Page 20

74 5 0
                                    

_20_

*Nuratu*

Tafiyar da bata fi ta awa guda da rabi bane ya kawo su Damaturu, daga tasha suka hau Napep bayan Inna ta fada masa unguwar da zasu je(Gwange), cikin kankanin lokaci suka iso,sun samu tarba mai kyau daga mazauna gidan, tin daga kan Inna har Mama da ta kasancewa abokiyar zaman ta(Nan gidan su marigayiya Khadija ne, wacce zata auri Fawzan Allah bai yi ba).

Nuratu kuwa take ta saje cikin kawayen Amina Amarya, da kuma Zulaihat kasancewan ta mai saurin sabo da mutum idan ta so. Suna gidan makotan su inda anan Amarya ta tare da bataliyar ta.

"Wai nikam Amina baza ki kira Ummul tayi sauri tazo ta miki lallen nan da tasa muka kwaba sa tin asuba ba sai lokaci ya kure mana? Kinsan fa anjima mai Dj zasu zo ko kuwa so kike har suzo su ba'a cire lallen ba?"
Fadar daya daga cikin kawayen Amarya mai suna Maryam.

"To yaya kike so nayi Maryam ki duba fa ki gani tin dazu Kiran ta nake a waya bata dauka, gashi Zulaihat kuma nace ta tafi gidan su suzo tare amma tace baza ta je ba sabida abinda ya hada su jiya,sannan gashi a cikin ku dik wacce nace ma yaje yazo da ita kun ki yaya kuke so nayi ne? " Amina ta kare maganar cike da damuwa.

Nuratu dake jin tattaunawar su kuwa ta tari numfashin su kamin kowa yace komai tace,"To idan babu damuwa ku kawo min tray da gum sai na miki lallen mana."

Daya daga cikin kawayen mai suna Ummie ta maida ma Nuratu da "Amma dai baki da hankali ke kam, ce miki akayi lallen amaryar wasan yara ne da kawai mutane suna zance zaki wani ce a kawo miki zakiyi salon kije ki dagula mata kafa da hannu?"

Da yake itama Nuratun ba wani hakuri bane da ita harara ta watsa ma Ummien tace "To ke kuma uwar yan shishshigi wa ya sako bakinki cikin zancen? Ko tinda kika shigo nan gurin na kasa dake a zance na?"

Ummie ba tace komai ba sabida toshe mata baki da Maryam tayi tare rokon kar ta sake cewa komai, sannan ta dubi Nuratu tace "Kema dan Allah kiyi hakuri karki sake cewa komai ba girman ku bane."
Kwafa kawai Nuratu tayi ba tare da tace uffan ba.

Amina dake cike da takaicin rashin daukan wayar ta da Ummul tayi, gashi kuma ba wata mai lallen ta sani da zata zo tayi mata a kurarren lokacin nan ba kawai tayi shahadar fadin Nuratun tazo tayi mata tinda ba sanin ta iya lallen tayi ba ko kuma bata iya ba tace "Nuratu kawai mu zauna kimin babu damuwa ni na yarda."

Dayawa yan matan dake gurin wautan Amina suke gani na Mika ma wacce baki san ta iya lalle ko bata iya ba kafarta a matsayin ta na amarya tayi mata lalle, sai kuma suka soma sakin baki da hanci suna kallon lallen cike da birgewa a sanda ta gama jera mata gam din kafa guda.

Basu tashi tsinkewa da lamarin ba sai da Amina ta cire lallen kafa da hannu wanda a lokacin wajen karfe biyu na rana tayi, kowa sai santun lallen yake cike da yabawa hatta Ummie da aka so yin fada da ita, fadi suke ashe haka ta iya lalle ai harma tafi Ummul din iyawa.
Ita da kanta ta sake ce ma Amina ta aika a siyo dayis, ba tare da bata lokaci ba kuwa aka siyo ta zauna ta tsara mata a hannayen ta guda biyu da yayi matikar kyau ba kadan ba.
Ai kuwa saida tayi ma Maryam, Ummie da Zulaihat suma a hannu dai dai sai yabawa suke.

Sai a lokacin Nuratu ta shiga gidan su Amina ta wuce dakin Mama inda anan Innar su Aminan ta sauki yan uwanta da suka zo daga potiskum din ciki kuwa harda Inna Zulai.

"Yar nan ina kuka shige ne tin safe ban saki a idanuna ba sai yanxu?" Inji Inna Zulai dake kallon Nuratu.

"Inna lalle tayi ma Amarya da kawayen ta sai yanzu muka gama wallahi dik na gaji baki ji yanda bayana ke ciwo ba kaman ya balle."

"Ai kuwa dole kiyi ciwon baya tinda ba ma mutum daya kikayi ma ba sannu kinji ko? Yanzu kizo ki kwanta na shafa miki man zafi a bayan sai ki huta"

Bata Musa ba kuwa tazo tayi kwanciyar ta a gaban Inna bayan ta cire Hijab din dake jikinta ta dage rigar ta Inna ta soma mulka mata man zafin da take yawo dashi sabida sha'anin ta ciwon kafa bata rabuwa dashi.
Mama ce ta shigo da sallama ta tare da Zama suka sake Sabuwar gaisuwa da Inna Nuratu ma ta gaida ta.

"Wannan diyar taki akoi shagaba kai kace sun sha nono guda da marigayiya ki duba kiga yanda ta wani kwanta a na shafa mata mai a baya." Fadan Mama dake dariyar karfin halin tuno mata Khadija da ta maye mata gurbin Maimuna da har yau bata san inda take ba.

Cikin nata dariyar Inna ta bata ansa da fadin "Wallahi gajiya tayi kinji Wai lalle tayi ma amarya, bayan ita kuna harda Karin mutum uku shine nace ta kwanta na mulke mata bayan da man zafi."

"Allah sarki, hakan na da kyau." Inji Mama.

"Rayuwa kenan da bata da tabbas, mudai babu abinda zamu ce da Wayannan la'anannun nutanen dake fakewa a rigar musulunci suna zalintar bayin Allah da basu ji ba, basu gani ba, sai Allah ya isa! Ace kuzo har muhallin mutum Cikakken musulmi a kan idanun iyayensu da yan uwansu kuyi musu kisan gilla sabida rashin imani?"
Fadar Inna cike da jimamin tabon da yan Boko haram suka barma ahalin wannan gida.

Cikin dauriya Mama tace  "Kedai ki bari kawai Yaya Zulai, kaman yanda kika ce ne wallahi mukam Allah ya isa tsakanin mu da su baza mu yafe musu zalincin da suka mana ba, ace har yara biyu suka kashe mana a rana daya, banda bakin da suka zo mana yan uwan su Mallam daga Gashu'a?"

Sai kuma hirar tasu ta karkata izuwa ga zancen Baban su Aminan da har yau shiru Babu labarinsa, tun Nuratu na sauraron hirar tasu har bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari aka daura aure ranar Juma'a, da dare kuma aka kai amarya gidan ta dake Unguwar White House kusa da Red bricks dake kan hanyar maiduguri. Tare da su Nuratu akayi kwanan gidan amarya, ranar asabar da dare Misalin karfe tara Nuratu da taji shirun yan rakiyar ango basu zo ba tayi tayi dasu Ummie su zo su tafiyar su amma suka ki, suka ce sai angwaye sun zo sun basu kudin siyan baki, hakan yasa tayi zuciya ta kada kanta zuwa bakin kwalta  a ranta sai masifa take ita daya tana jin dama tun da yamma tayi tafiyarta.

Tayi tsayuwar wajen minti 20 amma bata samu taxi ba, wanda hakan yasa ta fara yin hanyar cikin gari da kafarta kaman zata tashi sama a zuciyar ta kuwa sai tsinema abokan angwaye da suka ki zuwa da wuri take, gashi kuma Inna ta gargade ta kan kar ta kuskura tayi dare, hakan ne ma yasa ta kin jiran abokan ango kar laifin yayi mata yawa.
Horn din Mota da taji a bayan ta ne yasa ta juyowa a tsorace da dama a tsoracen take tafiyar tuntuni.

*FAWZAN*

Yau asabar da Misalin karfe 6 na yamma ya kamo hanyar Damaturu bayan ya karbi izini daga wajen ogan su da kyar kan zaije ya duba mahaifiyar sa, an kuma bashi kwana guda ranar lahadi ya juyo da yamma cikin sirri babu wanda ya sani tinda babu hakan a dokar aikinsu. Motan wani abokinsa soja da shi Dan maiduguri ya ara bayan ya cika da man da zai kaisa ya dawo dashi ya sanya kaya personal ba kaki ba ya kamo hanya, ya tsaya wajen wani tsohon mai gidan sa a Benshak shiyasa bai shigo Damaturu ba sai wajen tara da wani abu na dare.

Tin daga nesa yake hango matashiyar Budurwa dake ta faman zafga sauri kai kace kafafun ta zasu tsinke, haka nan ya tsinci zuciyarsa da son rage mata hanya gudun kar ta hadu da wa yanda zasu iya cutar ta duba da cewa hanyar bai shiga cikin gari sosai ba.
Horn ya danna mata yaga ta juyo a hanzarce da yasa shi dallare mata fuska da wutan gaban motar sabida ya kare mata kallo.

Comment
Vote
Share fisabillillah

*OUM MUMTAZ✍️*



CAPTAIN FAWZAN!Where stories live. Discover now