PAGE__10

11 3 0
                                    

Page___10💎

🤱🏻🤱🏾 *UWA DA ƊA...*🤱🏾🤱🏻
💎 _Sai ALLAH_💎

NEW EDITION 2022/2023

_Writting by:_ *_BILLY S FARI💎_*
*TRUE LIFE STORY*

_Akwai Zafafan littafanmu a ƙasa complete ga masu buƙata_
ZO GARE NI N300
FILHUB ₦500
WASU MAZAN ₦300
WAMINAL HUB ₦500
ALBI ₦500

*Ga masu buƙatar a tallata masu hajojarsu cikin karamci, zaku iya tuntuɓarmu ta wannan lambar, 07040402435*
______________________________
Da fara'a kwance akan fuskarta ta tsaya a gabansa, cup ɗin dake hannunta da freshmilk aciki ta miƙa masa ya karɓa, yanka ɗaya ta ɗauko daga cikin fruits ɗin dake ɗaya hannunta a cikin wani ɗan madaidaicin tray ta kaimasa abaki, ba musu ya karɓa ta sake ɗauko wani ta kaimasa abaki tun kafin ya ƙarasa haɗiye wanda ke cikin bakinsa, ganin tana ƙoƙarin sake ɗauko wani ya sashi buɗe baki da niyar yi mata magana ta sake tura masa wani yankan aciki, ɗaga mata hannu ya shiga yi don gaba ɗaya ma tacika masa baki ya kasa yin magana, ganin ba tada niyar ƙyalesa haka ya sashi saurin riƙe mata hannu, "pls Dad". Ta faɗa a shagwaɓe don ta riga data ɗauko wani yankan a hannunta, ba yanda ya iya dole ya sake buɗe bakin ya karɓa, murmushi ta saki tare da ajiye tray ɗin a saman Centre table dake tsakiyar falon, cup ɗin data miƙa masa ta karɓa shima ta kaimasa abaki, sai da taga ya shanye freshmilk ɗin dake ciki tas sannan ta janye cup ɗin daga bakinsa, "Yawwa Dad, Sannu ya jikin naka?" Ta faɗa tana dariya ganin yanda ya matse mata fuska, dariyar shima ya yi kafin yace.

"Alhamdulillah Zee, wato yau ɗure kika yiwa dadyn baki ko? ina Hajiya Mama ɗin taki take ne?" Kafin ya rufe baki ya hango kyakkyawar dattijuwar na saukowa itama daga matattakalar saman, kyakkyawa ce sosai kana gani basai an tambaya ba zaka gano both Dady da Zee jininta ne don suna yanayi da ita sosai, tafi mintuna biyar a tsaye tana kallonsu kafin tafara sauko cike da tausayin ɗan nata, takan tsinci kanta cikin damuwa aduk lokacin data ga Zee na ƙoƙarin yiwa mahaifin nata wasu abubuwan da mahaifiyarsu ne ya kamata tayi masa, tabbas ba kaɗan mutuwa ta yiwa mahaifiyar tasu gaggawa ba alokacin da dukkansu ke buƙatar ta, fatarta kawai ubangiji ALLAH ya jiƙanta da rahama, tayi addu'ar a cikin zuciya tana ƙara sa saukowa daga matattakalar idanuwanta akansu, harara ta makawa Zee kafin ta kalli Dad dake miƙo mata gaisuwa cikin girmamawa, tace "lafiya klw Ƙasim, wato wannan shagwaɓaɓiyar ƴar taka ta hana ka tuna dani sai yanzu ko?"

"Tuna nake yi Hajiya, ina nan tana yimun ɗure yanda kika san wani ƙaramin yaro". Ya ƙare zancen yana zubewa gaba aya ƙasa agabanta ganin ta nemi ɗaya daga cikin kujerun dake falon ta zauna, ɗago hannunta dake faman rawa irin na tsofaffin nan da suka kwana biyu ta ɗora a saman kansa tana faɗin.

"Ba komai Ƙasim ubangiji ALLAH ya yi maka albarka, ai indai Zainabu ce kaɗan daga cikin aikin da zata iya kenan, ko da yake bari nayi shiru, tsakaninku ne ba ruwana kar kuzo ku watsan ƙasa a fuska". Ta yi maganar tana ajiye kyakkyawar sandar da take dafawa irin ta zamani a gefe, turo baki Zee ta yi ganin yanda Dad ya manta da ita a wajen sai ta Hajiya Mama yakeyi, don indai wasar jika da kaka ne, to Hajiya Mama ko gajiya ma bata yi, ta sakewa Zee sosai ta yanda baza ta takura zama da ita ba, haka kuma baza ta ɓoye mata komai ba ko kuma damuwarta, duk da haka kuma wasu lokutan takan ajiye wasar jika da kaka ta taka matsayin uwa a wajensu don hanasu Jin kewar hakan, ko kuma tunananin rashin uwa atattare dasu.

Mere baki Hajiya Mama tayi lokacin da idanuwanta suka sauka akan Zee tana faman cika da batsewa kafin tace, "Oho dai! Ni ina ma nasan kinayi yarinya tunda bakiyi bindiga ba, nice nan da ɗana baki isa hanashi ya saurareni ba". Yanda ta ƙare maganar tana wani murguɗa baki ya sa Zee dariya haɗe da takowa waje ta zauna akan hannun kujerar da take zaune, kanta ta ɗora saman kafaɗar Hajiya Mama tasa hannuwa ta rungumota tana faɗin, "Oh ni Zainabu Abu mai tagwayen suna, to maida wuƙar Hajiya kaka, dama tsokanarki nakeyi, ina ni ina shiga tsakanin UWA DA ƊA, ALLAH ya baki na mai bara".

UWA DA ƊAWhere stories live. Discover now