2

474 11 0
                                    

AMATULMALEEK
Mamuhgee

2
Nisan dayake tsakanin Asmau da abeeda Bai taba rage kauna ko girman  junansu ba a zuciyarsu,
Babu dawowar da Abeeda zatai Nigeria Bata zo har kauye ta ziyarci Yar uwar tata ba Dan haka kusan kaf dangin mijin asmaun Babu Wanda baisan girman alaqarta da kaunar Dake tsakaninta da Abeeda ba,

Duk wata sutura da abincin datake ci Daya bambamta Dana Yan kauyen duka abeeda ce ta tsaya Mata akansu Koda Bata qasa ko tana qasar duk lokaci bayan lokaci sai an aikowa da Asmau abinci da suturar datake sakawa.

Acan dangin mahaifiyar abeeda Babu Wanda Bai gama sanin matsayin kaunar Dake tsakaninsu ba Dan haka Babu Wanda yayi yunkurin hanawa saima tsayuwa da sukai akan inganta rayuwar asmaun duk da tana kauye Dan haka itama asmaun Bata da tamkarsu.

Nisansu Bai hanasu zama abokan sirrin juna ba Dan kuwa Babu matsalar Asmau da abeeda Bata saniba kamar yanda asmaun Babu damuwar abeeda da Bata saniba.,

Rashin samun haihuwar Asmau da wuri yasaka Abeeda ta samu Samar dauko asmaun ta tafi da ita ganin Wani likita a porthcrt,

Da farko hankalin Asmau Bai tashi ba da rashin haihuwarta ba Amma ganin yanda abeeda ta damu ta kwallafa Rai Akai sai hankalinta ya tashi Wanda yasaka dole aka tsaya aka ringa yawon asibiti da asmaun.

Kamar yanda hausawa sukace ita dai kaddara yashi ce ko an dunkulata Bata dunquluwa, Abeeda ta tsaya da karfi da dukiyarta an nemawa Asmau lafiya Bata samu nutsuwa da Kwanciyar hankaliba Saida Asmau ta wayi gari ta samu ciki a jikinta.

Cikin Asmau nada wata biyu Aka kulla Auren Abeeda da Wani 'dan babban Aminin mahaifinta Aleeyu Muh'd Talba Wanda dagashi har ita bawai suna son juna bane Amma dayake Auren na connection ne Basu damu ba.

Auren Abeeda da Aleeyu aure ne na fitowar Rabon haihuwa kawai Wanda Allah ya kaddaro a tsakaninsu sbd Auren da wata uku Allah ya karbi ransa sanadin jinyar ciwon cikin kwana Daya kacal.

Bayan rasuwarsa ranar da Abeeda ta fita takaba ranar Asmau ta haifi AmatulMaleek wadda taci sunan Abeeda Amma suke kiranta da AmatulMaleek din sbd shine sunan da mahaifinta yafiso din Dan haka take amsa sunan AmatulMaleek din Amma a rubuce Abeeda AmatulMaleek ne sunanta.

Abeeda Bata samu zuwa haihuwar AmatulMaleek ba sbd itama tana fama da tsohon ciki me tsananin wahala Wanda ya Sakata shiga ciwo sosai.

Asmau duk da jegonta bata zaunaba haka taxo ta zauna jinyar abeeda harta samu sauki itama ta qarasa watanninta ta haifi 'ya mace itama take aka Saka mata sunan ASMAU Amma ana kiranta da Husnah.

A ranar da akai sunan Husnah a ranar aka daura Auren Abeeda da ASHRAF MUH'D TALBA 'dan uwan Aleeyu Wanda suke Yan biyu batareda sun taba ganin juna ba Amma hakanan zuciyar abeeda tafi kamuwa da son Ash Talba akan Aleeyu sedai Kuma halin Aleeyu ya bambamta sosai da ASH Dan haka zamanta dashi yafara Bata wuya ta bangarora da dama.

Wanna shine damuwar data fara Sako Auren Abeeda a gaba sedai Kuma Asmau ta tsaya sosai gurin Bata qwarin gwiwa Dan ta fuskanci aurenta ta tsaya ta riqe mijinta da kyau.

ASH baida raayin Auren mace biyu Bai taba shaawan Hakan ba Dan haka a zuciya da gangar jikinsa ya amshi abeeda dari bisa dari sedai rashin fuskantar halin juna da sanin juna yanda ya kamata yake azabtar da Auren nasu Amma Kuma kasancewar sunada ilimi dukkaninsu ya Saka Basu taba nunawa junansu gajiya ko gazawa da zamanba bare juna ba,

Matsalar datafi quntatar da Auren nasu shine rashin iya kulawa da soyayyar Auren Abeeda wadda Sam ta kasa yanda zata iya shiga zuciyarsa ta mallakesa ta hanyar kauna ko soyayyarta.

A idanuwansa tana iya hango tsananin girmamawa ne kawai yake mata Babu wata soyayyarta bayan Hakan Dan haka ta dage sosai dan ganin ta mallakarwa kanta zuciyarsa da Babu kowa a cikinta.

AMATULMALEEKWhere stories live. Discover now