GIDAN RINA!!SECOND EDITION.
Na
Jeeddah AliyuFREE PAGE.
005
Yana haɗa idanu da Daddy yafara murmushi yana sosa ƙeya alamar rashin gaskiya, dariya Daddy ya yi ya ce "lallai marhaban da baƙon Scotland barka da zuwa Gadanga k'
Ƙusar yaƙi.
Dariya ce ta subucewa Aliyu ya rufe bakinshi da tafin hannu, Kallonshi Daddy yake yana girgiza kai
"Good morning Daddy.
Aliyu yafada yana shafar gemunshi, "Morning Sultan idonka kenan. sometimes da sultan Daddy yake kiranshi kasancewar sunan mahaifinshi da yake da, murmushi ya yi tare da cewa "Daddy I'm sorry.
"Ba komai sultan.
Daddy ya faɗa "But zo ka zauna mu yi magana ta fahimta.
zaunawa ya yi kusa da Daddy kafin Daddy ya yi magana saida ya kama hannun Aliyu "Sultan dangane da zance aurenka ni da iyayen yarinyar mu yi fixing din Date nan da watanni biyu masu zuwa, saboda muna so ku same isasshe lokaci da za ku fahimce junanku. This time around idan ka sake ka ruguza aurenan Sultan I won't forgive you don haka make sure ka shirya this weekend ka je Yola ku gana da yarinyar kana ji na ko?"
Daddy ya tambayeshi, yana kallon yadda ya ɓata fuska tamkar zai yi kuka ga wani uban gumi da yake ta faman shawagi akan fuskarsa, da kyar ya haɗiye wasu busassu yawu sakamako bakinshi da ya gama bushewa ya ce "Daddy please idan har ya zama dole sai nayi aurenan ina neman alfarma ka ba ni dama na nemo wacce nakeso, saboda ba lallai bane kanemo min kalar mace da nakeso ba...
"Shut up my friend!
Daddy ya daka mishi tsawa "wallahi sultan ka shiga taitayinka da ni, muddin ka ga ba a yi aurenan ba ka ƙaddara hakan amatsayin bana numfashi tashi maza ka ɓace min da gani, shashasha banza da wofi.
Ƙasa da murya Aliyu ya yi ya faɗin "Daddy I'm so sorry karka yi fushi da ni please duk abinda ka ke so zan yi saboda ba zan iya jure fushinka ba.
Dauke fuska Daddy ya yi da barin kallonshi, hakan yakara ruɗar da Aliyu ya durkusa gabanshi, "Daddy nace na amince muddin zan sanyaka farin ciki koda mayya ce zan aureta.
Sai lokaci Daddy ya saki fuskarshi ya ce "thats my boy saidai ba mayya bace jikar Barkido ce sunanta Barrister Amina 'yar manyan mutane ce shiyasa banaso asame matsala, daga bangare na.
Zaro idanu Aliyu ya yi haɗe da Squeezing face "Daddy kana nufi yarinya lawyer ce?"
"Kwarai kuwa independent lawyer ce[lauya mai zaman kanta]
"Whatever! Daddy ni ko lawyer government ce I don't care kawai dai kasan I hate liar's kuma mostly lawyers maƙaryata ne.
hararrashi Daddy ya yi tare da furta "Banaso shirme Gadanga don kawai tana lawyer shi zai sa ta zama maƙaryarciya?"
Turo baki ya yi a sangarce ya ce "Ni dai Daddy I don't love her.
maƙe kafaɗa Daddy ya yi irin I don't care dinan, kafin ya ce kai dai karka yi gaggawa ka jira har ka ganta ido da ido.
Miƙewa Aliyu ya yi "sai na dawo Daddy ina da meeting around 12 o'clock.
"Asauka lafiya.
Daddy ya faɗa da murmurshi akan fuskarsa.
Ficewa ya yi yana fitowa isah direba ya jawo mota ya buɗe mishi back sit ya kame a owners corner, isah ya ja motar cikin kwarewa da tuki ya fice daga gidan.
****--*****-----****
Sai around 2:20pm Aliyu ya fito daga conference hall, kaitsaye ofishinsa ya wuce ya ajiye laptop 💻 ɗinshi da wasu files akan desk ya wuce ya bathroom ya duro alwala, yana fitowa P.A shi Kamal na shigowa riƙe da white coat ɗin Aliyu yanufi wata hanger da ke ajiye a cikin office d'in ya sakale rigar.
Aliyu yana fitowa daga bathroom da
sauri kamal ya shimfiɗa mishi praymat.
Batare da Aliyu ya kalle shi ba ya ce "Kamal ka yi min order abinci a chicken republic restaurant, yunwa nake ji cikina sai ƙugin yake.
"An gama Boss!
Har kamal ya juya ya sake cewa "ba ka ji ba kamal.
Cak! kamal ya tsaya.
"please help me call Jamal tell him I wants to seen him urgently.
"Yes boss!
Cewar kamal yana mai ficewa daga office din.
Aliyu yana gama sallah ya koma kan resting chair ya kwanta, ba abinda yake tunawa sai babban ƙalubali da yake tunk'aro shi, duk duniya ba abinda ya tsana irin aure da macce duk yadda ka ke da shi idan ka yi invited nashi daurin aure ba ya zuwa, ko a family su ake aure sai ya k'irk'iri tafiya don kada ya je sannan ko siblings ɗinshi da suke mata babu kyakkyawar alaƙa a tsakanin su hatta dasu da ya fito ciki ɗaya dasu ya tsane su, sosai abin yake ciwa Daddy tuwo a kwarya.
"Mtsss....ya ja d'an siriri tsaki ya dafe goshinshi duk lokaci da ya tuna Daddy ya ce dole sai ya je Yola wurin yarinyanan, sai ya ji faɗuwar gabansa yana daɗa hauhawa, wanda ya rasa na menene babban tashin hankalinsa bai san yadda zai ga yarinyar ba, ko yaya take bashi da mafita dole ya aureta don ya farantawa mahaifinshi rai. Sai dai ba za ta taɓa samun kulawa daga gare shi ba asalima ko kallo ba ta ishe shi ba.
Turo ƙofar da aka yi ya katse mishi tunani da sallama kamal ya ƙaraso, kusa da Aliyu ya ajiye ledar hannunshi.
"Boss na kira maigida Jamal ya ce zai zo nan ba da jimawa ba.
"Okay; ba damuwa za ka iya tafiya.
Ficewa kamal ya yi, yayin da Aliyu ya dauki takeaway guda ya fara ci kasancewar yana jin yunwa yasa yaci fiye da rabin abincin.
Abinci yake ci amma zuciyarshi cike take da zance zuci, turo kofar da Jamal ya yi, ya katse mishi zance zuci da ya ke yi, sallamar Jamal ta bugi dodon kunnenshi, ya dubi ƙofar yana mai amsawa Jamal ya shigo ya zauna kusa da Aliyu yana mai mik'a masa hannnu suka yi musabaha.
"Ya garin JB kwana biyu ka 6oye?"
Aliyu ya fad'a yana kallon fuskar Jamal.
"Al-hamdullilah! kwana biyu nan I'm too busy tun lokaci da Abba ya yi rashin lafiya abubuwa su kai min yawa.
Sauke numfashi Aliyu ya yi kafin ya ce "Gaskiya iyayenmu suna bukatar hutu musanmman yanzu da k'arfinsu kullum k'ara raguwa yake, gara kai JB kana da siblings maza su na taimaka maka a business d'inku saɓani ni da bani da kowa
Ta6e baki Jamal ya yi kafin ya ce "kadai ayi sha'ani kawai amma lamarin 'yan uwana sai addu'a daga mai shaye-shaye sai manemi mata, babu wanda za ka bugi kirji ka kira shi da nagari shiyasa kullum jini Abba daɗa hauhawa yake.
Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce "ALLAH ya kyauta ya shige mana gaba.
"Amin summa Amin!
cewar Jamal yana mai daukar robar ruwan Faro ya buɗe, ya kafa baki ya sha daga bisani ya ajiye ragowa.
Ya dube Aliyu gami da faɗin "king ya zance da mu ka fara a waya yanan ko ka watse shi?"
Ya k'arasa magana yana dariya.
"Uhm! Bari kawai JB wannan karo zance ba zai watsu ba.
Yanzu haka neman da nake maka zance nakeso, mu tattauna.
Daddy ya ce na shirya ranar Saturday naje naga yarinyar, sai ka shirya mu je tare.
"Allah ya kaimu cewar Jamal.
Ci-gaba da tattauna zance suka yi.
****----*****-----*****
Yammacin ranar Juma'a Barrister Amina tana zaune a office d'inta black suit ne sanye a jikinta, ga farin gilashi da ta manna a ƙwayar idanuwanta ya yi matuk'ar fitowa da kwarjininta.
Ta tattara hankalinta akan system, aka yi knocking k'ofa, "yes come in.
Ta fad'a tana mai ci-gaba da aikinta aka turo k'ofa tare da sallama ta amsa batare da ta d'ago kanta ba, ta ce "bebs sai yanzu ki ka fito?"
"Uhm bari kawai bebs case din yau ya bani kashi ba kaɗan ba kinsan shegen iyamuri nan Barrister Obi shi ne defendant lawyer, yanzu dai an d'age zama sai on 16 za'a ci-gaba da saurare k'arar kafin lokaci kotu ta umarci mu da mu zo da kwarara hujjoji ina fargaba Kada guy nan ya kada ni a shari'ar nan gashi ina matuƙar tausayi matar nan da marayu 'ya'yanta.
"Hmm!
Barrister Amina tai ajiyar zuciya haɗe da cewa "karki damu bebs In-sha-ALLAH za ki yi nasara, ALLAH yana tare da ma su gaskiya.
"Haka ne bebs thanks for the encourage me.
"You're always welcome!
Suka yi shiru na few seconds daga bisani Barrister Amina ta kawo karshen shiru nasu ta hanyar cewa, "bebs kamar yadda ki ka bani shawara na yi istahara akan mutumin nan, ba zan 6oye miki ba bebs akwananki nan kullum sai nayi mummunan mafalki wanda na rasa gane me hakan yake nufi.For those who interested of this love and romantic story you should kindly pay four hundred Naira. Here is my account details 0463745811 Hauwa Shehu Gtbank. send me your evidence of payment zero seven zero three two five six six one seven two
07032566172#Aliyu Ardo
#Barrister A Barkido
#Barrister Z Ladan
#Jamal
#Team Gidan Rina.
YOU ARE READING
GIDAN RINA
Non-FictionSoyayya wani nau'i abu ne da Allah subhanahu wata'ala ya sanya a tsakanin zukata biyu wato namiji da macce.