matter's of the heart

1.2K 50 4
                                    

Rai ɓace kamar Mahaukaci! ya ce "Wanne irin addini ne wannan for God sake? Komai ba kyau" ta fizge hannunta, kau! Ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, addinina ya fi ƙarfin cin mutuncinka sai a yanka wuyan wanda duk zai aibata Musulunci" idanun Abraham sukai jawur ya ce "Shi addinin ya haramta auren macen da ta girmeka kenan? Shekaruna 20 mene abun yarinta a jikina? Me ya sa kika raina ni? Kawai saboda ni yaro ne, saboda kin girme ni da shekaru goma sha biyar?"
  "Kai yaro ne"
"Zan wadata ki da komai JEE, don kin rai ne ni a lokacin da na rasa iyayena ba shi ke nuna ba zan iya zaman aure dake ba, ina soyayyar da kika nuna mini ina yaro? Okay fine, i have a solution! Your father doesn't like me kawai mu yi auren Choci ko kuma wallahi mu haifi ƴa ƴan banza kuma shegu, ko kuma na wulaƙanta addinin Musuluncin naku...

MIJIN MALAMAWhere stories live. Discover now