2

270 10 1
                                    

💧💧 *ƘALUBALEN RAYUWA.!*

*HASKE WRITER'S ASSO.*

    *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


_Gaba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga *AUNTY ZAINAB AHMED*  da Kuma *AUNTY ZAINAB ABUBAKAR KOTORKOSHI* Kun san dai yadda na ke son sunan Zainabu? To ga ire iren dalilin nan, Alherin Allah ya kai maku a duk inda kuke._

_Ina kike ƙawata, aminiyata, tagwayen Feedohm, Allah ya tsare mani ke, ya bar ki da baban mubee, ya cigaba da rufa miki asiri duniya da lahira._

_Ba zan manta da ke ba, ƙawar Alheri, NAFEESA MUHAMMAD SULE, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan ƙwana._

*002*

Wata shaƙa da Ya Abba ya mata yana tambayar "Uban me yasa kika ɗaukar mata abinci?" Ya sa na dawo daga duniyar tunanin da na cilla.

Da sauri na ɓanɓareta daga hannun shi ina faɗin "Ya zata yi? Yunwa take ji, Dan Allah ka ƙyale ta."

"In ƙyaleta ta saci abinci ƴar marasa mutuncin can.?

Na ɗago rinannun idanuna na ƙura mashi ido, a tausashe na ce "Sata ta yi?"

"Eh, duk abinda ba naka bane ka taɓa sata ce..." Ya bani amsa kamar zai dake ni nima.

Na maida kaina ƙasa, tare da furzar da zazzafar iska daga bakina, har ga Allah a gare ni Ma'u ba sata ta yi ba, ko da gaba ɗaya duniya zata kalle ta a matsayin ɓarauniya, sai dai ban isa na faɗi haka gaban ta ba, sabida yarinya ce, gaba zata iya ƙarawa, don haka na saka murmushin yaƙe na ce "Ya Mu'allim ya hukunta a haka? Bai isa ba?"

Ya maka mana harara ya miƙe ya je ya ɗauro alwala, sannan ya fice ba tare da ya kalli kuɗin da nake nuna mashi ba, yana fita na bawa Ma'u 1000 na ce ta amso mana taliya leda ɗaya da manja, ta washe baki bayan ta karɓa tana faɗin "Yaya har da kifi?"

"Kifi kike so?"

Sai na ga ta sunne kai ƙasa tana faɗin "Uhm Uhm, bamu da Abba, kifi na masu Abba ne..."

"Muna da Allah..." Na bata amsa tare da shafar kanta ina jefa mata murmushin da na san zai saka mata natsuwa.

"Allah ya bamu..."

Na amsa da "Amin..."

Ta wuce tana tsalle, har ta kai bakin ƙofa na ƙwala mata kira, ta dawo da baya da baya, na ce "Ki sawo kan kifin na 100 mu jefa a ciki."

Ta kurma ihun farin ciki, ta bazaza a guje tana dariya, yayin da na saki murmushi, ina tausaya mata, yarinya ce ƙarama amma ta ɗauki rayuwar a yadda ta zo mata, wani sa'in har mamaki na ke da sai ta ƙwashe sati bata furta Maama ba! Amma Abba kullum yana cikin kalaman ta, shin ko itama ta fahimci ta rasa shi har abada! Ita kam Maama mu ne ta rasa har abada...

Kamar yadda ta fita cikin farin ciki, a tunanina zata dawo cikin farin ciki, amma sai na ga akasin haka, ta shigo tana jan majina "Lafiya?"

"Husna ce da ƙannen ta suka min ihun ɓarauniyar abinci."Ta bani amsa tana jan majina.

Wani iri na ji a zuciyata, a hankali na maimaita "Ɓarauniya kuma?"

"Uhm.."

Ban ji daɗi ba sam, amma banda yadda zan yi, don haka na ce "Kinga gobe ba ra ki ƙara ɗaukar na wani ba." Na amshi taliyar na wuce ina jin wani ɗaci ɗaci a maƙoshina.

********************

  Cikin hanzari na ƙwaɗawa Ma'u kabeji ta ci ta tafi makaranta, sannan na juya gun Yaya Abba da ke shan kiɗa ina faɗin "Bawan Allah ba zaka samu ƙuli ba yau, sai dai na zuba maka gishiri ka ci."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 21, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƘALUBALEN RAYUWA Where stories live. Discover now