kurkukun ƙaddara E1

2K 23 4
                                    

*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*

*Boss Bature ✍️*

_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_

Gargarɗi

_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_

*E1*

Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfin gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, jikinsa na sanye da singlet da gajeran wando fari, aƙalla ya kai shekaru 40 a duniya. A launin fata kuwa wankan tarwaɗa ne, da ƙyar yake iya ware manyan idanuwansa a kan katafaren gadonsa kafin a hankali ya mayar da ƙwayar idonsa kan agogon bangon, tafin hannunsa ya kai tare da shafa fuskarsa cikin sanyin murya ya ambaci sunanta, "Angel!"

Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar, cike da mamakin wane ne yake kiran shi a irin wannan lokaci? Anya kuwa Lafiya?

Lokacin da ya kalli screen ɗin wayar sunan Aminina ne ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da ɗaga kiran ya manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare."

A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?"

"Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse.

A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call.

Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi.

Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon ya zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake  yi masa daɗi duniyar nan.

Yana cikin wannan halin ha'ula'in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, "Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku." Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 25, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KURKUKUN ƘADDARAWhere stories live. Discover now