*AL'AMARIN MU*
*Na*
*MEENAT A ƳANDOMA**Labari ne wanda ban taba tabo irin wannan jigon ba, labari ne daya banbanta da sauran kada in cika ku da labari domin hausawa sun ce gani ya kori ji muje zuwa.*
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
______________________________
*TSOKACI!*
*LITTAFINA NA KUƊI NE AKAN FARASHI 300 ZAKI RURO KATIN WAYA MTN KO KUMA KI TURO TA ACCOUNT AISHA ABUBAKAR 2151366600 U.B.A BANK, DAN ALLAH IDAN BAKI SHIRYA BA KADA KI TABONI🙏🏻*https://www.facebook.com/100089289690624/posts/pfbid0g4v9HS1bQyzKz8hoWpHvMiMGqZYT8euDexn97Z5ixW9F97NFsUB5D5zvhNhEoeAl/?app=fbl
👆🏻👆🏻👆🏻
*DAN ALLAH KU SHIGA CIKIN WANNAN LINK ƊIN KUYI MANA COMMENT DA SHARE**TALLAH*
Albishirnku mata munzo maku da magani na gargajiya wanda zai saukarmaki da ni,ima yaqara maki lfy yawanke miki dattin mara daduk wani sanyi dake damunki,
Ina amare dake shirin yin aure kafin kifara shan komai yakamata kifara da mgnn sanyi domin matuqar bakishaba kayan ni,ima bazasuyi tasiri ajikinkiba,
Ina masu jego gadama tazo,Atafasa asa lipton da sugar da mada asha 2 times Muna katsina muna tura kaya ko ina yankatsina free deliver ne 1500 zaimiki 1month Ku tuntube mu akan wannan number 0903 641 3535 🤸🏻♀️🤸🏻♀️🤸🏻♀️@2023 January
*PAGE 1️⃣&2️⃣*
...Gagarumin hadarin da yayi ma garin ƙawanya ne ya haddasa ma garin matsanancin duhu wanda ko tafin hannunka baka iya gani, lokaci ɗaya iska ta fa ra kaɗawa da ƙarfin alamun ruwan sama yana gaf da saukowa."Manahil, Ridwana, Rizwana."
Wata dajjijuwa dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun falon ta hau kwalama kira.
A tare ƴan matan uku suka rusuna gabanta tare da amsawa.
"Kunci abincin dare"?.
Dattijuwar da kallo ɗaya zaka yi mata ka fuskarci ƴan matan ƴa'ƴanta ne saboda tsananin kamar da suke yi."Aa bamu ci ba."
Suka faɗa a tare.
"Maza ku bace mani da gani ku ɗauki abincin ku ku nufi dakin ku domin hadari na gaf da sakin ruwa maza sai Allah ya kai mu nima kwanciya zanje in yi."
Tana ƙarasa maganar ta afka ɗakin tare da maido ƙyaure.Ƙaramar cikin su me suna Rizwana ce ta fara magana.
"Hmm! Umma kenan daga yau dai ba zaki kuma ganin mu a cikin gidan nan ba domin kuwa mun kusa bar maki gidan sai ki jiƙa ki sha."
Ridwana ce tayi saurin bige mata baki.
"Ke fa baki da hankali, yanzu in Umma taji a tunaninki duk wani shiri namu bai wargaje ba."
"Ki barta domin gaf muke da barin ta cikin gidan nan."
Manahil ta faɗa.A tare suka shige ɗakin domin yanzu ba ta abinci suke ba hankalin su ya kaɗu akan su fara harhaɗa kayansu ko zasu aiwatar da abinda ke cikin zuciyarsu.
Manahil ce ta ɗauki wayarta tayi kira.
"Ku kasance cikin shiri, gamu nan fitowa."
Ƙit ta kashe wayar.
Ruwan da suka ji an balle dashi ne ya basu damar haɗa kayansu cikin wani babban akwati, cikin sanɗa ba tare da sanin mahaifansu ba suka fice daga gidan zuciyar su cike da zallar farin ciki...***
...Mayrasa ne ya fa ra leƙa ɗakin mahaifan su cikin sanɗa domin tun safkowar ruwan saman ya ji su shuru, cike da farin ciki ya dawo ɗakin su.
"Ya sunyi barcin ne"?.
Ra'id ya tambaya.
"Ni fa a matse nike mu fice daga gidan nan domin banga abinda zai hana mu barin gidan nan ba."
Cewar Rashdan."Ku fa baku da hankali, yanzu in banda ana ruwa wannan surutun kaɗai ya isa ya tayar dasu Hajiya, yanzu abinda za'ayi shine maza kumu harkaɗa mubar gidan nan tun kafin a gama ruwa duk wani shiri namu ya lalace."
Maysara ya faɗa tare da janyo katon akwatin da suka shirya kayan su ciki.Cikin sanɗa suka fice daga gidan duk da ruwan saman da ake sheƙawa amma ko a jikinsu basu jin shi domin idonsu ya rufe burinsu ɗaya shine su gansu inda suka shirya.
Tafiya suke cikin ruwan ga matsanancin duhun daya mamaye garin, ba zato ba tsammani sai ganin mutum suka yi a gabansu, Maysara ne yayi saurin ja da baya domin sai da ya tsoratar dasu ba kaɗan ba.
"Ƴan samari ina zaku je cikin daren nan, baku tsoron dare kuka fito ku kaɗai"?.
Mutumin da basu san daga inda yake ba suka ji ya faɗa.
"Ba mu gane ina zamu ba, shin kana da damuwa da inda zamu ko kasan mi ya fito damu ne"?.
Ra'id ya faɗa yana me yarfe ruwan dake wanke ma shi fuska.
"Kai kama tsaya bashi amsa har yake neman rena maka wayo daga ganin mutum kawai sai ya wani tarbe mu da wasu tambayoyin renin wayo to me ye damuwarshi damu."
Rashdan ya faɗa.
"Zaku rabu dashi ku wuce mu tafi ko sai na yi gaba na barku nan."
Cewar Maysara yana me jan ƙaton akwatin shi yayi gaba, su ma suka mara ma shi baya.
"Brox nifa wannan Guy ɗin ya tsorata ni cikin daren nan me ya fito dashi da har zai tarbe mu yana mana wannan tambayoyin haka"?.
Ra'id ya faɗa.
"Ni fa har yanzu gabana faɗuwa yake domin da ƙyar mutumin nan in ba Jinnu bane, ni fa sai na juya inga in biye yake damu."
Ra'id ya faɗa tare da juyawa, amma mi sai gani suka yi wurin wayam babu mutumin.Cike da firgici suka fara kallon junansu nan ido ya raina fata domin wannan mutumin sun sake yarda ba Mutum bane.
Da hanzari suka bar wurin suna janye da ƙaton akwatinsu, har suka ƙarasa wurin su Manahil.
"Amma fa kun shanyamu ga ruwa sai dukan mu yake, Haka muka yi daku"?.
Manahil ta ƙarasa maganar tare da hararar Maysara.
"Bari kawai Beb da wani Guy muka haɗu a hanya ya nemi ya raina mana wayo yana neman bata mana lokaci, wai me ya Fiddo mu cikin daren nan."
Manahil kuwa Saurin kallon yan uwanta tayi domin su ma sun haɗu da mutumin nan.
"Muma haka ya tsayar damu har yana faɗa mana mun jima da tsoma kan mu cikin bala'i da musifa tunda har muka ɗaura aniyar tafiyar nan."
"Ai badan Yaya ta hana ni ba da sai na wanka ma bawan Allah-n nan tafi sai ya gane shine yake cikin musiba ba mu ba, yasan abinda ya koro Zomo daga ruwa ya faɗa wuta ba karami bane."
Ridwana ta faɗa.
"Yanzu dai mu ajiye wannan maganar muyi gaggawar barin unguwar nan tun kafin iyayen mu su farga bamu cikin gidajen mu."
Maysara ya faɗa tare da yin gaba.A cikin ruwan haka suka taka har zuwa bakin hanya jikinsu duk ya jiƙe Ridwana har ta fara kyarma domin bata san sanyi ko alama sai kuma yau gata ita ce cikin ruwa yayi mata Mugun duka.
Suna nan suna shawarwarin yadda zasu samu abun hawa sai dai tsayuwar wata tartsetsiyar mota baƙa wuluk suka gani gabansu.Sauke glas ɗin motar akayi.
"Ƴan samari ina zaku je cikin daren nan ga kuma ruwa yana ta dukan ku, in babu damuwa ku shigo ciki mu rage maku hanya."
Shuru suka yi suka kallon mutumin domin su har ga Allah basu san lokacin da motar ta tsaya a gabansu ba sai dai ganin ta suka yi tsaye a inda suke.Ba tare da wani dogon tunani ba suka afka kai cikin motar tare da saka jikkunan su domin idanunsu sun rufe burinsu ɗaya shine suga sun bar garin nan.
Mace da namiji ne a gaban motar namiji yana jan motar sai mace a gefenshi.
"Sannunku ƴan matasa ga sanyi ga shi kuma duk kun jiƙe da ruwa, gari zamu bari fatan kuma tafiyar duk ɗaya ce"?.
"Eh gari zamu bari."
Maysara ya faɗa.""Manahil kai na juya mani yake."
Rizwana ta faɗa.
"Nima kai na bibbiyu nike ganin ku."
Cewar Ridwana.
Kafin Manahil ta samu damar magana ƙannenta dake kusa da ita tuni sun sulale, kafin tayi wani yunƙuri ji tayi idanunta sun rufe.Su Maysara ma haka ce ta kasance da su duk sun suma, mutanen gaban motar ne suka babbake da wata irin mahaukaciyar dariya.
"Dawa yayi nama, tsuntsaye daga sama gasassu."
"Hhh yau fa mutum shida muka samu a tare wa ya kai mu sa'a duk yau."
"Ai raina fal da farin ciki kuma da ganin su duk matasa ne."
Mutumin gaban motar ya faɗa tare da jan motar da ƙarfin tsiya, tamkar walƙiya haka motar ta bace..*KADA KU MANTA NA KUƊI NE BA SAI NA CIKA KU DA SURUTU BA DOMIN NA YARDA DA ALƘALAMINA, TAFIYAR TA DABAN CE DOMIN DUK LITATTAFAINA KO WANE SALON SHI DABAN, ZAKU IYA TUNTUBA TA A WANNAN NUMBER 08133562798*
*MEENART...............✍🏽*
08133562798