💥
💥
💥*ƘARSHEN ALEWA ƘASA*
💥
💥
💥
💫
*NA OUM SULTAN*💫
*ALHAMDULILAHI ALLAH MUNGODE MAKA, MASOYANA INA JIN DADIN YADDA KUKE NUNA MIN KAUNA NADOGE SOSAI KUCIGABA DA BIYAYAR OUM SULTAN TAKU CE..*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*page* *7↪️8*
dukan "zarah yake kamar ba gobe yana dan ubanki mamata kike ma rashin kunya, to kiji tsoron hukuncin da zan rinka maki akanta wallahi"!
Kuka zarah ke yi kamar ranta zai fita ta e don Allah" babyn nawa kayi min hakuri kada ka kashe wayyo ni".
Bilkisu tace' Dear ƙara mata don yasan Ni ba sa'ar taba ce, ta kiyayeni tasan ni ba sa'ar ta ba ce ta ƙarashe magana tana balla mata harara.Haka dai "Ismaeel ya mata duka, jikin ta duk tsami yake mata shiga part ɗin ta tayi ruwan wanka mai zafi ta haɗa sosai wanka take tana mai zubar da ƙwalla ace wai mijin kane ya maka wannan dukan, mai tai ma Allah da ya zaɓa ma mata wannan rayuwar' saurin istigifari tayi ta gama wanka fitowa tayi ta shafa man zafi a jikin ta ɗan cikin ta tasha fa wanda yanzu zai yi wata uku, kwanciya tayi kan gado barci ne mai daɗi ya ɗauke ta"!
Bilkisu ta zo tana shafa bayan sa tace'' dear sannu wannan banzar ta wahalar min da kai".
Rungumo ta ya yi tare da yin kissing ɗin ta yace, no indai zata cigaba da ɓata maki rai wallahi zan cigaba da dukan ta, ko da ace kuwa na safe daban na rana daban haka ma na dare yafada yana huci kamar "zarah na kusa dashi''..
Sharhuliyar su suka ci-gaba dayi..
Bangaren zarah kuwa yunwa ce ta tashe ta daga barcin da take, cikin tane ya ƙara ƙugi miƙewa tayi da sauri Kitchen ɗin ta tanufa indomi tada fa sai ƙwai biyu da tahaɗa ta soya, fitowa tayi zaman take nan akan darling talble ya shigo ko sallama babu ita tazaci ma hakuri ya zo bata, yace ki kiyaye Ni Dan matata ba Sa'ar ki ba ce ita..
Ɓudar bakin ta tace' don Allah yaya kayi hakuri in Sha Allah bazan sake ba.
Haka dai ya tafi ya batar da da tunanin dukan da ya mata, bayan fitar da da 30 sai ga "bilkisu tashigo tace kinga dai abin mamaki yadda mijin naki ya wulakanta ki a gabana, nan gaba ma ke zaki koma ƴar wanke wanke na"!
Kallon ta zarah tayi tace' wai yanzu kina nufin kinyi wannan abun ne don kiji daɗi ne, kisani akwai Allah shine zai min maganin ki' in Sha Allah asirin ki sai ya tuno..
After 2 month abubuwa da dama sun faru ciki harda shariyar da "Ismaeel yake ma zarah, inda bangaren bilkisu suke cin duniyar su da tsinke yanzu bata mai da hankali kan tabashi hakkin sa, tafi gane liwaɗi ɗin ta' tasamu wata Hajiya wacce take haɗa ta da mata da maza manya ƴan gayu sosai"!
Kamar kullum yau ma tunda" Zarah ta tashi take aikin gida duk girman gidan ita ke sharewa, ga ba fulowa ruwa hon aka yi, da ɗan cikin ta wanda yanzu wata 5 kenan take tafiya irin ta masu ciki ta je ɓuɗe get ɗin da ƙyar take tura shi, saboda bilkisu tace duk a kori wani mai aikin gidan tafi don na zarah, zuwa tayi ta duka ta masa sannu da zuwa a gatsine ya ke kallon ta ko amsawa bai ba ya shige ciki, ƙwallon ce ta zubo mata tacigaba da shara".
Makociyar tace tashigo ta ƙaramar kofar gidan, daman tasan lokacin ne tasan tana aikin yamma ta amshi sharar ita kuma ta ba fulowa ruwa, sun gama suka zauna kan tebur ɗin da mai gadi ke zama suna fira, firar tasu dai "nasiba[ makociyar ta] take bata hakuri da tattashin ta akan dai tasan mijinta bazai mata haka cikin hankalinsa ba.... Haka dai har suka gama fira ta tafi gida, tazo shigowa daidai part din "bilkisu taji tana waya tana cewa malam wallahi aiki ya yi kyau, sai dai ina so a ƙara mallake min ƴan uwan sa duk su fita harkar ta".
Hankalin tane ya tashi, tai saurin wucewa, bata san miyasa hankalin ta ya ƙara tashi anya "bilkisu kuwa zata shiga aljanna ta raba shi da iyayen sa, ta tabashi da matar sa, yanzu kuma gashi tana shirin tabashi da ƴan uwan sa".
Hajiya ta kira take faɗa mata halin da take ciki, gashi tana shirin yi masu......." Hajiya tace zarah mu dage da addu'a Allah shi zai mana maganin ta, yanzu haka muna nan muna nema ma Ismaeel taimako, abinda take masa ya karye"..
Hamdala tayi ma, Allah tace to "Hajiya Allah Ubangiji ya taimaka mana.
Ameeen ameeen, ki fara zuwa a wone??
Tace a'a ina dai son fara zuwa, kada na faɗa ne yamin duka tunda yanzu ya gane duka na!
Tunda aka yi la'asar take fama da aiki har tasaba sai dai idan dare. Ya yi tai tafa da ciwon jiki, tagama shara ne sai ga "bilkisu tafito cikin riga da wando na Pakistan tana tafe tana taunar cingam, tace ke jaka idan mijina yadawo kice mai natafi anguwa, sai kuma tace ke ƙyalesa ma banda damuwa dashi"..
Ita dai "zarah kallo ta bita dashi ba'abinda take illa kallon ta, da take tana fita ba daɗe wa sai ga Hajiya tashigo ganin zarah Yadda tabi talala ce tarame ga baƙi da tayi, shigowa suka yi part din ta suka zauna suna magana kusan awa daya sai ga Ismaeel ya dawo, gani tai ta tashi da sauri take ta buɗe masa get din ba karamin mamaki bane ya kama Hajiya ba to wai ina mai gadi ne wannan maganar cikin zuciyar ta take magana, dukawa tayi ta amshi jakar hannun sa ta mai sannu da zuwa gun da Hajiya take suka nufu yace yaushe kika zo ne Hajiya"?
Wata tambayar ta jefo masa ba tare da tabashi amsa ba Tace "Ismaeel wai mai ke faruwa ne a gidan naka ne naga Duk zarah ta rame"?
Kallon "zarah ya yi yace uban me kika faɗa matane, kedai bazaki daina munafincin ba ko? Zanyi maganin ki wallahi a gidan nan".Tunda taga haka, tahau sababi, ta inda take fita batanan take shiga ba faɗa take tamasa yace''hajiya wannan yarinyar bata da mutumci gashi bata da mutun ta matata, ita ce kullum bata ɗaukar girman ta"!
Maganar ta girgiza "Zarah tace wallahi Hajiya banayi mata komi shine dai da ta faɗa masa sai ya ɗauka, ba bincike".
Faɗa tamasu sosai, ta tafi tabarsu, kallon ta ya yi yace'' kin kai ƙara ta don tayi min me gashi tazo ta tafi sai ki kuma kai wa gobe, tashi yayi tashiga part din bilkisu Kiran ta yake yana baby baby baby kusan sau uku amma bata amsa ba, shiga ɗakin yayi yaga bata nan kiran wayar ta yayi yaji akashe haka ya zauna yana jiranta..
Zaune take gaban bokan ta, tace so nake ka mallake min duk wani ƙwarkwata nashi su dawo mallaki na.
Kallon ta ya yi yace''angama bilkisu mai gadon zinari amma kisani idan zan maki wannan sai mun kasance kullum tare har tsawon kwanaki 10, ya ida maganar yana mai lashe baki".
Tace'' malam ba wata hanya da za'a shine sai wannan"?
Tsawa ya daka mata yace, idan baki so sai ki tashi kitafi, haka dai ta amince da buƙatar sa tashi suka yi suka shiga cikin bakin ɗakin nashi don aikata masha'arsu....
Har kusan 11pm bata dawo ba,ɗakin "Zarah ya shiga kwance take kan gado tana barci cikin kwanciyar hankali , tausayin tane ya kamashi saurin kauda tunanin ya yi, lalubar zanin ta ya fara, ji tayi kamar ana tabata saurin buɗe ido tayi ganin shi tayi tace lafiya dai"?
Murtuke fuska yayi tare da faɗin talla gyara min ni!
Ƙi tayi haka yayi mata ta ƙarfi har ya cimma haƙarsa........ Kuka ne ya kubce mata ace kusan wata huɗu bai zo gare ta sai yanzu ma batare da wani ɗan sako ba..
Wanka tayi ta tsaftace jikinta dawowa tayi ta kwanta...
Can "bilkisu ta kwana sai asuba ta dawo gida".
Ko tambayar inda taje baiba, sai ƙara lallaba ta yake kada ranta ya ɓaci..
Zarah kuwa da asuba' cikin ta ya murɗa mata ciwon mara ya ishe ta tun tana hakuri har ta kira Hajiyar su, don ta faɗa mata amma bata ɗaga wayar ba"anty Jidda ta kira sai gata wajan 7:40 asibiti suka nufa domin aduba ta"!
Kuci gabada bina don jin yadda zata kaya
*MASU SAN AUDIO ƊIN KARSHE ALEWA ƘASA MUNA DA SHI SAI SUMIN MAGANA A 08130266111 SAI NA JIKU*