GIDAN RINA!!
Na
Jeeddah Aliyu*Bismillahim rahamanin rahim*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki sarki ina gode masa da ya bani ikon rubuta wannan littafi._
_Kuma ina neman gafararsa, haka kuma ina neman taimakonsa, ina neman tsarin Allah daga sharri mutum da Aljan, Allah yak'arawa Annabi Muhammad{S.A.W} daraja yasa muna ciki wanda zai ceta ranar alk'iyama Amin.__Gargadi:- Ban yarda wani ko wata ya juya min labari ta kowace siga batare da izzini na ba Saboda haka akiyaye._
*FREE PAGE*
001.
*Abuja*
*Maitama*
*10:47am*Hajiya Zaituna tana zaune akan ɗaya daga cikin manyan-manyan Royal chairs da suka yi matuƙar ƙawata mata tankamemen sitting room ɗinta, mai kama da na matar president saboda girma da ƙawatuwarshi.
Kyakyawa macce mai cikar halitta fara sol da ita kallo ɗaya za kayi mata ka gane buzuwa ce. shekaru ta na haihuwa ba zasu zarce hamsi da biyu zuwa da uku ba.
Jikinta sanye da shadda kamfala orange in colour irin na ƙasar Mali, sai kyali da daukar ido take. Yayin da wuyanta da tsintsiyar hannunta haɗe da yatsunta sun sha ado na gold ƙirar Dubai.
Duk da kasancewar shekaruta sun ja hakan bai hanata fente fuskarta da makeup.
Duk da wannan uban ado da ta caɓa bai hanawa fuskarta bayyanar da tsan-tsan damuwar da take ciki.
jin take tamkar ta daura hannu aka ta kurma ihu azahirin gaskiya yau ta kasance mata ranar mafi muni a rayuwarta, rana ce da zata ruguza mata burinta na tsawon shekaru masu yawan gaske.
Ba ko shakka wannan ita ce the most terrible day in her life.
Wani kafirin gwaron numfashi ta sauke, kamar wacce tayi gudu ceton rai, babban tashin hankalinta bai wuce aure da mijinta Alhaji Muhammad Ardo yakeso ɗanta Aliyu ya yi, duk duniya ba abinda ta tsana sama da Aliyu ya yi aure abinda bata fatan faruwarsa.
Duk da tasan ɗan nata yafi ta tsanar aure ko kalmarsa bayaso a anbata masa, shiyasa duk lokaci da ta tuna da hakan sai taji hankalinta ya kwanta.
Sautin muryar mijinta ta tsikaya yana kiran sunanta zuciyarta ta buga very fast babu sharri ta miƙe tsaye har tana haɗawa da dafe ƙirji.
"Alhaji har kafito?
Tafaɗa cikin rawar murya.
"Eh! nafito kinsan jirgin 12 noon za mu bi, kuma sai mu biya ta gidan Alhaji Yusuf saboda tare, za mu tafi dashi da Suraj da yake shi Suraj nayi waya da shi ya ce mu haɗu a Airport.
''Ina Sultan ko har yanzu bai gadi fitowa ba so yake sai ya ɓata mana lokaci.
Ajiyar zuciya ta sauke dake cike da fargaba ta ce "Alhaji akwai matsala fa.
"matsala kuma?
Yafad'a yana mata kallon mamaki.
"Eh...Al...ha..ji..Sultan baya gidanan nima da asuba naga text ɗinshi ya ce ya wuce Scotland.
Ashe ya yi booking jirgin da asuba suka ɗaga....
Ke! Dakata.
Alhaji ya daka mata tsawa azarane ta ja da baya.
Cike da zallan masifa ya hayyaƙo mata "har ni Sultan yakeso ya kunyata, ni yakeso ya mayar ƙaramin mutum to wallahi bai isa ba.
Wannan shine karo na hudu ina nema masa aure yana ruguza shi, da izinin ubangiji a wannan karo aure nan ba zai lalace ba ko don albarkacin addu'o'i da ake min akansa. Na rasa meke damu shi da ya tsani raya sunnah ma'aki{s.a.w}
Amma ba laifinsa bane duk abinda yake yi agidanan ke ce ki ka daure masa gindi, daga ke har shi a sannu zan yi maganinku, tafiya Yola nema masa aure babu fashi, ba Scotland ya tafi ba in iya ya tafi birnin sin duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya awurina.
Na tabbata ba wani scotland da yatafi ina barin garinan zai dawo cikin gidanan, ki faɗa masa ya gama karyayyakinsa ga baki ɗaya za mu haɗu ni da shi, sai naci ubanshi ba dai ni ya wulaƙanta ba.
Cikin kwantarda murya irin na macce da ta kware da kissa da kisisina Hajiya Zaituna ta ce
"Ka yi haƙuri Alhaji ka bi komai a hankali, ni sai nake gani kamar akwai matsalar da ta ke hana shi aure...
Ke baƙar munafuka al-mura rufe min baki, har ni za ki kawowa canfe-canfenku na mata mtswww..!
Ya marasa magana haɗe da jan dogon tsaki, gani za ta ɓata masa lokaci yasa bai ƙara tamka mata ba ya nufi ƙofar fita yana mai cigaba da ɓamɓami faɗa kamar ya ari bakin kare.
Tana gani ya fita ta ɗauki wayarta tai dialling digit ɗin Sultan ta kara akunnenta "Hello....yarona nasan kana cikin garinan na roƙe ka, ka dawo gida inaso magana da kai.
Ta ƙarasa magana kamar za tai kuka
Zamanta ke da wuya girls ɗinta su uku suka shigo kowacce da shigar English dress, su yi matukar kyau da ka kalle su kasan ita ce ta haife su. Saboda tsanani kama da suke da ita.
Teema ce ta fara magana cikin sanyi muryarta "momma ki ji tsoron ALLAH ki tuna za ki mutu za ki kuma riske abinda ki ka aikata yana jiranki a kabarinki. Ni ban taɓa gani uwa irin ki ba Ya Aliyu dai ɗanki ne da ki ka haifa da cikinki momma, I don't know the reason why da bakyaso ya yi aure kullum ƙara masa tsoron mata da tsanarsu ki ke yi narasa miye ribarki na yin hakan idan ma wata huɗubar sheɗan ce ki ke bi sai kai ki ya baro.
Har Teema ta dasa aya azanceta momma tana kallonta.
Girgiza kai momma ta yi gami da cewa "ALLAH yaye miki wannan ciwo Teema, kina dauke da wannan mummunar lalura wa zai aure ki.
Turo baki Teema tayi tana firfito da idanuwanta, "enough momma ya kamata zuwa yanzu kin daina danganta ni da ciwon hauka ni lafiyata ƙalau bani dauke da kowacce irin cuta. Kawai dai ina ƙara tunatarda ke ki dinga tunawa da mutuwa ehee...
Abinda zai ba ka mamaki saura girls ɗin su biyu kamar ba su cikin sitting room ɗin kowacce ta mayarda hankalinta a wayarta tana operating.
Momma ta juya ta kalle su ta ce "Zee-zee!
Na'am!
"Halan yau Teema ba ta yi taking maganguna ta ba?
"Ban sani ba momma saboda batare mukayi breakfast ba.
Meena ce ɗago ta dubi momma ta ce "tasha ni ce ma na bata da kaina.
Teema ta yi karaf ta ce ban sha ba a sink na zube shi nayi flushing shege.
Cikin taussasa harshe momma ta ce "Akan me za ki yi flushing maganinki Teema?" Kin kuma san irin illar da rashin shan magani nan yake haifar miki.
"Mtcwww.....!
Teema ta ja tsaki haɗe da wulga wa momma danƙareriyar harara,
"Ai na faɗa miki ba zan ƙara sha ba.
Wallahi tausayinki nake ji momma saboda akwai ranar kin dillanci ranar da zani maigari yaɓata, muddinba ki tuba ba ki ka komawa ALLAH tare da neman gafara mutane da ki ka zalunta idan kin mutu sai an jefa ki wuta jahannama, ga ki ga fir'auna ke a ƙasa shi a sama.
''Na shiga uku Teema ni ki ke haɗawa da fir'auna? Ni mahaifiyar ki fateema.
Momma ta faɗa tana zaro idanuwa, "Amma ba yin kanki bane sheɗanu aljannu da suke da ke kanki ne sune suke sa ka ki kina min rashin kunya.
Teema ta murguɗa baki tana harara momma " Gara ma ki daina waɗannan karyayyaki naki momma don ni babu wani aljani da na ke tare da shi.
Momma tafashe da kuka tana cewa "ALLAH ka ba wa yarinyar nan lafiya, in ban da sharri Jinni ace yarinya ba wacce ta ke zagi sai ni mahaifiyarta
Meena ta miƙe tsaye tare da riƙo hannun Teema "zo mu tafi little sis ki sha maganinki kinga a dalili rashin shan maganinki gashi nan sai misbehaving ki ke yi kinsan momma tana kuka.
Zee-zee ta ce "gara ki ja ta ku tafi yanzunan sai su ɓatawa mutum mood.
'Meena ta yatsine fuska haɗe da ƙya6e baki ta ce mu je kinji ƙanwata.
Cikin rarrashi ta ja ta suka nufi bedroom ɗin su.
A dai-dai lokaci Aliyu, ya shigo sanye da farar shadda, fuskarshi a muturƙe as usual
kallo ɗaya Zee-ze tai mishi ta ɗauke fuska, da kyar ta buɗe baki ta gaida shi saboda tasan halinsa ba lallai bane ya amsa mata ba. Ya amsa ko bai amsa ba ita kan tashi tayi ta bi bayan 'yan uwanta.
Momma tana gani shi ta fara rawar jiki.
"Zo nan yarona!
Tafaɗa tana miƙa masa hannunta.
Ya kalli hannunta ya dauke fuska ya nufi two sitter ya zauna yana wani yatsina fuska, kamar ance mishi sai ya zauna.
Momma ta gyara zamanta da kyau tare da fuskantarshi "Yarona Daddynka fa yace wannan karon ba fashi sai yai maka aure, kwata-kwata baya bukatar amincewarka.
Ta ƙarasa magana tana karantar yanayinsa a fakaice.
Tsawon lokaci ya ɗauka yana jujjuya zoben yatsanshi, kamar ba zai yi magana ba sai tsotsar lower lip ɗishi yake can ya gama izzar tasa ya shiga magana cikin sanyi murya "Ni fa banaso aure kwata-kwata arayuwata, ban taɓa kallo wata 'ya mace naji ina sha'awarta ko sonta asalima tsoronsu nake ji maybe ni ba namiji bane ko kuma bani da cikakkiyar lafiya I don't have any feelings akan mata. Please momma ki ganarda Daddy ya haƙura da zance aure nan, ko yanayin business ɗina kaɗai ba zai barni na ba wa matata kulawa ba. Ga kuma wannan lalura dake damuna banaso ya yi abunda zan bashi kunya. Kina dai gani duk wani business na Daddy ni kaydai nake handle ɗinshi, Sauki na ɗaya uncle Suraj yana taimaka min da ba don shi ba da basan yadda zan yi ba. Ni kaina bana da lokaci kaina yaushe nakeda lokaci wata 'ya mace.
ya ƙarashe magana yana squeezing face ɗin shi.
Momma ta saki ɓoyayyen murmushin daɗi "Wallahi Son ba abinda ban faɗa masa ba, amma ya kafe akan lallai sai ya je Yola nem maka aure. Tsakani da ALLAH na rasa dalilinshi naso yi maka auren dole.
A wannan zamani ko mata an daina yi musu auren dole saboda kai yawaye, ballantana irinka Sultan ace za'ai maka dole wannan abu dubawa ne.
Ta faɗa tana wani girgiza kai.
shiru Aliyu ya yi haɗe da lumsashe manya sexy eyes ɗin shi.
Momma ta ci-gaba da cewa "shi fa aure lokaci ne da shi idan lokaci yinsa ya yi ba sai an cilasta wa yaro ba, ni a ganina lokaci aurenka ne bai yi ba.
mahaifinka ya ƙi fahimta kai ba mata ka ke nema ba awaje ka tsare kanka na rasa hujja Alhaji na nacewa akan lallai sai ka yi aure.Tsorana ɗaya yarona bansan wacece yarinya da zai auro maka ba. Matan zamani nan ba kowacce ke da imani ba, yadda mahaifinka yake da tarin dukiya kuma kai kaɗai ne ɗasa namiji, duk wacce ta aure ka ba don ALLAH za ta aureka ba sai don kuɗin ka da kyau surarka, burinta idan mahaifinka ya mutu ka gadi dukiyarsa, ita kuma ta kashe ka ta mallake dukiyar ita kaɗai karka yi mamaki hatta ni da 'yan uwanka sai ta gama damu.
jin abinda ta faɗa yasa Aliyu sauri buɗe idanunshi, yana kallonta gani yadda yake kallonta yasa ta fara kukan makirci, ta na cewa "ALLAH kaɗai yasan abinda zai faru anan gaba.
"Momma please stop crying banaso kina imagination ɗin mummuna abu akaina, in fact ba ni kaɗai bane ɗan masu arzki ba duk saura mata basu kashe su ba sai ni? Don ALLAH ki saki ranki momma ba abinda zai sameni.
''Ba za gane ba Aliyu duk lokaci da na kwanta bacci wallahi sai nayi mummuna mafalki akanka. Wai macce ta caka maka wuƙa a ciki ka ka mutu.
"Whatever!
Ya faɗa yana taɓe baki shi fa har ga ALLAH ya fara gajiya da tsoki burutsu nan na momma, saboda ya kawo karshe zance nata ya ce "Momma ba kowanne mafalki yake zama gaskiya ba.
''Waya gayamaka?"
momma tafaɗa tana zare idanu gata da manya idanu tubarakallah masha Allah!" Ita dai burin ta ta ƙara dulmiyar dashi.
Har ta karkace baki za ta ci-gaba da kimtsa baƙar dabara ya katsi mata hanzari da sauri yana faɗar "please momma I have some works to do.
Murmushi dole ta yi haɗe da cewa "To ai shike nan tashi katafi but you better think what am saying clearly.
"Yes momma!"
Ya faɗa yana miƙewa da sauri ya fice gami da nufar apartment ɗnshi tun kafi tasake tsayarda shi da wani zance.
_____________________________
*Adamawa-Yola*
*1:34pm*
YOU ARE READING
GIDAN RINA
Non-FictionSoyayya wani nau'i abu ne da Allah subhanahu wata'ala ya sanya a tsakanin zukata biyu wato namiji da macce.