          

Ruwa akeyi sosai tamkar da bakin ƙwarya, yayin da gari yayi baƙiƙirin ko tafin hannun mutum baza ya iya gani ba, kasan cewar dare ya farayi babu wani haske da zaka iya hangowa ta ko ina face hasken sararin samaniya da hasken walkiya da aketa faman yi, wata mata na hango can makure a bayan wani ɗan madaidaicin gida, wanda kallo ɗaya zaka yiwa gidan ka gano gidane na masu rufin asiri daidai gwargwado.

Cikin mamaki nake kallon kyakkyawar matar data ƙurawa agogon dake ɗauke a tsintsiyar hannunta kallo, wanda ya nuna kusan karfe takwas da kwata na dare, a lokacin gabaɗaya angama sallolin isha'i a mafi yawan masallata anguwar, ajiyar zuciya na sauke kafin na ƙurawa matar da jikinta ya soma rawar sanyi saboda yanda ruwan sama suka duketa idanuwa, wata irin tsawa akayi wanda ya sata rintse idanuwanta saboda tsabar firgitar da tsoro tana sake shigewa jikin katangar gidan, a daidai lokacin ne na samu damar ƙare mata kallo tsaf, Kyakkyawar mace ce fara tas mai manyan idanuwa dake ɗauke da zara zaran gashin idanuwa, sai siririn hancinta daya saitu da ɗan madaidaicin bakinta mai ɗauke da tausasan laɓɓa, abun dai tubarkallah masha Allah sai wanda ya gani.

Sanye take cikin wani haɗaɗɗen lace da kuɗinsa zai kai kimanin dubu arba'in zuwa sama, haka ma mayafin dake rufe a jikinta aƙalla shima zai kai dubu goma zuwa sha biyar, a shekaru kuma baza tawuce shekaru ashirin da biyar ba (25yrs), kana kallonta zaka san cewa ita ɗin ɗiyar wani hamshaƙin mai kuɗi ce duba da irin shigar dake jikinta da kuma gwalagwalan dake shimfiɗe a jikinta,

A hankali ta fara buɗe idanuwanta cikin mantawa da yanayin da take ciki ta shiga dube dube ko ALLAH zai sa ta hango abunda tazo nema,
ta daɗe tsaye tana jiran ko zata ga fitowar maigidan zuwa wajen sallar isha'i don ta samu damar cika burin data kwashe kimanin watanni tara tana neman yanda zata cikasa ba dare ba rana, ba bu wata rana da zata zo ta wuce ba tare data shigo anguwar ba don tasamu damar cika wannan burin nata ba tare da an ganta ba, amma kash! har yanzu haƙarta ta kasa cimma ruwa saboda yanda aka kasa kuma aka tsare tare da bawa wannan abun kulawa fiye da tsammanin ta yanda burinta bazai taɓa cika ba a kansa, wasu zafafan hawaye ne suka sauko mata afuska cike da nadama da dana sani, cikin raunin muryar ta ce,

"Ya ALLAH ka dubeni da idon rahama kayafe mun kuskuren dana aikata da kuma laifukana ka bani ikon ɗauke ƴaƴan a wannan daren, ALLAH ka tausaya mani ka dawomun da farin cikina a hannuna tare da bani dama ta biyu domin gyara kuskurena". Cikin wata irin husky voice irin ta jaruman mazaje dake cike da ɓacin rai da kuma al-ajabin ganinta a wajen ta ji ance, "Too late to cry Sha'awanatu!, In Sha ALLAH har abada 'yarki baza ta taɓa dawo hannunki ba !, HAFSAT (UMMITA) 'yatah ce Ni kaɗai, kuma bazan taɓa bari tasan koda mai kama dake ba balle kuma ke, zan reni abuta kuma na bata kulawar da baza ta taɓa nemanki ba a matsayin uwa, zan yi mata fatar da bazata taɓa barinta yin tunanin uwa ba aranta balle har ta nemi saninki,  "Kabir.." ta faɗa cikin muryar kuka ya yi saurin dakatar da ita haɗe da cewa, "bari in tunatar dake abun da kika manta, ke da kanki kika nemi wuƙa cikin rashin tausayi da imani kika datse igiyar soyayya da tausayin dake tsakanin UWA DA 'DA kika ce bazaki iya kula da ita ba, saboda idanunki sun rufe da tsanar mahaifinta, kika kasa tuna halaccin da uwa take dashi ga ɗanta don son zuciya da kuma kwaɗayin duniya, to bari kiji in faɗa maki wlh tunda har kika rufe idonki kika yi ƙoƙarin maido Ummita a hannuna lokacin da take matuƙar buƙatar ki ba tare da kin tausaya mata ba duk da ƙanƙantar ta, ni kuma bazan taɓa jin tausayinki ba balle har in iya ɗaukarta na sake baki ita".

Yana kaiwa nan ya juya yabar wajen idanuwansa jajir tamkar an watsa masa barkono saboda tsananin ɓacin rai, cikin kuka tayi saurin kamo gefen rigarsa haɗe da zubewa ƙasa a gabansa tana faɗin

"Haba Kabir, don ALLAH kaji tausayina, wlh ina son matuƙar son Ummita har cikin raina, ɓacin rai da son zuciya ya sani aikata haka, kuma yanzu na gane kuskurensa don ALLAH ka bani ƴatah". Ganin ya yi tsaye haife komai ba ya sata miƙewa tsaye tana kallonsa haɗe daci gaba da cewa, "Haba Kabir! taya kake tunanin uwa zata nisanta da ɗan ta kuma ace ɗan ma ƙarami sosae kamar Ummita kayi tsammanin zata samu natsuwa a zuciyarta da kuma gangar jikinta, don ALLAH Kabir kamanta da abunda ya faru kabani ƴata, na yimaka alƙawarin zan zamo uwa ta gari agareta tare da bata kyakkayawar kulawa fiye da tsammaninka.

Wani irin murmushi ya saki dake ɗauke da ma'anoni kala-kala zuciyarsa na suya da kuma ƙuna, wani mugun kallo ya keyi mata ba tare da ya ce  mata komai ba, hakan ya sata cewa, "Plz Kabir say something.." kafin tarufe baki aka saki wata irin tsawa, cike da tashin hankali da firgita ta faɗo a jikinsa ba tare data san hakan ba.

Da karfi kabir ya tattaro jarumtar data ragemasa don shima kansa ya tsorata da tsawar da akayi ya tureta ajikinsa yana fad'in,

"Wal'iyazubillah, me kike yi haka?"

"Kabir...."

"Shurtup". Ya faɗa cikin ɓaci rai tare da shigewa gida yana mai jin haushin faruwar hakan, shigewarsa keda wuya ruwan sama ya sake saukowa da ƙarfi kamar da bakin ƙwarya, hakan ya sa tana kuka tabar kofar gidan, tsananin yanda ruwan ke sauka ya saka ko gabanta bata iya gani sai hanya take faman haɗawa har ta isa can bayan wani lungu data ajiye motarta.

Daƙyar ta iya ɗaya hannunta tasa makulli ta buɗe marfin motar ta shiga ciki ta rufe tare da haɗe kanta da sitiyarin motar tana tunanin meye mafita a wajenta yanzu? Sai data kwashe kimanin mintuna biyar ahaka sannan ta yiwa motar key da niyar barin wajen, hasken fitilun motar tane ya hasko mata Kabir a tsaye bakin kofar gidan nasa riƙe da Ummi tana wasa da gashin kansa shi kuma yana kallon motar ta Sha'awanatu dake ƙoƙarin tashi, wani wawan burki ta taka don har motar ta fara tafiya, da gudu ta fito daga cikin motar ta nufi ƙofar gidan tana kukan farin cikin ganin 'yar tata, tunowa da abunda ta yiwa yarinyar ya sa Kabir ya shiga girgiza kai yanaja da baya har ya shige cikin gidan had'e da turo ƙofar ta rufe kafin ta ƙaraso, tana isowa yana rufe ƙofar ta fashe da wani irin kuka tare da bubbuga ƙofar tana kiran sunansa amma fir yaƙi buɗewa, jin yanda take kuka tana dukan ƙofar da ƙarfi ya sashi saurin shigewa can cikin gida gaba ɗaya don kar ƙarar ta firgitar masa da ƴarsa.

_Guys to ya kuka ji salon, zamu iya ci gaba?"

*ALLAH KA JIƘAN IYAYENMU👏😭*

UWA DA ƊAWhere stories live. Discover now