💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..**Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*
*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)Bʏ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..**From the writer of:*
-ƘADDARA KO SAKACI?
-RAYUWAR WANI
-ƳAR GARUWA
-BAMBANCIN AL'ADU
-INA MAFITA
-ZAƁIN WA ZAN BI?
-WANI AL'AMARIN
-ALƘAWARIN JINI
-ƊAN MACE
- IFZAA
-MAKTOUB
-MANAR
-IN-LAWS
-KALLO YA KOMA SAMA
-CIWO A JIKIN WANI
-DAUƊAR GORA 1,2 & 3
*AND NOW*
-WAZEER07
#Interpolated
Yammaci ne me daɗi dake bada wani irin sanyayyan yanayi,ko da yake duk inda unguwar masu kuɗi yake akwai yawaitar shuke²,wanda duk safiya da kuma yammaci za ka samu yanayin gurin yai daɗi,ni'imtacciyar iska na kaɗawa sosai. Mugun gudun da motar wacce ta fito babban get ɗin gidan,shi ne yasa matasan samarin da suke jugging cikin line sanye da train suite juyawa suka bita da kallo,a hankali ɗaya ya ɗan yi murmushi yace "Hjy *MUNIBA* kenan,ko ina take shirin zuwa,da yasa take irin gudun nan haka?" Ba tare da damuwa ba ɗayan ya ɗan taɓe baki kafin ya juya yaci gaba da abunda ke gabansa,ta mirror ɗin motar kyakkyawar budurwar ta ɗaga kyawawan roundish almond eyes ɗinta masu jan hankali da haske ta bisu da kallo,daga yanda suka tsaya ta fahimci maganarta suke,a hankali tai ɗan murmushi kafin ta ci gaba da driven ɗinta kamar mai shirin tashi sama,fara ce tas duk da a zaune take bazai wuyar gane doguwa ce ba,kamilalliyar fuskarta ma'abociyar fara'a na ɗauke da dogon hanci da ɗan thin round lips,a tsarin zubin halittar jiki kuwa,Allah bai yita irin masu girman jiki nan ba,da kyakkyawan kallo ɗaya ya wadatar da me kallonta cewar,duk inda ta fito ba ta rasa nasaba da jinin asalin Fulani gaba da baya. Duk inda kake neman kyakkyawa,ka sameta tabbas ta kai koma ace ta zarta,domin irin matan nan ne da ake kira da full option,idan nace full option ina nufin ta ɓangaren kyau/kyawawan halaye,uwa uba kuma cikakkiyar tarbiyya,nasaba da ilimin addini. Muniba kenan kamar yanda samarin suka kirata da shi,asalin mahaifanta dukansu uwa da uba,haifaffun cikin tsakiyar birni ne a nan garin Kano,ƴar gata ce a gurin iyayenta ta gaban kwatance. Sunan mahaifinta Dr Abbas Bashir Mijinyawa,haifaffen ƙaramar hukumar Dala ne cikin unguwar Ƙoƙi,asalin gidansu matan babansu Malam Basiru biyu,Inna Rahila itace uwar gida,aurensu tun na sakun lalle ne,yaran Inna Rahila a gidan 4,3 daga ciki dukansu maza ne,ɗaya ce kawai mace me suna Talatu kuma ta girmewa Abbas da shekaru 7,tun daga kanta Inna Rahila bata sake haihuwa ba,daga baya²n haihuwarta sannan Malam Basiru ya ƙara aure,ya auri mahaifiyarsu me suna Maryam,suna kiranta Gwaggo Mairamu,mahaifiyarsu ta kasance kyakkyawar bafulatanar daji,babu jimawa da shigarta gidan ta haifesu su tak,Abbas shi ne babba,sai ƙaninsa dake bi masa Sulaiman,a gurin haihuwarsa Allah yaiwa Gwaggo Mairamu rasuwa ba tare da ta san abunda ta haifa ba,duk wanda ya san kyaun halitta da halin Gwaggo Mairamu,ya kalli Abbas da Sulaiman zai tabbatar ƴaƴanta ne,domin babu abunda basu ɗauko ba na daga kyaunta da sanyin halinta,har ta rasu bata taɓa tankawa Inna Rahila ba,duk masifar da za tazo tayi mata kuwa,kou da kanta za tazo tana sababi,hakan bazai sa ta taɓa ɗaga kai ta kalleta ba,da yawan lokacima sai dai ta bata haƙuri,daga haka za ta bar gurin tana faɗin "Allah ya huci zuciyarki Yaya,duniyar nanfa ba matabbata bace,idan yau mune gobe bamu bane.." Bayan mutuwar Gwaggo Mairamu,danginta sun so karɓar yaranta,amma sai Malam Basiru ya nuna zai riƙe ƴaƴansa,a cewarsa ya fiso yaransa su tashi a gabansa duka,idan akace an rabasu suna wani guri daban da inda ƴan uwansu suke zumuncinsu zai lalace,haka dangi suka haƙura suka barsu hannun mahaifinsu,shekaru 10 tsakani da rasuwar Gwaggo Mairamu,Allah ya karɓi ran Malam Basiru,kafin rasuwarsa haka ya bar wasiyya akan Inna Rahila ta haɗa yaran da nata dana Mairamu ta riƙe,ta kula masa da marayun ƴaƴansa kamar yanda za ta kula da nata,tai na'am tana kuka,tunda Malam Basiru ya kwanta dama,yanayin rayuwa kasancewar yaranta duka babu wanda yai karatun boko sai kasuwanci,ganin Allah ya ɗaga mata nata ƴaƴan yasa ta zubar da Abbas da ƙaninsa Sulaiman,a hankali zamansu a gidan ya sauya,a da ganin idonsa yakansa Inna Rahila nuna musu so,amma tunda ya bar duniya kullum suna cikin wahala da azabtarwa,da daɗi da babu haka suka rayu,wahalhalun yau daban dana gobe,wannan dalilin yasa Abbas dagewa yai karatu,bisa tallafawar dangin mahaifiyarsu,cikin hukuncin Allah haka shi da ƙaninsa suka fita zakka a gidan,har zuwa lokacin da ya fara aiki a matsayin likita,cikin ƙanƙanin lokaci da kama aikinsa Allah ya ɗaukakashi,kafin kace me sunansa ya kai inda bai taɓa zato ba,a yanzu haka da fara aikinsa ya samu shekaru sama da 30,kuma ba'a dena damawa da shi ba,ƙwararren likita ne da ake ji da shi a garin Kano,sannan shi ne amintaccen likitan gidan gwamnatin jihar,tare da duk wani babban me ji da kansa,yanzu haka kuma shi ne Kwamishinan lafiya (commissioner for health) na garin Kano. Dr. Mijinyawa shi ne sunan da kowa ya sanshi da shi yara da manya tun kafin ai masa muƙami a gwamnati ya zama commissioner,idan sanin makamar aiki ne,sunanshi a kaf cikin Kano zai fara zuwa a lambar farko,ya yi aiki a asibitoci da dama,kamar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH),Muhammad Abdullahi Wase (Nassarawa hospital),da kuma asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital (MMSH). Matarshi ɗaya tak tun auren saurayi da budurwa me suna Aminatu,haifaffiyar ƙaramar hukumar tsakiyar birni ce (Municipal),an haifeta a nan unguwar Kankarofi,su 5 ne a gurin iyayensu,Yaa Taheer shi ne babba,sai Muhammad Taqiuddeen,Hashim,sannan ita,sai autarsu Wahidah,iyayensu ba wasu masu kuɗi bane,amma sun taso cikin gata da tarbiyya,mahaifinsu Malam Imraana mutum ne dake son ganin yaransa sun yi karatun zamani,shi yasa mazansu da matansu duka ya tsaya tsayin daka wajen inganta rayuwarsu,ta yi karatun firamare (primary) a Gidan Makama Special Primary School,daga nan ta tafi makarantar gaba da firamare (secondary) a makarantar kwana ta ƴan mata wato Shekara,sannan tayi karatun jami'a a makarantar Ahmadu Bello dake Zaria (ABU),bayan kammala digiri (degree) ɗinta na farko a ɓangaren abunda ya shafi tattalin arzikin ƙasa (Economics),tana matakin digiri ɗinta na biyu Allah ya haɗata da Dr Abbas Mijinyawa wanda ya kaisu ga yin aure,tana ɗakinta tai Masters,inda ta karanci International Economics a jami'ar Bayero,bayan nan ta kama aiki a matsayin Malamar makaranta a jami'ar,a lokaci ɗaya kuma tana karatun Doctoral degree ɗinta,har zuwa matakin da take a yanzu na Dean,duka a jami'ar ta Bayero dake Kano. Suna da yaransu biyu tak,Imraan wanda yaci sunan mahaifinta shi ne babba,suna kiranshi Khalifa,sai Muniba data ci sunan mahaifiyar Dr Abbas Maryam itace auta. Dr Sulaiman Mijinyawa,ma'ana ƙani a gurin Dr Abbas Mijinyawa,shima Likita ne kamar yayansa,ya yi aiki a asibitin Nassarawa,a yanzu haka shi ke kula da babban hospital ɗinsu da suka buɗe da wasu harkokin kasuwancinsu,kusan duk wasu harkokin yayansa shi ne akai,shi yake wakiltarsa akan duk wasu harkoki da suka shafi dukiya,a yanzu haka suna da yara samari da suke tallafa musu,yana da mata ɗaya kamar yayansa,tsayin lokaci ya so sake yin aure Allah bai nufa,yaranshi 3,babban ɗansa namiji Bashir wanda suje kira Mubasshir,sai Khalidah dake bi masa,sannan auta Maryam da suke kira Baniynah,alhmdllh basu da yawa,sai ƴan uba da suke da su,wanda basu damu da sanin yaya suke ba,sai tarin hassada akan ɗaukakar da Allah yai musu,suna zaune cikin farin ciki da rufin asirin Ubangiji,tare da zumunci mai ƙarfin gaske,duk inda Dr Abbas Mijinyawa zaisa ƙafarsa,idan ka duba kusa da shi ƙaninsa ne Dr Sulaiman Mijinyawa,shi ne PA ɗinsa,shi ne best friend nasa,shi ne special advisor ɗinsa,a duniya ƙaninsa shi ne komai nasa. (Wannan kenan)..
YOU ARE READING
WAZEER!
Romance...Me zai sa mahaifi ya aure budurwar ɗansa? Son zuciya? Son kai? Kou kuma budurwar zuciya? #Follow this fairy tale of love,jealousy and ultimate betrayal that leads someone to the lost end..